← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 128

Sashe 8

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kyar na nuna mata jakana ta je ta dauko ta kawo min ta sa min a hanci ina shaka.amma Sam numfashina bai daidaita ba.

Kawai ta kira Momy ganin halinda na shiga yasa Momy tace kar a bata lokaci mu tafi asibity.

Muna zuwa aka min allura cikin jijiya cikin ikon Allah numfashina ya dawo dai dai.sannan muka dawo gida.

A harabar gida muka ga ya salim da wani sanye da kayan soja.

Nan naji zuciyata ta tsinke don tsabar tsoro don mu a kauye ko police ma gudunsa muke bare kuma soja.

Muna fita suka karaso wurinmu.

Da kyar na iya dagowa jin kamar muryar ya salman yana gausheda Momy.

Aikuwa ina dagowa muka hada ido da sauri na sauke idona nayi ciki da sauri.

Momy da ya salim har hada baki suke lfy rumaisa?

Faiza ne ta yi dariya tace "tsoron ne taga ya salman da kaki.kunsan a kauye police ma na basu tsoro.

Dariya sukayi gabadaya banda ya salman don shi haushi ma yaji.
Momy tace " aikuwa gara ta cire wnn tsoron.

Salman yace" Momy ina kk je ne haka?

Momy tace" wlh tsautsayi ne faiza ta fesawa rumaisa turare a hanci shine ciwonta ya tashi .ba bata lokaci muka tafi asibity don dazun da kyar take numfashi ma.

Ya salim yace" subhanallah! Allah ya bata lfy.

Sukace Amin .

Daga nan suka nufi Palo.faiza ta kalli salman murmushi tayi tace" yayana na shirya maka abinci da abinsha kala kala.

Ba tare da ya kalleta ba yace" nagode.

Bayan sallar isha muka hadu a dining.

Da kyar na iya kallon ya salman ashe ya cire kakin nasa.

Muka hada ido da sauri na sauke idona nace" ina wuni yaya?

"Lfy " ya amsa.

Daga nan naja bakina nayi shiru sai faiza da hakim suke ta zolayata yau dai na kasa sakewa bare in basu amsa.

Muna gamawa na tashi zan wuce daki faiza tace" ke za.a fara BEYHADH yanzu ko kin manta ne?

Nace" aa ni bacci zan yi.

Ya salim yace " ko dai har yanzu ba kya jin dai dai ne?

Na Dan yi murmushi nace " aa Alhamdulillahi naji sauki so nake inje in karasa parking inyi bacci da wuri saboda in tashi da wuri.

Yace" OK to Allah ya tashe mu lfy.

Nace " Amin.

Hakim yace " aunty rumaisa ki tsaya ki gani mn.

Harararsa nayi Na shige ciki.

Fa,iza kam Na gefen ya salman akan kujera ko da muka hada ido ma gwalo ta min.

Da safe kuwa muna gama breakfast muka je muka sallami daddy anan Na kara yi masa Godiya.

Yace" babu komai rumaisa wani hutun ma kizo don munji dadin zuwanki.

Momy tace kwarai kuwa.

Murmushi nayi.

Mun fito harabar gida .
Na gaisheda ya salim sannan Na kalli ya salman shima ni ya zubawa ido Na rasa dalilin yawan kallona da yake tun jiya.

Nace" yaya ina kwana.

Yace lfy.

Momy tace" salman ban yarda da kallon nan da kk mata ba .

Murmushi yayi yace " Momy na ga 'yar kauyen ta canza ne gabadaya.

Sukayi dariya Momy tace tukunna ma.kai dai in kana yi ka shigo daga ciki muyi ' yar gida gida kawai.

Yace " Allah ya sawwaka ni me zan yi da 'yar kauye?

Faiza ta yi Farat tace " yaya ni fa?

Murtuke fuska yayi yace " ke ni sa,anki ne?

Da sauri ta koma bayan Momy .

Salim yayi dariya yace " kai dai kaje kayi tunani duk wacce kaga tafi dacewa da kai acikinsu.

Momy tace " dukkansu ma zamu iya baka my son .

Yace " Momy kuna magana a ga ban yaran nan sai su dauka da gaske su rainani.don Allah Ku bari.

Ya kalleni yace" ke Dan Allah shiga mota.

Dariya suke ta masa.

Daga nan Momy ta mn addua faiza kam har da kuka nima sai da hawaye ya cicciko min ido .

Har mun fara tfy yayi parking ya kalleni yace " yar kauye daura belt.

Na fara lalubowa ganin zan bata masa lokaci yasa ya Dan kwanto jikina yaja belt ya daura min .cikin rashin sa,a hannunsa ya taba bakina sai ga Jan baki a hannun shirt dinsa ya fitar da shape din bakina mai kyau a jikin rigana.

Ya kalli hannun rigar tsaki yayi yace " dubi yadda kk batan Riga da Jan bakinki anya ba da gangan kikayi.

Saura kadan dariya ya subuce na matse nace" yi hakuri ban Sani ba ne.

Baice komi ba ya tashi motar aikuwa gudu yake kamar zai tashi sama nikam kamar Na saki fitsari don tsoro kai ya salman bai da dadin sha,ani.
Ranar da muka zo da ya salim a hankali yake tfy munata hirarmu har muka isa.

Tsabar gudu sai gashi mun iso da wuri ni dai sai hamdala nake ganin mun isa lfy.

Salima ne Na hango ta fito daga cikin gida.

Nikam ina fito da kayana ko kallo bata ishen ba.

Shine ma yana hangota ya saki murmushi kamar ba shi ba.

Ta karaso cike da fara,a tace " oyoyo dear.

Yace " ranki ya Dade gimbiyar mata.yaushe kk dawo?

Tace hmm nima dazu Na dawo ai bansan kana Abuja da mun taho tare .

Yace "waya gaya miki ina son ki yi taravelling by road ?

Murmushi ta yi tace " to kaima ka daina.

Murmushi yayi ya harde hannayensa kan kirji yana kallonta

Anan ta ga Jan baki a hannun rigarsa nan da nan yanayin fuskarta ya sauya .

Ta kalleni harara Na watsa mata naja akwatina.

A fusace ta juya zata tafi yace" zo kiji Salima.

Bata ma saurareshi ba tai tfyrta.

Har zan shiga gida ya tsaida ni ya karaso yace" me kk mata ta yi fushi?

Nace" ni ban mata komi ba.

Hade fuskarsa yayi yace " Na lura da irin kallon banzan da kk mata wlh zan mugun bata miki.daga yau in kinganta ki girmama ta ki gaisheta kina jina ko.

Cikin jin haushi Na amsa masa " eh .

Ya wuce ciki Na bishi a baya.
[05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```

➡ page 7

Ina dawowa washegari na tafi gidan mama.

Nine ban dawo ba har ana gobe Monday driver ne ya dawo dani.

Na sami ya salman a waje yana zaune shi kadai .

Nan da nan na murtuke fuska don tun randa muka dawo Abuja da yamun magana akan Salima nake jin haushinshi.

Da kyar na iya fadin " yaya ina wuni?

Kai kawai ya daga min .nashiga ciki .daga inna harsu sadiya ba Wanda ya min ko sannu nima ban ce musu ba dakin mama na wuce muna hirar school da sakina.

Tun ranar na daina kulasu in dai na gama aikina ciki zan koma inyi kwanciyata wayana nane abokin hira na a yanzu.in dai kaga fara,ata to na tafi mkrnta ne ko islamiyya.

Har ya salman ya koma Lagos bana kulashi.dama ba wani kula juna muke ba.

Lokaci na tfy gashi har mun kusa mu fara WAEC don haka Abba ya biya mana jamb dukanmu mukayi kuma duk mun ci sa,a sadiya ce kawai ta fadi faiza munyi waya tace ta haye.

Haka nan WAEC and NECO nida sakina da faiza munci amma sadiya da raihana duk sun fadi.

Bakin ciki gun Abba da ya salman ba,a magana inna dai ko ajikinta zugasu ma take suyi aure wai su huta.don har ta sami Abba da maganar.

Yace shikenan tunda haka suka zaba ko wacce ta turo Wanda zata aura ko cikin satin zai musu aure.

Inna kam farinciki sosai take.

Da farko ya salman yaso ya roki Abba akan kar ya auradda su amma da ya tuna irin kwashe kwashen samarin da suke sadiya kam nata daban ma don har aka barta gaba kadan zata janyo musu a in kunya.don haka ya shafawa kansa lfy.
Nidai ina shan Hutu gidan mama .har ma na sami admission na BUK sakina kuma ABU a tare da faiza.

A haka aka saida maganar auren su sadiya .yanzu sati biyu ya rage.

Dole na tattara na dawo don mu fara shirye shirye don mune kawayen raihana.faiza ma tazo.don haka a tare muke ta tsula tsiyarmu.

Mama tazo sai dai a sashin kawu kasim ta sauka tare suke da momyn su salim na lura Sam Sam bata shiga harkar inna sai dai mmn sakina.

'Yan kamaroo sun cika gida inna sai fulatanci ake ta yi .kyawwawan mutane wlh gasu farare sannan na lura ko wacce mace bakinta baki irin na inna ko me suke shafawane oho.

Ranar walima a wani filin ya salman da salim muka shirya zamuyi kuma kusa da gida ne sosai aka zo aka mana decorating din wurin yy kyau.

Kawaye munsha ankon material mai kyau.

Salima ma tazo anci adon nan kam kamar hauka sai ji da kanta take tana zuba yanga ta fito da iPad dinta sai hotuna take ma amare.

Ni da faiza kam duk mun cika da haushinta faiza ta Ciro nata iPad din tace" rumaisa zo muje muma muyi photo.

Na tashi muna rikeda hannun juna har muka isa inda saliman take faiza kam sai da tasan yadda ta yi ta bangajeta.

Da sauri Salima ta juyo tace" malama ba kya ganine kk tureni.

Faiza ta juyo ta kalleta a wulakance tace" o Ashe mutum na ture sorry fa.

Wani irin kallo tayiwa faiza sannan tace" da gangan kk tureni kenan ......

Harara na sakar mata nace" ke Dan Allah yiwa mutane shiru an tureki din sai me?

Ta yi saurin fadin ke banyi magana dake ba kija bakinki ki mn shiru na lura Sam bakida kunya.

Na tako na isa gabanta na kalleta nace " Ashe kin gane .gaskiane banda kunya ko kadan kuma kk kuskura kk yi magana anan zaki ga yadda zan yi dake.

Faiza ta harareta tace" kinji ai.

Shiru ta yi tana kallonmu.

Nace ' kuma wannan da kk gani itace matar da ya salman zai aura don haka ki daina mafarkin kece matar ya salman.

Naja hannun faiza muka tafi.

Dariya muka ringa yi nace faiza wlh ta tsorata.
Chapter 8 · 0% Book details