← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 128

Sashe 9

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Faiza ta yi dariya tace ba dole ba? Ke koni ma na tsorata kinga yadda kk dunga bude mata wuta Ashe haka kk da tsiwa.

Mukayi dariya.

Nace " hmm kunsan me wlh idan ta fadawa ya salman zamu fuskanci hukunci sosai .

Tace "kinsan Allah ban ko tunashi ba.

Nayi dariya na ce " koni wlh hmm Allah dai ya somu in ba haka ba akwai matsala wlh.

Washe garin daurin aure an kawo 'yan kidan kwarya .

'Yan matan kamaroo sai rawa suke.
Koda muka shiga har mun ma fisu iyawa don haka kowa mu yake kallo.

Momy da Mamana har spray suka mana.
Muna cikin rawa sakina tazo tayiwa faiza rada.

Faiza tazo nima cikin kunnena tace" ke ga ya salman ya shigo kuma ya ganmu sai kinga yadda yake jifanmu da wani irin......

Na juya ban ganshi ba nace" ke ni ban ganshi ba rabu dani.

Tace " innace ta kira shi suna dakinta.

Nace " ke shareshi don Allah.

Dariya mukayi mukaci gaba da rawarmu.

Da yamma tuni 'yan daukar amarya raihana sunzo don ita a zoo road za a kaita sadiya kuma a cikin unguwar tamu amma can gaba kadan.

Don haka muka fita don ganawa da abokan ango.sai janmu suke da hira mu ta yi har da dariya in ka ganmu zaka dauka mun shekara tare.

Kwatsam zai ga ya salman ya danno kai da motarsa .ni ban ganshi ba sai tadina nake sakina tuni ta yi cikin gida tana ce mn ga ya salman.

Shareta mukayi ni da faiza.
Koda ya sauko tsayawa yayi ya kare mn kallo ya gyada kai yayi cikin gida.

Bayan an kai Amarya mu a can aka barmu sai washe gari aka sallamemu .

A motar abokin ango muka dawo su biyu ne dayan yace yana sona daya kuma wai sakina.faiza kam da an tabota sai tace ai an mata miji. 🤭

Mun dawo dakin inna Na shiga na sameta da yan uwanta suna ta filatanci na gaishesu.tace " rumaisa har kun dawo?

Nace eh

Tace" ina kayan da nace ki amso min?

Nace" inna wai ki bar mata duka bedsheets din tana so.

Tace" ai raihana bata dama duk zata hada ta bata gashi ba wanki take so ba.

Nace " inna ai gidan raihana ba irin gidan nan bane mai wanki mijinta zai samo mata.

Tace" Allah yasa

Nace " amin

Tace" kije ciki ki dauko flaks din salman da kofinsa ki kai masa nasan baya son shiga gida cike da mutane ne.

Ai sai da naji kirjina ya buga a sanyaye na tashi na shiga na dauka na tafi dakinsa.

Nayi sallama jin ba,a amsa ba yasa nace ko yana waje don haka kai tsaye na shiga ina murna har da 'yan wake wake.

Ina dagowa kawai karaf muka hada ido.

Bansan sanda nace " wayyo .yaya kayi hakuri na dauka ko baka nan ne.

Na russuna nace 'ina kwana?

Kallona kawai yake baice min ko kala ba.

A tsorace nace " dama inna ce tace in kawo maka tea dinka.

Na ajiye na tashi zan fita yace " zo nan .

Zaro ido nayi a tsorace nace" na,am?

Yace " zaki zo ko sai na tashi ?

Da sauri na isa gabanshi na durkusa .

Bai kuma cewa komi ba naga dai yana daddana waya can yasa a kunne naji yace " Momy kice faiza tazo yanzun nan ina jiranta.

Nikam na kara zaro ido jikina ya shiga rawa.

Ba jimawa faiza ta shigo da alamu har ta soma bacci.

Zama ta yi a kasa tace" yaya ina kwana?

Kallonmu kawai yake mun dauki kusan minti biyar a haka .

Sannan ya fara magana " duk kunsan me kk yi don da gangan kuka dinga rashin kunya son ranku .

Ya kalli faiza wacce ta nitsu kunnenta ya cafko ya murda da karfi ta saki ihu

Tsawa ya mata " shut up !

Sannan yace " Salima ta gaya abubuwa da kk yi mata na rashin mutunci .bansan faiza baki da hankali ba sai yanzu .don haka nake ja miki kunne akan Salima wlh wlh wlh Salima ta kuma ce min ko kallon banza kk mata kinsan saura.

Ya kara murde mata kunne yace " irin abubuwanda kk dinga yi a bikin nan duk na gani kuma zan gayawa daddy ya miki aure karki fi haka lalacewa.

Kuka faiza takeyi ya saki kunnen ta yace " tashi ki bar nan nonesense.

Ta mike da sauri ta fita .

Ya kalleni yace " ke kuma .....

Jin yayi shiru yasa na dago a tsorace.mukayi ido hudu na sunkuyar da kai nace" yaya don Allah kayi hakuri wlh na tuba wlh......

Hannu ya daga min sannan yace " me na gaya miki a baya akan Salima?

Nace ' yaya faiza ce ta zage..

Ya katseni " keep quite before I bounce on you .an gaya miki bata fada min irin zaginda kk mata bane wlh ki kiyayeni kece baki sanni ba kar ki kuskura ki kaini bango don wlh bazai miki dadi ba.

Hawayene ya fara zubo min nace " kayi hakuri bazan sake ba.

Yace,kima sake in kinga dama .

Ya danyi shiru sannan yace " daga yau idan na kuskura na kara ganinki da wani kuna tsaye ko a bayan idona naji labari zan mugun saba miki. Kamar yadda mamanki tace karatu za kiyi to karatun zakiyi kuma dolene ki cire tunanin aure a ranki don ba yanzu zakiyi ba.don haka ki maida hankali. Kamin ki kureni nayi miki mummunan hukunci.

Kaina a sunkuye nace" kayi hakuri.

Yace tashi ki ban guri.....

Ai tun kan ya karasa na tashi abuna.

Hauly ce👍🏻😍
[05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```

➡ page 8

Biki ya kare an watse gida sai mu.

Ni da sakina tuni mun fara shirye shiryen mkrnt don har ya salman ya mn registration.

Ina cikin dakin inna ya shigo a Palo ina jin yana cewa inna.

" ina rumaisa ne?

Tace " ina zaka ganta a waje Dan tsabar bakin hali a daki take zama kamar mayya.

Yace" ai ki daina damun kanki inna ' yar kauyece.

Tabe baki ta yi tace " lfy kk nemanta?

Yace" eh so nake su shirya itada sakina suzo mu tafi suyi siyayya kayan bukatarsu na makaranta kinga a satin nan zasu tafi.

Tace" yawwa zauna dama ina son magana da kai.

Ya zauna yana ksllonta.
Tace" na lura sai faman kashe kudi kk akan karatun wnn yarinyar lfyn ka kuwa yaushe ka fara aikin harda zaka dinga kashe kudinka a banza.

Yace " inna naga ya dace ne in tsaya mata ta yi karatu ta cikawa mamanta burinta na son taga yarta ta yi karatu me zurfi kuma in kin lura rumaisa tana da ilimi uwa uba kwazo da kokari kinga ai bai kamata ace an barta a banza ba.....

Ta katseshi da fadin " hmmm ina jiye maka tsoron shishigi da kk Wa yarinyan nan wlh .salman bari kaji in fada maka rumaisa bazata taba yin abin kirki ba in kun kaita jamia lalacewa zatayi domin halin uwarta tayo .dama zaku gane Ku lallaba Ku mata aure zai fiye muku sau dubu.ka daina bata kudinka a banza.

Ya danyi shiru sannan yace" inna in Allah ya yarda ba abinda zai faru da ita ki mata fatan alheri.

Tace " shikenan ,amma ka fita harkanta ka daina kashe kudinka akan ta.in kudi ne da kai ka fara gininka ka min nan in mahaifin Salima ya amince kayi aure yafi maka .in ba haka ba kuma ka bawa sadiyq da raihana jari su fara sana,a a gidajensu yafi maka alheri akan wnn asaran da kk yi .makarantar rumaisa bazai amfanar mn komi ba naga abbanku da alhaji kasim ma sai dagewa suke akanta suna ganin zatayi abun arziki hmm Allah ya kyauta.

Yace" amin inna ina son ki daina damun kanki .gini dai mun fara tara kudi tare da salim a hankali zamuyi.snn sadiya da raihana daddy yace zai basu kudi suyi jari.kuma duk kudin nan da kk ganin nake kashewa rumaisa ba duka kudina bane goggo Amina tana turo kudi yanzu ma ita ta turo min dubu Dari biyu tace ayima sakina da rumaisa siyayya....

Inna ta Dan zaro ido tace " dubu Dari biyu ! Aminan? Me takeyi haka?

Kai tsaye yace" kasuwanci mn kinsan ta na da kokarin nema tun a kauyema bare yanzu ta na cikin gari kuma mijinta babban mutum ne kin Sani.

Ta Dan tabe baki tace da kyau kaje ta na ciki inaga bacci take.

Yace" to

Ya same ni a daki rufe idona nayi kamar me bacci.

Tsayawa yayi yana kare min kallo sanye nake da dogon Riga marar hannu irin roba dinnan yabi jikina sosai. Kamar kullum gashina ko parking babu haka na sake shi har ya Dan rufen fuska don kiwiyan parking nakeyi don yawan gashin bana iya gyarawa ni daya mama ne mai gyara min nan kuma sakina ce ko zainab suke tayani.yanzu ma rabon in gyara har na manta haka nake sakeshi ko in kama in daure don ko kitso ba mai son yi min.

Dan ajiyar zuciya yayi a ransa fadi yake" kamar aljana Allah na tuba.

Pillow da nake kwance ya bubbuga da kyar na iya bude ido .kamar mai bacci gaske.

Na kalleshi fuskarsa ba fara,a yace" ki tashi ki shirya ina jiranku keda sakina a waje.

Na tashi a hankali na zauna mika nayi sosai hade da salati na turo kirjina gaba.

Kauda kai yayi da sauri don yaji wani iri a jikinsa.

Yace" kiyi sauri inada wurin zuwa da yawa.

Yana fada ya fita.nima bayansa nabi inna na Palo bance mata komi ba na fita na Debi ruwa a bucket na shiga wanka.a gurguje na shirya muka fita da sakina muka samu yana jiranmu a mota baya na shiga sakina a gaba.

Mun Dade a kasuwa don ba abinda bamu tsiya ba.

Mun kai kwana uku muna parking.

Sakina ta rigani tfy don saida ya salman ya kaita ya dawo kamin nan nima na je na sallami mama nasiha ta min sosai akai rayuwar jamia
Chapter 9 · 0% Book details