← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 128

Sashe 74

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nikam da sojana mun shimfida rayuwar soyayya kamar zamu hadiye junanmu.in yana gida har kitchen tare muke zuwa wanka tare in ya tafi aiki kuwa ina indai ya samu sarari sai ya buga min waya ko yace in turo masa hotan kwalliyata da English wears musamman kirjina O! Ni Rumaisa ya Salman dan duniyane.

Karkuso kuga yadda na dada kyau da haske gwanin sha,awa duk Wanda ya kalleni sau daya sai ya kara don haka nema ya salman ya hanani sa gyale in zamu fita sai dai hijabi.

Ana Azumi saura kwana biyu ne ranar naji anata mana knocking na kofa dama ina waya da sakina ne don haka na tafi da sauri na bude kofar.

Watace na gani saida zuciya ta ta buga don daga gani ' yaruwarsu ya salman ne na cameroo don gata kamanninsu duk daya dasu adda A'i kyau kam kamar su sukayi Kansu.

Ganin ina tsaye banyi magana ba yasa tace " lfy .

Murmushi nayi na karfin hali nace " ai ke za,a tambaya.

Tsaki taja hade da fadin " kaji rainin hankali nan ba gidan ya salman bane?

Nace " eh nan......

Tun ban karasa ba ta dauki jakarta ta tureni da karfi saura kadan in fadi tana cewa" dan Allah malama ni ki bani hanya kin tsaya kina batama mutane lokaci.

Binta nayi da kallo hade da fadin " hmm another trouble.

Na rufe. Kofa bance mata komai ba na tafi daki na tarar ya salman sai baccinsa yake hankali kwance don haka bana son in tasheshi.

Dole na koma Palo na kalleta nace " yayan na bacci.

Hararata tayi hade da fadin " nuna min dakinda zan sauka don ba yau zan tafi ba dadewa zan yi .

Nace " to ai ba matsala.

Sai cewa tayi " hmm in ma dashi ina ruwaana.

Nidai shiru kawai na mata yayinda na dauki jakar kayanta na kai mata dayan dakin da yake kallon namu.ba komai a dakin daga katuwar katifa sai wardrobe na jikin gini.ga kuma toilet.

Saida ta tsaya ta karewa dakin kallo tsaf snn tace" hmm ki bani tsintsinya wnn daki naku kamar akurki sa,a daya akwai Ac da bazan zauna ba.

Ni dai yau ina ganin ikon Allah.bayan na kawo mata tsintsiya na dawo Palo ina zaune ya salman fito dagashi sai vest da boxer.

Murmushi na masa nace" yaya har ka tashi
Zama yayi kusa dani hade da fadin " wayo kk min kk sani bacci shine kk gudo Palo ko?

Dariya nayi hade da fadin " wlh yaya na gaji ne.

Yace" anya baby ba Amarya zan kawo miki ba? Don kefa bazaki iyani ke kadai ba saida mataimakiya ko?

Nan da nan yanayin fuskata ya sauya na fara fushi.

Yayinda ya shiga ratrashina.

Muna cikin hakan mara kunyan ta fito don ni bansan sunanta ba.

Wando tasa 3quarter da vest ta sake gashunta dayasha kara yayinda kamshin turarenta ya rigata fitowa.

Tana fita ta sakarwa ya salman murmushi .shi kam lokaci daya daya ganta annurin fuskarsa tuni ta gushe ya tamke fuska tamkar bai taba sanin maiye dariya a rayuwarsa ba.

Ni kuwa haushin suturarta naji kamar nayi yaya da raina.

Cike da fara tace mishi " yaya yau kam na cika alkawari nazo......

Rai bace yace" wnn wane irin iskanci da rashin kunyane haka ? Don Allah koma ciki ki nemi kayan mutinci kisa wawiya kawai.

Dan zumbura baki tayi snn ta juya tayi cikin daki tana guna guni.!!!!!!!

Fans ayi hkr rasuwa aka Mani!!!!!🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Hauly ce🤗🙏🏻
[9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡68

***********Hankalina ya tashi matuka da zuwan madiha ya salman har ya gane don haka yace in hankalina bai kwanta ba to gara fa ta koma .

Nace" aa wlh babu komai

Yace " Rumaisa nasan kina tsoron abinda ya faru ne kwanaki amma karki damu insha Allah bazan kuma sakaci da kaina irin na baya ba kuma a koda yaushe ina alfaharin kasancewar ki abokiyar rayuwata Allah ya maki albarka.

Murmushi nayi zuciyata fess nace amin yaya na.

Yace " ina fatan kin yi niyyar azumi?

Nace " sosai ma ka ma tuna min bari naje na fadawa madiha don kila bataji ba.

Yace " OK kuma idan ta maki rashin kunya ki fada min inje in sameta.

Murmushi nayi bance komai ba na fita zuwa dakin da madiha ta sauka.

Na samets tayi bacci don ga laptop din ta ta kunna tana kallon film koda na matso sai naga ashe bf ne abun ba kyaun gani .har naji zuciyata ta tsinke.

Da sauri na kauda idona na fara tashinta.

Wani dogon tsaki taja hade da fadin wai mene ne ?

Nace " ya salman yace a fada miki ki kwana da niyyar azumi gobe snn kuma madiha a matsayinki na musulma ina baki shawara ki daina ganin irin wadan nan films babu kyau masifa ne........

Hannu ta daga min hade da fadin " ina ruwanki ne wai rayuwar ki ko tawa?

Nace " hmm taki ce amma dai na fada miki ki gyara.

Mtswww taja tsaki hade da fadin " naji amma in kina son ganin na bari ki bawa mijinki shawara ya aureni domin ina son shi .

Murmushi nayi nace " Allah sarki mijina ya maki nitsa kwata kwata va kya jerin matanda yakeso.

Na dafa kafadanta nace " madiha tunda kk zo gidan nan nasan dalilin da ya kawo ki .am sorry to say yayana bazai iya auren mace irinki ba zaki gama yayinki ki koma ne yadda suhaila ,nabila da sukhaina sukayi suka barshi ......

Tura hannuna tayi a kafadarta da sauri ta mike hade da fadin " hmm ni MADIHA na wuce tunaninki Rumaisa ban taba neman abu a rayuwata na rasa ba don haka ya salman ma na sameshi na gama kuma wlh wlh wlh kinji na maki rantsuwar musulunci idan na auri ya salman sai ya sakeki ! Ki rubuta ki ajiye.

Dariya nayi sosai snn nace " ni kuma madiha ina mai tabbatar miki da cewa karo na farko a rayuwar ki zaki rasa abinda kk so don ba zaki taba samun salman ba salman nawa ne ni kadai! Ki rubuta ki aje.

Ina gama fadin haka na fita ba tare da na kula da bakaken maganganu da take jifana dasu ba .

Koda na koma daki na tarar da ya salman yana waya da inna nasa key a kofa hade da kashe wuta nazo na kwanta kusa dashi.

Da asuba koda muka tashi dama na rigada nayi mana miya tun dare so tuwon semo na tuka nasa a kula ya salman ya kaiwa hassan don har zuwa lokacin bai dawoda silfa ba shi kadai a gidan.

Madiha kuwa kin fita tayi har muka gama duk abinda muke yaya yaje massllaci ya dawo muka koma daki muka kwanta.

Sai nine ya salman ya tashi yayi wanka ya shirya don koda nazo taimaka masa cewa yayi karna tabashi azuminsa ya karye.

Don haka koda ya gama na rakashi a Palo muka sami madiha yau ma tasha English wears musamman kirjin nan kusan kadan ne a cikin rigan komai nata a waje tana zaune a dining tana shan tea.

Gabadaya kallonta mukayi ya salman ya tamke fuska sosai hade da fadin " ke !bakiyi azumi bane?

Ta juyo ta kalleshi hade da shagwabe fuska tace " ni yaya inada olsa ne banayin.......

Da sauri ya tari numfashinta da fadin " don Allah rufe min baki mara kunya dama ai ke ba damuwa kkyi da ibada ba inaga aljanun kanki arna ne kekam .kuma ki tashi maza kije ki cire wadan nan shaidanun kayan idan kk kuskura na sake ganinki da wadan nan banzan shugan wlh zaki yabawa aya zakinta nonesense !

Tashi tayi tana gyara gaban rigarta snn ta wuce ciki tana kada mazaunai hmm! Ikon Allah sai kallo.

Tsaki yaja snn ya kalleni yace" ke kuma ba barinta zakiyi tana rashin kunya son ranta ba taka mata birki zakiyi domin wlh rashin kunya irin na madiha ya wuce yadda duk kk tunani.

Yana gama fada ya fita ransa a bace dama yaya........

Tunda ya mata fada akan kananan kaya ta daina sawa azumi kuwa dole yace sai tayi in kuma taki to sai dai ta koma inda ta fito.

Tayi guda biyu rak rannan da daddare kawai muka jiyo ihunta muka fita da sauri a Palo muka samets rike da kirji wai kirjinta na ciwo

Koda ta samo ya riketa gabadaya ta narke a jikinsa acikin daren muka kaita clinic ba komai sukace ba illah suka rubuta maganin olsa.

Tun ranar da taga ya salman ya fara sassauta mata shikenan sai tadinga matsa mana muna shiga daki da daddare take zuwa tayi mana knocking na kofa wai kirjina nta na ciwo bata son kwanciya ita kadai kar wani abu ya sameta cikin dare kuji min iskanci.

Haka ya salman yake cewa inje mu kwana da ita .

Duk ta takura ma na ya salman duk ya rasa yanda zaiyi gashi azumi ne in gari ya waye shikenan ba harka.

Mun kai 2 weeks madiha tana ta mana wnn iskancin.

Da rana kuwa garau dinta wuni take rawa ta kunna music maimakon wa,azi ba daman zama a Palo dole nake wucewa daki in kunna wa,azi inajin abuna .

Ranar kawai sai gashi ya dawo yayi mantuwa don haka ya sameta a Palo ta kunna music tana rawa.

Aikuwa ya zuba masifa ranar saura kadan ya mata duka nice na bashi hkr da kyar amma har ya fita masifa yake tayi.

Da daddare kuwa yace tunda abun nata iskanci ne ita kadai zata kwana ni in dawo daki.

Ya kuma ce mata wlh idan kk kuskura kk kwankwasa mana kofa idan na fito sai na harbi kwakwalwarki da bindiga!

Zaro ido tayi a tsorace hade da fadin " kayi hkr yaya.

Yace " tashi ki tafi ki bani wuri mara kunya kawai.
Chapter 74 · 0% Book details