← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 128

Sashe 93

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabadaya zuba masa ido mukayi ni da mama muna dariya salmah kuwa sai in mun hada ido ta danyi yake.

Can ya dago ya kalleni snn ya kalli mama yace"goggo Amina babyn nan fa dani tayi kama sosai ko kin lura?

Dariya sosai mama tayi tace"eh da kai take kama salman .amma fa tun dazu kake rike da ita baka baiwa salmah ita ba.

Salmah tayi murmushi tace"Goggo kawai ki barshi sai ya gaji da kallon babynsa.

Mama ta mike hade da fadin "to bari na baku waje .

Har zata fita ta juyo ta kalleni tace"rumaisah ki bata nono fa kinji abinda nurse dinda ta fita tace koh?

Nace"eh mama.

Tana fita yaya salman ya mikawa salmah baby ta karba tana murmushin da bai kai zuci ba .

Tana karban babyn ya rumgumeni cike da fara,a ko kunyar salmah baiji ba ya shiga kissing dina hade da fadin"baby nagode sosai Allah ya miki albarka gaskia bazan iya fada miki irin murnar da nake ciki a yau ba .

Murmushi nakeyi yayinda nake dan janye jikina daga nashi saboda banson salmah ta ji wani iri.

Ya dago yana kallona yayinda yake rike da hannayena yace"babyna ina fatan dai bakijin komai yanzu?

Nace"babu komai yaya lfy lau nake jina .

Yace"masha Allah gaskia naji dadi sosai.

Gabadaya mun shagala muna hira mun manta da wata salmah.

Can mukajiyo kukan baby da sauri ya salman ya mike ya karbeta yana cewa "salmah me ya sameta?

Tace"inaga yunwa takeji ka bata mamanta tasha nono.

Da sauri yaya ya kawota ya mika min yana "gaskia kam yunwa takeji ki bata tasha.

Na karbeta hade da fadin "nifa ban wani iya bada nono ba ka kira min mama tazo ...

Ya katseni da fadin "ba sai an kirata ba gyara ni zan koya miki yadda ake shayarwa.

Ya dada kusanto yana shirin kai hannunsa gaban rigana .

Salmah haushi duk ya cika ta don haka bazata iya gani ba kawai ta mike ta fita.

Mu dai bamusan ma ta fita ba sai kokarin sawa baby nono muke a baki ni dashi da kyar muka samu ta kama.

Yaya ya sauke ajiyar zuciya hade da fadin"Alhamdulillah har naji sanyi a raina wlh banson jin kukanta.

Bayan ta dan sha ya salman ya karbeta anan ya mata addua ya mata huduba da suna *AISHA* innah ta samu takwara Allah dai yasa kar ta dauki halin innah *amin*

Inna kuwa kasancewar ba ita ce da girki ba bata sami labarin haihuwar ba abbah yace sai gari ya waye zai sanar da ita.

Aikuwa yana dawowa daga masallaci ya tafi dakinta ya sanar da ita cike da farin ciki innah ta washe baki tace"Alhamdulillah Allah mun gode maka me aka samu alhaji?

Abba yace "mun samu Aisha salman ya fada min ke yayiwa takwara.....

Abba be gama magana ba innah ta rangada guda wanda ya tashi sadiya wacce yau kwananta biyu da dawowa daga lagos.

Abba kam dariya yayi yace"shatu ba kyau fa hamdala zakiyi kedai.

Inna cike da fara,a tace"Alhamdulillah Alhaji amma ka barni inyi guda ma Allah ya amshi adduata.

Abba yace"to se ki shirya muje asibity.

Inna tace"yanzu kuwa.

Abba ya fita yana dariya .

Sadiya kuwa tunda gudan innah ta tasheta ta fito palo tana kallon innah sai da abba ya fita tace"innah gudan meye kikeyi?

Inna ta juya tana murmushi tace"na karuwa mana yau Allah ya amshi adduata rumaisa ta haihu kuma harma salman ya min takwara.

Dam! Xuciyar sadiya ta buga duk yadda taso ta boye bakin cikinta ya gagara sai da ya fito fili
Tace wa innah shine har da wani guda kamar yau kk fara samun jika innah?

Nan da nan inna ta daure fuska tace "to uwata gaya min.wai ma ina ruwanki da ni ne?

Gsnin haka yasa sadiya fadin Allah ya baki hkr innah.

Ta juya ta tafi daki cike da bakin cikin wnn labarin mara dadi.

Kamin gari ya karasa wayewa asibity ya cika da mutane.in tsaya fayyace muku irin farinciki da muke ciki bata lokacine .

Tunda na haihu nake ta samun alkhairai ta koina Alhamdulillah.

Ranar sunan *AISHA* *FAREEDA* gidan mama ya cika taf ba masaka tsinke .kaya kuwa mun samu har mun rasa inda zamusa .

Inna ma tayi rawar gani gun hado ma takwararta kayayyaki sai wanda ya gani.bangaren ya salman da daddy ba,a magana .

Anyi suna qalau an watse qalau ba wata matsala sai sambarka .

Masu bakin ciki suna fama su sadiya da adda A'i.Salmah kuwa har fushi tayi tace zata tafi gidansu sabida ya salman ya daina kulata tunda na haihu baida lokacinta yana danne mata hakki.

Aikuwa ko kallo bata isheshi ba har ta gama fushinta ta fasa komawa gidan nasu lol! Don ta lura in dai ta salman ne bai ki ta tafin ba.....

Hauly ce🥰👍🏻
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡84

**********Alhamdulillah yanzu kam Rayuwa tayi mana dadi babu wata matsala.

Saida mukayi satinmu shidda snn muka fara fita gidansu innah muka fara zuwa wai karkuso kuga farin ciki gun innah kamar ta goyamu .ta karbi farida tayi ta mata rawa.

Gashi tayi wayo sosai ga ta dama tubarkallah katuwa hasken fatarta kullum karuwa yake ga dariya kuwa ko wani motsi in dai idanta biyu dariya takeyi ko fanka ta gani yana kadawa ta dinga dariya knn.

Gaskia na lura ba karamin shiga ran innah farida tayi ba motsi kadan zata dauketa har da goyo wani abin dariya ma har Tadi take mata.

Sadiya kuwa ba karamin haushi takeji ba don har ta gaji tacewa innah"kai innah irin wnn so haka naga ba,a kanta kika fara samun jika ba ko dan takwararki ne? Ga Abdul dina shine jikanki na farko wanda a gidan nan na haifeshi a dakinki yayi wayo amma sam baki damu dashi kamar wnn ba......

Inna ta katseta da fadin"don me zan damu da Abdul din irin rashin mutunci da ubansa ya dinga shimfida mana a anguwan nan ba irin zagin duniya da bai mana ba nida abbanki musamman ma ni marainiyar wayonsa ranar da naje don a sasanta ina rufe ido yayi ya zageni tass .kina nan kwanaki na tura sa,a nace a kawo min su Abdul na gansu ba turowa yayi yace"baza a kawo su ba saboda shi mara kunya baisan darajar babba ba.don haka ni ba ruwana da wasu Abdul suje can suyita zama da dangin ubansu din marasa mutunci.

Nida nake zaune shiru tun dazu bansa musu baki ba sai yanzu nace"sai hkr innah basu kyauta ba gaskia amma duk daren dadewa yaran nan in suka girma zasu zo gun uwarsu abu gari daya anguwa daya ma wlh karki daga hankalinki.

inna ta tabe baki tace"oho ya rage nasu yanzun ma da ya hanasu zuwa Abdul ai indai ya tashi makaranta baya kwana biyu bai biyo ta nan ya gaida uwarsa ba.

Nace "Allah sarki kinga ya yi wayo knn.Allah ya rayasu ya masu albarka.

inna ta amsa da" amin kawo kayan shatu a samata mun gama shafe shafenmu yanxu kam saura musa napkin da kaya.

murmushi nayi nace"to bari na dauko.

Sadiya kuwa tunda innah ta fara magana taja bakinta tayi shiru na lura ranta ba karamin baci yayi da maganar innah ba duk da dai tasan gaskiane .

bayan na dauko kayan farida da pampers na kawowa inna da turaranta innah ta karba hade da fadin"au matar har da turare ma takeda shi?

nan ta shirya farida tsaf ta kama yi mata wasa sunata dariya yayinda sadiya duk ta gama cika.A ha ka ya salman ya shigo ya samemu tunda ya shigo ya saki fuska yace"Innah hira kk yi da mai sunan naki knn?

Inna tace"eh mana baka gani sai dariya take tayi kazo zaka katse mana hiranmu na kawaye.

dariya mukayi ysyinda innah ta mikawa ya salman farida tace"riketa kuje ta gaida maigidanta nima wanka zanyi yanzu inzo inyi kwalliya sai muyi hoton solfie da me sunana.ko ba solfie kk cewa ba turawa.

Bani kadai ba harda ya salman saida yayi dariya snn yace " hakane innah selfie ba.

Inna tace"koma dai bahaka ba tunda kun fahimceni ina zuwa.

daga nan ta tashi ta fita.ya salman ya kalli sadiya hade da fadin ke kuma lfy kk ta wani zumbure zumburen baki ?

fuska daure tace"babu komai ina kwana.

ya amsa mata da lfy.snn ta tashi ta wuce daki.

ya salman ya zauna kusa dani hade da fadin "wai don Allah yaushe zaki dawone babyna wlh inata kewarki.

murmushi nayi nace"yaya ai bangama yawon arba,in ba sai naje Abuja da yola tukun.

yace "haba baby na gane yanzu ba kya missing dina sam .

a hankali nace"inayi mana yaya sai dai kasan dole ne inyi wadan nan tfy tfyn sai dai ka kara hkr idan mun dawo dai shikenan ai.

yace"to ya na iya Allah ya bada sa,a ya kuma kiyayeku.

Nace"ameen.

ya kalli fareeda yana murmushi yace"innata zaki tafi ki bar daddy ko?

ya mika min ita hade da fadin gaskia a bata nono tashi tana jin yunwa na taba cikinta ba komai.

karbanta nayi tasha baysn ta koshi ya dauketa suka fita .basu shigo ba har bacci ya daukeni .bansan ya suka kare ba su innah ko anyi selfien oho.

Satinmu daya da kyar innah ta barmu muka wuce Abuja gidan kawu kasim na fara zuwa kwanana biyu snn naje gidan goggo ummi itama na yi kwana biyu daga nan sai gidan ya salim gaskia ruma taji dadin zuwanmu ga babynta mimi ta girma ita ma sai wayo.munsha hira sosai kwanan mu biyu muka wuce yola Gidan galadima na fara sauka gunsu hajia rumaisa gaskia sunyi ta murna har da 'yan koke koken murna abinka da tsufa lol!
Chapter 93 · 0% Book details