← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 128

Sashe 27

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri na kwace nace " me ye haka idan ka bugu ka fita hayyacinka wa zai karasa min labarin?

Idanunsa sunyi jazur yace" Queen ki daina wasa don Allah wlh seriously abin nan ya dameni ba kadan ba kinsan ni sarai ba haka na tsara rayuwata ba.

Na danne dariyata nace" amma ina bakayi mata komai ba.

Yace" ai dole ne kawai in ba haka ba zasu tara min jama,a ayita min kallon raggo mara lfy.shine na nuna musu lfy ta garau.

Ya fadi hakan ne yayinda yake lumshe ido yaci gaba da fadin " da gangan na ki binta a hankali tunda ita ta jawo na mata raga raga yanzu suna can asibity .kuma ta kuskura tayi ciki sai na bar musu kasar nan.lol!

Kauda kai nayi ina dariya ciki ciki sannan na kamoshi na kwantar dashi nace " rabu dasu kai dai ka sauke nauyin da Allah ya dora maka sauran kuma ya rage nasu.yanzu bari na maka tausa.

Ya jawoni ya rumgume a jikinsa yace " my Queen amma fa da dadi.

Murmushi nayi nace" wow kace ka more lol! Yau dai ka zama ango!

Toshe bakina yayi sannan ya dada rumgumeni anan muka fara romancing din junanmu sai dai ba,a kai koina ba ya saki jiki sai bacci.

Zuba mishi ido nayi cikin takaici na lura shaye shayen nan shi ke hana Ahmad komai a rayuwa .

Nan na kwanta a jikinsa naci gaba da kidana da rawana ni kadai har na dan sami relief daga nan bacci mai nauyi ya daukeni .

Bamu muka tashi ba sai wajan karfe hudu na yamma da kyar na tasheshi

Bayan munyi wanka nace " ni zan tafi.

Rumgumeni yayi ta baya yace " no ba yanzu ba kizo muje muci abinci tukunna.

Na ce " kamar kuwa kasani yunwa nakeji tun breakfast.

Yayi murmushi yayinda ya sumbaci bakina yana shafa cikina yace " eh gaskia kina jin yunwa my Queen mu tafi.

Nan muka fita sai wata hadaddiyar restaurant muka ci muka koshi daga nan muka fita wajen shakatawa kusan magriba nace " king gara in tafi gida shugaban 'yan sa ido na gari.

Yace " Salman ko?
Na ce"eh
Yayi tsaki yace " forget about him yau akwai casu na musamman muje kiyi koda one hour ne inyaso...

Na ce " kai mama zata kashe ni!!!!

Yace " kawai kice musu kin kwana a hostel ne.

Na ce hmm Mamana 'yar duniyace zata gane .amma fa duk da haka casun nan ba zai wuceni ba .

Murmushi yayi yace " daz my Queen!

Na ce " to albishirinka yau lectures uku na rasa sai kasan yadda zakayi.

Yace " karki damu da wnn my Queen kamar kinje kin gama ne.

Har bayan sallar isha muka tafi gidansa bayan mun biya kanti na zabi kayan zuwa casu mini siket ne da riga ko vest ' yar karama cibiya a waje yau nayi niyyar duk Wanda ya kulani zan kulashi tunda Ahmad bai iya komai ba sai Shaye shaye.

Wayoyina kuwa na kashe tuni yau dai duk abinda zai tafasa ya kone.!

Karfe goma muna wurin casu an saka music masu zafi rawa kawai muke wuri duk ya rude.da nishadi da annashuwa.( _wa_ , _iyazubillah_ )

Caraf naji an rumgumeni ta baya . na duba gabana banga Ahmad na juya da sauri a tunani na shine kawai sai mukayi ido hudu da wani hadadden gaye Wanda ya tafi da imanina .

Murmushi ya sakar min nima na maida masa .

Kawai ya dada rumgumeni tura hannunsa yayi ta gaban rigana yana wasa da.........

Lumshe ido nayi ina jin wani irin dadi gaskia wnn ya hadu a cikin rawa kawai har ya kusa sumar dani inaga in mun shiga ciki?

Tuni kuwa na manta da wani Ahmad yana can yana shan shisha hankalinsa kwance.

Tuni mukayi gefe da wnn gayen ya kalleni kamar zai hadiyeni yace" baby kin hadu wlh kamata yayi muyi cinikin kwana.

Na kashe masa ido daya nace " ka fini haduwa ai.ba matsala sai yanda kace.

Ya sakar min murmushi yayinda ya riko hannuna da nufin tfy.

Kawai sai ganin Ahmad mukayi a gabanmu yana huci kamar wani bakin kumurci .

Da sauri na janye hannuna cikin na gayen a tsorace na koma gefe .

Ya kalleni yace baby waye kuma wnn.

Da kyar na daure nace" dashi nazo dama......

Tsawa Ahmad ya min hade da fadin ki wuce mota ki jirani.

Tab! Nan ko ake yinta ina zan iya barin wnn hadadden gaye?

Na fada a raina don haka na dake nace" gaskia king ni ba yanzu zan tafi gida ba kawai kaje daga baya na taho.

Ya dubeni fuska a daure yace "ko?

Na ce " sosai ma.
Ya gyada kai sannan ya kalli mutumin yace" ina maka last warning akan wnn babyn idan ka kuskura ka sake kulata sai nasa an batar da kai!

Ran gayen ya mugun baci yace" kai waye da zaka sa a batar dani?

Ahmad yace" sai ka kulata din zaka gane.

Ya finciko hannuna yana jana ina tirjewa har bakin mota ya bude bayan motar ya jefani ya kulle

Ya zagayo ya shiga ya zauna ya tada motar.

Nikam ban iya nace komai ba a halinda ake ciki ma jina nake sama sama kamar a gajimare.

Bansan ma me ake ciki ba kawai sai ji nayi ya fincikoni waje yace" ki bude idonki da kyau ki gani nan kofar gidanku ne na kawoki ga can Dan iskan yayanki sojan nan yana tsaye yana ganinmu sai kije Ku karata tunda 'yar iska ce ke.

Yana kokarin sakeni na damkeshi cikin maye nace mishi" ba komai kai ni.....wurinshi...kasan ...nasha da yawa bazan iya tfy ba.......

Yace " yayi kyau tunda haka kika zaba .

Ya riko hannuna har wajen ya salman. Da take tsaye mamaki da tsoro ne ya rufe shi ganina a cikin yanayin maye kuma karfe sha biyun dare.

Ahmad ne ya katseshi da fadin" ga nan kanwarka na dawo maka da ita sai ka kaita gida.

Bai ce komai ba ya kamoni yayinda Ahmad ya juya ya shiga motarsa ya fice ya salman ya bi motar da kallo har ya bace daga layin.

Sannan ya kalli fuskata kasancewar akwai hasken farin wata sosai .

A take yaji wani abu ya taso ta tokare masa kirji tsabar bakin ciki ya rasa mai zai ce. Don tunda magriba suke nemana da mama a waya basu sameni ba. Ganin hankalin mama ya tashi yasa shi cewa ya kira kawata kuma tace ina hostel wayana ba chagy shiyasa in an nemeni baya shiga.da haka ya lallaba mama .

Shi ma yanzu abinda ya tsaida shi a waje yana tunanin ta inda zai fara nemana ne.gashi yayiwa mama karya hankalinta ya kwanta shi kuma ya kasa bacci.

Ya sauke ajiyar zuciya ya daukeni cak! Yayi cikin gidansu a Palo ya saukeni kan 3 seater sannan ya koma ya kulle koina ya dawo ya zauna ya zuba tagumi yana kallona

Banma San yanayi ba .don tuni bacci yayi awon gaba dani!!!!!!!!!

Hauly ce👍🏻😍
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```

Page ➡24

*************Nice ban tashi ba sai goma.

Ganina kwance a palon su ya salman yasa hankalina yayi mummunan tashi

Da sauri na tashi zaune ina Salati na bi kayan jikina da kallo anan na tuno abinda ya faru duka

Na zaro ido hade da fadin wayyo Allah na shiga uku ni yau ya zan.........

Shigowar ya salman ne ya katseni.nan naji wata irin faduwar gaba da ban taba ji ba tsoro ya lullubeni jira kawai nake naji saukan duka.

Kaina a sunkuye na kasa yarda muyi ido hudu.

Zama yayi akan kujera ya kalleni cike da bakin ciki mara misaltuwa ya hadiye bacin ransa yace" sai yanzu kika tashi?

Jikina a sanyaye kunya ne ya rufeni sosai na zamo daga kan kujeran na durkusa gabansa nace" yaya kayi hkr don Allah wlh sharrin shaidan ne.

Kauda kansa yayi yace ki shiga dakina akwai kayanki a gado ki saka sai kizo.

Kunyane ya dada lullubeni na mike a hankali na shiga daki na sami dogon rigata na atamfa da hijabina na saka na bar masa mini skirt din da vest akan gadon na fito sai lokacin ya kalleni sannan ya mike yace " muje gida.

Cikina ne ya duri ruwa na zazzaro ido waje ina tunanin me zancewa mama in naje.

A karo na biyu yace muje mana.

Anan na kalleshi nace " yaya dama ina son inje toilet ne fitsari nakeji lol!

Baiyi magana ba ya koma ya zauna ni kuma na wuce toilet na fi minti goma a ciki ina tunanin karyar da zanyiwa Mamana.

Haka na daure na fito.

Muka fita INA biye dashi har side din mama.

Muna isa sai naga ya kamo hannuna ya riko yayi sallama .

Mama dake Palo ta amsa hade da yi masa iznin shiga.

Ganinmu tare yasa ta mike tana cewa" zuwa kayi ka dawoda ita? ai da ka barta muga iya gudun ruwanta.

Ya girgiza kai yace " goggo ba haka nan taki dawowa ba.zazzabine ya rufeta shine sukaje asibityn makaranta suka mata allurai hade sa mata ruwa banason hankalinki ya tashi gashi dare yayi shiyasa ban fada miki ba .shine dazun da zan tafi asibityn na tura Zainab ta karbo kayanta don sunce wancan ya baci da amai.shine da naje suka sallamota.

Ya kalleni ni kam kaina a sunkuye ina mamakin yadda yaya ya zage ya na shirga karya hankalinsa kwance.

Yace" kije ki kwanta bari in je in siyo magani.

Ya saki hannuna sai lokacin mama tace" sannu rumaisa Allah ya sawwaka .amma INA wayarki in mun kira muji a kashe?

Nan na tuno gabadaya jakata ma na motar Ahmad .na dago na kalleta bansan me zance ba.

Ya salman yayi farat yace" sunce ba cajine kuma sun bari a hostel

Mama ta ce" OK.jeki kwanta bari a kawo miki abinci.

Na wuce daki na cike da mamaki ya salman me yasa yake rufa min asiri?
Chapter 27 · 0% Book details