← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 123 OF 128

Sashe 123

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nafisa ta tashi ta zauna tace "kwarai kuwa saboda kin hanani jin dadi da sakewa da walwala da farko kunyi sanadin aurena da ya salman alhalin kinsan ni suraj nakeso maganarmu har tayi karfi amma saboda son zuciya irin naki saida kikayi duk yadda zakiyi kika raba mu ta hanyar sanya tsanarsa a zuciyan iyayenmu .kikazo kika sa na auri ya salman saboda dukiyarsa kullum cikin sakani a matsala kike duk .....
Haushi ya cika adda A'i a fusace tace"bana son zancan banza.ai ba shi na tambayeki ba.kuma da kk wani cewa ni na saka kika auri salman gata na miki ko cutar ki nayi? Wawiyar banza kawai wlh idan salman ya sakeki ba karamin nadama zakiyi ba don bazaki taba samun kamarsa ba.

Sa,adatu tace "hmm ba wnn ba adda yanxu ta fada mana wnn uban kudin meyesa ta dauka kuma ina ta kaisu?

Duk tsit sukayi anan nafisa ta fashe da kuka sa,adatu ta jawota jikinta tana lallabata .

Nan ta fada musu yadda sukayi da adda A'i akan maganar kudi duka.snn suraj ma da yazo kano suka hadu bukatar kudince ta kawoshi wai so yake ta kara mishi wasu kudaden domin ya fadada kasuwancinsa zuwa lokacinda zata kashe aurenta suzo suyi aure su shimfida rayuwarsu mai dadi.

Koda ta dawo gida tunanin yadda zatayi ta samo kudade masu yawa takeyi domin dolene tasan yadda zatayi ta toshe bakin adda A'i wacce tace in ta kashe aurenta zata gayawa iyayensu komai kuma tasan in dai bata bata kudin ba zata iya aikata komai da ta fada.Snn kuma tana son suraj ma ya fadada kasuwancinsa domin suji dadin more rayuwarsu in sunyi aure don haka dolene sai ta nemo kudin nan ko ta wani hanya domin taga komai ya wuce ko zata huta itama.wnn dalilin ya sanya ta daukar kudi a dakin salman.

Tana karasa gaya musu ta ci gaba da kuka tana fadin"duk kun sani a matsala gashi nazo nayi abinda ya dameni .....

Su adda A'i tuni suka hau kan ta da fada da zage zage wai ai tayi rashin hankali .

Sa,adatu ne ta dinga lallabata tana bata hkr akan ta bar kuka kar zazzabi ya rufeta.

Su adda A'i kuwa har lokacin zaginta suke wanda hakan daga baya ya tunxura nafisa sosai ta tashi ta bar musu dakin.

Washe gari kasancewar lahadine Salman ya kira inna a waya yace gashinsn zuwa yanxu su fito mishi da kudinshi.

Dama sadiya da raihana ma sunzo duk suna palo.

Inna kuwa dama ko fita batayi ba tinda gari ya waye sai da salman ya kirata ne ta fito ta samesu dukansu a palo nafisa na kwance jikin sa,adatu saboda zazzabi da ta tashi dashi da kyar tasha tea sa,a ta bata magani .

Sadiya kam jiran kiris take yau ma tayi rashin mutunci sai dai lura da hakan yasa su adda A'i ba wacca ta tanka mata.

Breakfast ma da maman sakina ta turo musu ba wacce ta iya ci a cikinsu.
Saida sadiya ce ta zo dama bata tsaya yin breakfast ba a gidanta tunda ta samu jafar ya barta dai ta kamo hanya tazo don haka tana shigowa taja warmers ta cika cikinta ta hada tea tana sha tana jifansu da harara.

A haka inna ta fito ta samesu duk ta bisu da kallo.
Nan suka gaisheta bata amsa ba kawai tace "Salman yace yana nan tafe ina fatan kun fito masa da kudin nasa?

Gabadaya nafisa suke kallo lumshe idonta kawai tayi batace komai ba.

Sadiya ta ajiye kofin tea tace"hmm ai dole ma kawai kudin nan ya fito.

Inna bata kuma yin magana ba ta juya ta ciki abinta.

Har saida ya salman ya shigo gabadaya saida kirjinsu ya shiga dukan uku uku nafisa kam kasa bude ido tayi don tana matukar jin kunyarsa da nauyinsa yayinda zuciyarta fal da nadama.domin a iya zaman da tayi dashi ya gwada mata soyyaya na ban mamaki kuma yasha ajiyeta yana mata nasiha akan duk abinda zatayi a rayuwa ta dinga sanya tsoran Allah a ranta ashe yana sane da abinda take masa sarai hmm.

Ya zauna gabadaya suka gaisheshi yau har da su adda A'i don tasan bazai gaisheta ba lol.

Ya kalli raihana yace" ke ina innah ?

Ko kan raihana tayi magana sai ga inna ta fito tanacewa gani.

Snn ta zauna.

Kai tsaye yace ina fatan kun fito minda kudina?

Tsit sukayi.da farko.nafisa ce tayi karfin halin mikewa ta shige dakinda ta sauka ba jimawa kuwa sai gata da jakar kudi su adda A'i har suka ji sanyi a ransu ysyinda ita kam nafisa kunya sosai takeji haka dai ta daure ta karaso gaban salman ta durkusa kanta a sunkuye tace"Yaya don Allah kayi hkr ka yafe min nima ba yin kaina bane sharrin shaidan ne da kuma son zuciya ta kaini ga aikata wnn babban kuskure a shirye nake dana karbi dukkan hukuncinda zaka min amma kamin nan ya zama dole na fada komai gameda aurenmu......

Nan ta bashi labarin komai daga farko har karshe duk da yasan wasu amma wasu kam baisani ba .
Inna kam bata taba tunanin hakan daga garesu ba sosai mamaki da tsoro ya bayyana a fuskar innah.

Adda A'i sosai ta shiga hada gumi gashi babu daman karyatawa.

Yayinda nafisa ta fashe da kuka tace " yaya don Allah don son Annabi ka yafe min wlh nayi nadama.kuma zan koma gidanka inci gaba da zama a yanda kake sona bazan sake bin zugin kowa ba pls yaya ...

Ajiyar zuciya yayi baice komai ba ya bude jakar kudi data ajiye a gabansa ya duba da kyau yaga ko sisi ba a taba.Allah ya toni asirinta tun kan tayi kasafinsu.

Jinjina kai yayi ya maida jakar ya rufe snn ya kalleta har lokacin tana durkushe a gabanshi tana kuka .

Kamar ansa shi dole yace"Nafisa na yafe miki dukkan laifin ki.tunda kudina suka dawo gareni ba tareda ko sisi yayi ciwon kai ba.

Su adda A'i harda ajiyar zuciya tayi najin dadin yadda salman yace ya yafewa nafisa.

Sadiya kam ta gama cika fam sai dai salman bai bata fuskar tankawa ba.

Anan su Adda A'i madiha da nabila suma suka shiga rokonsa da alkawarin hakan bazai kuma faruwa ba.

Mamakin rashin kunyarsu yake sosai amma baice komai ba.

Sa,adatu da raihana sunji dadin yadda al,amarin ya warware ba tareda samun matsala.nan sukayiwa salman godiya.

Inna dai tana zaune binsu take da kallo har lokacin bata tanka ba.

Ya salman mikewa yayi ya zuba hannunsa cikin aljihu ya kalli nafisa snn ya zaro wata farar takarda ya mika mata.

Hannunta na rawa ta karba fuskarta na bayyana alamun neman karin bayani.

Murmushi yayi yace"Hmm wnn tukuicin dawo min da kudina da kikayi ne na baki.sauran bayani na ciki.

Snn ya kalli Inna yace"Inna gasu nan duk hukuncinda kikaga ya dace da su ki yanke musu ni na gama nawa.

Yana fadin haka yasa kai ya ficewarsa.
Nafisa da ta gama karanta takarda ta fashe da kuka ta karasa gaban inna ta durkusa tana "Goggo yaya sakina yayi har saki uku .

"Uku!!!
Duk suka maimaita yayinda sadiya tace"Alhamdulillah.lol!

Nafisa ta dada fashewa da kuka tace"wayyo na shiga uku na lalace ni nafisa me zance da su baba?Adda kun cuceni kun bata mun rayuwata.....

Ta dada fashewa da kuka mai ban tausayi.sa,adatu da raihana ne suka kamata suna bata baki amma ina ta kasa sauraransu.

Maganar inna ce ta sasu nitsuwa dukansu suka maida hankali kanta.

Cewa tayi "Ban taba tunanin haka daga gareku ba musamman ma ke A'i.ba irin gatan da ban miki ba a rayuwa kai bama ke kadai ba gabadaya danginmu don sanin kanki ne nice na tsaya tsayin daka wurin ganin samun ci gaban danginmu gabadaya.a cikinkun nan wacece ban jata a jiki ba na nuna mata kauna kamar ni na haifeta? amma da yake dan Adam butulu ni
sai gashi da abunda kuka saka min.to ku sani kanku kukayiwa bani ba.don haka ba tare da son jin dogon bayani ba ke A'i madiha da nabila ku tattara nafisa yanxun nan ku bar gidan nan kuma kar in sake ganinku na yanke duk wata alaka dake tsakanina da ku kuma yanxu zan kira in sanar da iyayenku dukkan halinda ake ciki don su sani .

Tashin hankali tuni su adda A'i suka zube sunata rokon inna yayinda sa,adatu da raihana ma suke tayasu.

Sadiya kam ko a jikinta sai ma dadi dataji sosai.

Ba irin magiyar duniya da basuyi ba fir inna taki sauraronsu tace lallai lallai su tashi su fice mata daga gida.

Don dole kowacce ta hada kayanta jiki babu kwari zasu tafi adda A'i ta kalli nafisa tace"se ki tashi mu tafi ai.

Nafisa dake aikin kuka tun dazu ta harari adda A'i tace Allah ya sawwaka har abada bani baku wlh ni anan zan zauna bazan bikuba.

Inna tace"aikuwa ko cibiyarki aka binne anan dole ki barshi ki tashi ki bisu nagodewa Allah da baki haihu da salman ba kuje can ku karata duk wanda tsautsayi ya dibeshi ya kwasheki.

Anan nafisa ta tubure tace ko kasheta inna zatayi bazata bi su adda A'i ba.

Anan sa,adatu tace shikenan in ta tashi tfy gidanta su tafi tare.

Wata uban harara inna ta zubawa sa,adatu amma batace komai ba.

Su adda A'i haka suka fice jiki babu kwari.

Haka sa,adatu da raihana ma kamin azahar duk sun fice .nafisa ta hada kayanta tabi sa,adatu kaduna.

Saura sadiya da inna suna zaune jugum jugum sallah kadai ke tashinsu.

Can sadiya ta dago ta kalli inna tace"Inna ni a ganina duk wnn abubuwa da ya faru alhakin RUMAISA ne ya kamamu .

Hawaye ya zubowa sadiya taci gaba da fadin"Inna nikam nayi nadamar abinda na aikata irin nadamar da ban taba yi ba a rayuwata .inna mun zalunci rumaisa bana wasa wlh innah idan har bamu nemi gafarar rumaisa da goggo Amina ba bazamu taba ganin dai dai a rayuwarmu ba.

Sadiya ta fashe da kuka tace"Inna kullum na tuna abubuwanda mukayi tayiwa rumaisa sai bacci ya kaurace ma idona .tabbas duk wahalanda da nayita sha a rsyuwa alhakin rumaisa ne ya kamani don haka nikam nayi nadama kuma zan nemi gafararta daga ita har goggo Amina da yaya salman.....
Chapter 123 · 0% Book details