← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 128

Sashe 6

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sakina tace kin ganta tafi girma ko ? Yarinya ce jin dadine kawai amma fa ta fimu don sa,ar su sadiyane yanzu zasu gama secondary.

Tabe baki nayi nace nace hmm sun dace mu tafi.

Mun iso kofar gida har zamu shige ya kirani Sakina kam ta yi ciki.

Na dawo nace"gani.

Yace in ba abinda kikeyi je ki share min dakina.

Nace "to.

Salima ce ta dago ta kalleni tace " wacece wnn ban Santa ba?

Yace 'kanwatace.

Haka kawai na tsinci kaina da jin haushinta.

Harara na watsa mata nayi ciki.

Kallonshi ta yi cikin mamaki tace"amma dai ba 'yar gidanku ba?

Yace ke dai kin cika tambaya

Tace kaga wata uban harara da ta buga min duk kannenka suna respecting dina amma ita ko gaisheni ba ta yi ba.

Murmushi yayi yana kallon fuskarta snn yace " ki tashi kije gida kamin au Abba su fito su sameki kiji kunya.

Tace ai na gaya maka yau nazo ne don ka kaini in gaida innahrmu.

Ya mike yana to muje .
Sun shiga cikin gida.har dakin inna ya kaita suka gaisa.

Ta rikowa inna sayayya cike da Leda sabulan wanka ne da rurarrruka masu tsada sai Wanda ya gani.dayan ledan kuma juices ne kala kala.

Inna sai waahe baki take tn zuba Godiya.

Ya kai ta dakin mama ma suka gaisa sannan ya rakata har gida sannan ya dawo ya sameni har na gama sharar daki ina tsaye ina kallon hoton salima kato manne a dakin tn murmushi kyakkywace gaskia gata 'yar gayu.

Ko da ya shigo baimin magana ya wuce abinsa ya fara cire shirt din jikinsa.

Motsin da naji ne yasa na juyo da sauri sai ganin mutum nayi da vest ba Riga yana kokarin cire belt din wando ma.

Zaro ido nayi a tsorace don ban taba ganinshi haka ba. Gashi kirar karfi ne da shi hannun nan a murde.

Naja baya zan gudu kawai sai naci karo da stool
Da zafin nama ya taroni don saura kiris in kife.

A tsorace na rikeshi baice komi ba sai da na dawo hayyacina na ga yadda na masa kyakkyawan riko kunyane ya kamani.

A hankali na cire hannuna da kyar na iya fadan "yi hakuri.

Yace" zauna.

Na zauna a kasa yace "gobe zan koma Lagos ki fada min abubuwanda baki dashi sai na siya miki don in na tafi zanyi watanni biyu a can.

Ji nayi kamar ince kar ya tafi don ko ba komai su sadiya suna suna raga min in yana nan.

Hawayene ya taru a idona har ya fara zubowa nace " babu komai.

Shiru yayi yace "aa tuna dai?

Na girgiza kai nace babu.

Yace kina da man shafawa da sabulu?

Nace aa

Yace me sunan manki?

Nace cocoa butter

Yace " turare fa ?

Nace "babu.

Yace " wanne zan sya miki?

Nace "smart collection ne mama ta ke saya min ko Vanilla.

Ya gyada kai yace " pad fa....

Da sauri na sunkuyar da kai cikin jin kunya na kasa dago kaina.

Yace " ko baki sanshi ba?

Nace 'mama tana tsiyamin.

Yace OK

Ya sake cewa me size na bra dinki da pant.

Shiru nayi kaina a ksa ganin banda niyyar magana yace au ba tambayarki nake ba kk min shiru?

Har yanzu kaina a sunkuye nace ina da pant...kuma bana sa bra....

Yace" ke dai yar kauyece to me kk sawa a kasan kayanki?

Nace "mama ta na saya min have vest.

Yace" lallai Maman nan tn kokari wurin kula dake duk da a kauye kk.

Ni dai duk na kosa yace in tafi .

Can kuma ya dauko maganar makaranta yace " naji ana yabon kokarinki a makaranta ki Kara kinji kanwata ina son gaba daya dis year Ku rubuta ssce

Wani irin dadi naji har nayi murmushi don babu abinda nake buri irin naganni a Jami,ar bayero da nake jin labarinta.

Yace shikenan kince ba wani abu ko?

Nace"aa yaya dama inaso in anyi Hutu inje gun Mamana.

Ya girgiza kai yace mamanki amaryace bazakije ki takurata ba.za dai kije ki dawo in ta tare.amma in kina so in anyi Hutu zan yiwa salim magana yazo ya daukeki ya kaiki Abuja .

Wani dadi naji zanje Abuja naji ance garin'yan Hutu ne da jin dadin rayuwa😀

Nayi murmushi nace "na gode yaya .

Hannu ya daga min snn yace " kina iya tfy.

Na tashi na fita ya bini da ido ya rasa dalili tausayina yake sosai don haka yake kokarin jawoni jiki yaji matsalolina amma shi bai iya sakin fuska irin na salim ba.duk yadda yaso ya sakar min fuska abin ya gagareshi.

Ina shiga gida na tarar duk suna sakar kowa da goran juice a hannunsa ana sha ana zuba zance sadiya sai washe baki ake.

Da shigata innah ta kalleni tace "tuntuni sai yanzu kk gama sharar dakin salman din?ni kinga har na gama rabiya na manta dake ungo ragowar nawa ki karasa sai kizo ki min kitso.

Na kallesu nace 'bako akayi a gidan ne ya kawo abinsha.

Sadiya tace " bakuwa ce aunty Salima matar da yaya zai aura itace ta kawo mn.

A take fuskata ta sauya a raina nace shine suke ta rawar jiki.....

Inna ta katseni da fadin ungo amshi mana.

Na girgiza kai nace aa inna na koshi bari in dauko comb in zo muyi kitson.

Na wuce ciki fuskata ba fara,a.

Muna kitson ya salman ya shigo Inna tace yaje ya dauki juice ta ajiye mai a fridge din Abba yace ni bazan sha ba aba rumaisa.

Inna tace "to ai taki sha ban Sani ba ko ta rainane don na bata kadan to in mun gama kije fridge din palon kawunki ki dauki na salman din.

Nace " ni na koshi ne inna.

Zata yi fada ya katseta da fadin rabu da ita inna 'yar kauyece bata San juice bane.

Snn yace Inna gobe fa da sassafe zan koma in akwai wani abu a gaya min zan shiga kasuwa yanzu.

Ta danyi shiru snn tace "ni ban bukatar komi kudi zaka bani.

Yace " to zan turo muku Abba zai Baku.

Shiru ta yi kamar bata so.

Shi kam tashi yayi ya tafi.
[05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

(👨🏻‍🚒Matar soja👨🏻‍🚒)

_(Labarine da ya kunshi fadakarwa,Ilmantarwa da kuma Nishadantarwa_)

Story and written
By
Maman khausar✍🏻

*INTELLIGENT WRITER'S ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**

```~BISMILLAHIRRAHMANI RAHEEM!~```

➡page 5

Yaya salman kamin ya koma Lagos sai da ya saya min duk abinda nake bukata.

Sannan ya ban dubu biyar yace in ajiye in wata bukata ta taso in dauka In kashe kuma ya gargade ni yace banda yawo.

Naji kewa sosai duk da ba magana mai tsawo ke shiga tsakaninmu ba.

Munyi exams an bamu Hutu na tsawon wata daya.

A cikin week din ya salim yazo ya sauka a dakin ya salman ranar raba dare mukayi a dakinshi muna hira saida mmn sakina taxo ta kira mu tace mu bar shi ya huta.

Washe gari kuwa muka shirya ya kaimu gidan mama dake borno avenue.

Babban gida ne tsarin ginin zamani ga kayan alatu.

Alhaji Aminu shine mijin mama shahararren Dan kasuwa ne matansa uku mamace cikon ta hudu yaransa goma sha shidda yawanci sunyi aure wasu kuma na makaranta .

Ko wacce mace da sashinta da kuma masu aikinta.

Wlh ko da naga irin jin dadi da Mamana ke ciki ji nayi kamar nayi zamana.

Ta kawo mana kayan ciye ciye kala kala ga 'ya'yan itatuwa da lemon kwalba ga abinci iri iri.

Muka bude ciki mukayita ci.

Bayan munyi azahar ne ta kaimu dakunan kishiyoyinta muka gaggaisa har palon alhaji ta kaimu ya karbemu kamar yaran cikinsa.

Ban samu na kebe da mama ba Sam saboda su sadiya har dare karfe 7 ya salim yazo yace mu tafi .

Gaskia kishiyoyin mama suna da kirki ko wacce sai da ta cikamu da kaya.

Shima Alhaji ba,a barsa a baya ba.kudi ya raba mana dubu goma goma.

Anan mukayi sallama da kowa kamar ince zan kwana.

Ganin yadda na bata fuska hawaye na kokarin zubowa yasa ya salim yaji tausayina yace " Goggo Amina rumaisa ta kwana jibi zanzo in dauketa......

Kafin ta yi magana har sadiya ta yi farat tace " to muma zamu kwa......

Tsawa ya salim yadaka mata"don Allah wuce mota malama .in kun kwana suwa zasu yi aikin gida.

Suka shige mota nik am tuni na tafi gun mama.

Yace "Goggo kamata yayi ma rumaisa ta miki sati saboda kun jima baku hadu ba amma zatayi kwana biyu kawai don ina so ranar Sunday mu wuce Abuja da ita tayi hutunta.

Cike da fara,a mama tace babu komai salim na gode sosai Allah ya kaimu rai da lfy.

Ya mata sallama nima na daga masa hannu ina murmushi.

Motarsu na fita mukayi ciki da mama.

Har bedroom na wuce na fada gado ina birgima ga AC.

Mama ta yi murmushi tace to meye hakan kuma?

Nace wlh mama rabona da in kwanta kan gado tun kauye a dakin inna a Palo nake kwanciya ni kadai akan kujera in ta jin tsoro kuma da asussuba take tashina in ran girkintane ta yi ta Sani aiki ga zagi da gori.

Nan na tsinke da bada labarin su Inna .

Tun mama na tsaye
har ta gaji ta zauna ta na kallona .

Har na gaya mata asma na ma ya tashi.

Ta numfasa tace "hmm Allah shi kyauta shatu dai bata canza hali wlh ni dama dakin rabi kk zauna.

Nace" ai yaya salman ne ya kaini dakinsu nima bana so.

Tace kar ki damu ke dai kici gaba da musu biyaiya kiris ya rake idan kk tafi jamia hostel kawai zaki zauna.tunda salman yace zakuyi ssce dinku a ss2

Nace eh haka yace.

Hira mukeyi har sha dayan dare bamu sani ba.

Mama ne ta kalli agogo tace tashi kije bandaki kiyi wanka.

Nace"mama sai kin nuna min yadda ake yin komi fa a bandakin naki.
Chapter 6 · 0% Book details