Sashe 36
Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shatu kuwa idan akwai abinda yake damunta bai wuce ganin Mohd yana ji da amina kamar tsoka daya a miya kuma baya ko ganin laifinta.
Don sau da yawa Amina zatayi laifi amma sai yaki yi mata fada ko kuma ya maida laifin kan shatu Wanda hakan yana matukar kona mata rai.domin zama da Amina yana son ya ja mata matsala da mijinta.
A lokacin da amina ta gama secondary ta sami sakamako mai kyau ba ba ta lokaci aka samo mata jamiar Kaduna ta fara zuwa
A lokacin kasim kuma Allah ya hadashi da ubangida na gari Wanda ya jawo shi a jiki ya bashi aiki a companynsa.ganin amana da gaskia irin na kasim yasa ya bashi 'yarshi Zuwaira ya aura anan suka hada kudi da Mohd suka sayi gida Dan madaidaici suka koma anan akayi bikin cikin aminci.
Zuwaira ma ' yar jamia ce don ta wuce amina ma da shekara daya don haka tare suke zuwa .
Sosai Amina take shiri da Zuwaira kominsu daya domin acewarta bata har ka da kauyawa.
Shatu kuwa ba karamin damuwa ta shiga ba daga zuwan Zuwaira gidan don sosai take kishinta musamman gashi daga zuwanta har ta sami ciki ita kuwa shiru har kuka ta rikayi gashi bata da kowa a garin
Mohd yana kokari wurin rarrashinta don har islamiyya ya sata ya kuma bata jari ta fara sana,oin cikin gida ko zata rage damuwa.
Cikin ikon Allah kawai ranar itama ta tsinci kanta a yanayin rashin lfy ranar sai amai take tayi.
Amina ce ta shigo gidan da kawayanta ganin shatu na amai yasa ta ja dogon tsaki tace" wai ke yaushe zaki wayene ? Kinzo tsakar gida kina ma mutane amai don tsabar kazanta?
Kawar amina mai suna fati ta kalli Amina tace" wacece wnn meenah?
Amina ta yatsuna fuska tace " hmm 'yar aikin mune.
Shatu ta dago da sauri kuma cike da mamaki .
Amina ta watsa mata harara ta kalli kawayenta tace " kuzo mu isa ciki gun auntyna
Nan suka wuce gefan Zuwaira wacce take fama da laulayi
Sun gaisa anan suka shiga hirar makaranta.
Amina ta fita taje gun shatu dake kawance tace" wai kin gama girki ne kikazo kika kwanta?kin bar mutane da yunwa?
Shatu kam tana fama da kanta da kyar ta iya fadin " na gama miya tuwo ne kan wuta.
Amina ta dan yamutsa fuska tace" to da kike kwance anan kin fadawa yayan bakida lfy ne?
Girgiza kai tayi Amina taja tsaki tace " ke dai bansan yaushe zaki waye ba.
Ta fita zuwa kitchen ta debo kwanuka ta raba abinci duk ta kai wa kowa nashi.
Bayan sun gama cin abinci kawayenta sun tafi ta kalli Zuwaira tace " aunty shatu fa ba lfy dazu mun shigo sai amai take kuma ko girki bata karasa ba ni nayi.
Zuwaira tace" subhanallah shiyasa mana yau bata shigo ta biya karatunta ba.
Amina ta yi dariya tace " kina kokari da kike koyarda ita wlh wnnn mata bazata taba wayewa ba yaya dai hasken nan da dan kyan nan ya rudeshi yaje ya auro wacce in sun haihu bazata iya tarbiyantar masa da yara ba.
Zuwaira tace " don Allah Amina ki rabu da matar nan haka.
Amina ta tashi tana dariya tace " bari naje na sameta muje clinic tunda su yaya baza su dawo da wuri ba.
Zuwaira tace " gaskia ne kam gara akaita din.
Anan amina taje tacewa shatu ta shirya su tafi asibiti.
Sun fita a hanya suna jiran mai keke napep.
Anan wata sabuwar mota dalleliya tazo gabansu ta tsaya anan mai motar ya fara sauke glass a hankali .
Wani matashin mutum ne kyakkyawa fari Sol ga hanci har baki yana sanyeda jumper da wando sky blue ga hularsa mai tsadar gaske da ya kafata ya tafi da yanayin kyaun fuskarsa mai cike da saje.
Ya kalli Amina wacce kwata kwata hankalinta baya kansa.
Ya saki murmushi yace" meenah
Sai lokacin ta kalleshi cikin mamaki mara misaltuwa tace" laa Ib yaushe a garin namu?
Fuskarsa cike da fara,a yace " tun last week.ai tunda Ku kun share mu dole muzo.
Tayi dariya tace " kaji Ib wai mun shareku.
Yace " eh mana meenah ko waya ba,a samunku .
Tace" o sorry Ib wancan layin ya dade bana amfani da shi.
Murmushi yayi ya kalli shatu yace " aunty ina wuni?
Can ciki ta amsa da lfy ta kauda kanta.
Amina tace " bata jin dadine 'yar uwar matar yayana ne ta zo daga kauye .
Yace" eyya sorry Allah ya bata lfy.yanzu asibity zakuje ne?
Amina tace " eh wlh .
Yace " to muje mana na ajiyeku ai ba damuwa.
Amina tace " no Ib ka tafi harkokinka kawai.
Yace" ai meenah ke mai tsadace bai dace a barki anan kan hanya ba.
Dariya tayi sannan tace " shikenan mun gode.
Ta kalli shatu ta danyi kasa da murya tace " wlh kika kuskura kika masa amai a mota hmmm kinsan saura .kuma ba wai in kin shiga ki dinga kalle kalle kina zare ido kina kauyanci ba nitsuwa zakiyi don ma dai na Riga na fada mishi ke din daga kauye kikazo amma dai ki kula.wnn mutum da kike gani wayayye ne dan boko bai son kauyanci.
Shatu ta hade rai tace " to aini bance miki ina bukatar shiga motar saurayinki ba.da kike cewa daga kauye nazo waye waye a haka yayanki ya gani kuma yakeso.
Tsaki amina taja tace " asircesshi kukayi.
Ta bude kofar motar na baya tace " zo ki shiga.
Shatu ta shiga ba dan ranta naso ba amina ta rufe sannan ta bude gaba ta shiga tana murmushi ta kalli Ib bayan ta rufe tace " Ib kuna shagalinku.
Yayinda suka fara tfy yace Amina ke dai banda zolaya kinga nki yadda kike shining kamar wata Zara a cikin taurari wai meye sirrin ne?
Murmushi amina tayi tace kaima ka zolayeni ni.da nake koduwa a school?
Haka suka manta da wata shatu suka dinga hira wani hadadden private hospital ya kaisu ya hadasu da doctor nan akayiwa shatu gwaje gwaje aikuwa cikine har na wata biyu da satittika.
Anan amina ta hau murna itama kanta shatun farin ciki ya gama cikata bayan sun gama komai Ib ya ne ya dawo da su yayinda ya cika su da kudi.yacewa amina zaizo.
Suna shiga gida amina ta kalli shatu tace " to saura inji kin kuskura kin gayawa yaya abinda ya faru.
Zuwaira ta kalli shatu tana murmushi tace " shatu me yene kk boye mana ke da kanwar taki?
Shatu tace " hmmm saurayi ta samu ya rinka dawainiya damu.
Zuwaira tace " ayya
Amina tace " ke shareta Ib ne fa.
Zuwaira tace " kai ? Yaushe yazo?
Tace " hmm wai tun last week akwai aikinda aka turoshine anan KD
Tace " aunty Zuwaira albishirinki?
Zuwaira tace goro fari Sol!
Tace " shatu ma ciki ne kuma har wata biyu da satibiyu tare ma zaku haihu don watannin cikinku daya.
Zuwaira ta kalli shatu cike da tsantsan farinciki tace " wayyo yar uwa na tayaki murna wlh naji dadi sosai.
Shatu kam ba ta yi magana ba ta wuce daki ta kwanta.
Da daddare su kasim suka dawo bayan sunci abinci sun huta an fara taba hira amina ta kalli Mohd tana murmushi tace " yawwa yaya akwai albishir da zan maka.
Mohd yace " to kanwata ina jin ki.
Ta kalli shatu tana murmushi wacce ita kam tuni ta mike ta yi daki saboda kunya irin namu na Fulani.
Tace " yaya shatu na dauke da ciki har na wata biyu da sati biyu dazu na kaita asibity.
Ta mika shi takardar scarning.
Sosai Mohd ya nuna murnarsa a fili ya dinga Godiya ga Allah nan da nan ya mike ya bita daki amina da kasim suna dariya.
Tundaga ranar Amina ta dauke nauyin hidima dasu domin babu abinda take so a rayuwa da ya wuce taga sun tara zuria suma tunda dangi sun guje su.
Shatu kam duk tattalinta da amina takeyi gani take kamar ta hada bakine da Zuwaira don a ganinta Sam basa sonta.
Amina da Ib sun kulla soyayya mai karfi a tsakaninsu har ta gabatar da shi gun yayyunta amma abin mamaki sai ta lura Sam basu yi na,am dashi ba .domin a ganinsu.bai kamata amina ta yi nitsa dasu ba kamata yayi ta yi aure kusa dasu domin Susan duk abinda take ciki.
IBRAHIM AHMAD GALADIMA wato Ib cikakken dan Adamawa ne a garin yola dan babban family ne domin in kaje yola kace galadimas family to ba Wanda bai saniba.
Ib ya hadu da Amina ne a sakamakon wani aiki da ya kawo shi KD bai bata lokaci gurin nuna mata yana sonta ba amma ta dinga ja mishi aji har yaxo ya koma .
Dawowarsa na wnn karon ne yasamu ya shawo kanta amma ya lura kamar yayyunta basu karbeshi ba hankalinsa ya tashi kwarai don a ganinsa zai iya yin komai akan yaga sai ya aureta.
Akwai dan yayan Zuwaira Farouq da yake matukar son Amina amma ita bata so yayyunta kuma sunfi sonshi ba don komi ba sai don danuwan Zuwaira ne sannan dan Kaduna kuma mahaifinsu mutumin kirki ne ya rike kasim kamar dan cikinsa don haka suna ganin auren amina da Farouq shi zai kara musu dankon zumunci.
Amma Sam amina taki yarda ita dai IB take so.
Zuwaira kam har ga Allah bata yi fushi da Amina ba don tasan halin soyayya.har kokari take ta baiwa yaysnta hkr da ya hkr ya nemi wata kawai amma kasim ya hanata yace ta bari zasu shawo kan Amina.
Shatu kam taso ace amina ta fuskanci tsanani gun yayyunta don bata son su lallabata don haka ta dinga ingiza Mohd tana kara cusa musu tsanar Ibrahim tana nunan musu ai shi yake zuga Amina yana hure mata kunne ta bijire musu.