← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 128

Sashe 18

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya salman ma rabonda da in kirashi har na manta dama shi ba kullum yake kira ba sai da dalili.

Watarana bayan mun fito lectures Salima ta karaso wurinmu suka gaisa da su Juliet.

Ni ko kallonta ma banyi ba ina kokarin neman Ahmad.

Ta kalleni tace Rumaisa inada magana dake mu biyu.

A yatsune na kalleta sannan na cire idona na wuce gaba ta biyoni muka sami guri muka zauna .nace" ina jinki.

Ta dan numfasa tace" Ya salman ya wulakantani duk soyayyar da mukayi a baya.maganar da nake miki yanzu saura sati biyu aurena da yaya Ahmed.amma sai na lura abubuwa da yawa na faruwa .kar dai kice min soyayya kukeyi ?

Nace " ni faa har yanzu ban fahimci dalilinki na ajiyeni anan ba kawai kin tsinke da bani labarin da be shafeni ba.kinga in bakida abin fada ni inada abinyi a gabana da yawa.

Na mike har zan tafi tace" just a minute rumaisa.

Ba tare da na juyo ba ta zo gabana tace" So nake ki rabu da Ahmad domin yanzu kiris ya rage ya zama mijina ki yanke duk wata alaka dake tsakaninki da shi domin ya fi karfinki kin rigada kinyi sake tun farko .amma duk da hakan ma kin ci rabonki tunda gashi har kin sauya tashi guda hmm. Sai ki godewa Allah.snn kije ki nemi wani don Ahmad kam ya miki nitsa.

Murmushi nayi nace" shikenan abinda zaki fada min din?

Tace" shikenan sai a kiyaye kuma don a zauna lfy.

Na gyada kai nace" to ba damuwa.

Daga nan wucewa nayi na barta a gun tana bina da kallon mamaki.

Da yamma muna gurin shakatawa da Ahmad ya kalleni yana murmushi yace" Queen yau baza kisha ice cream bane ?

Nace" no yau banjin sha,awar komi kuma ma ina tsoron asmana kar ya tashi.

Yace" eh to hakane amma yau dinma fa ban fahimci yanayinki ba.ko zuwa wurin koyon driving dinma kinki muje yau.

Nace" hmm ai ni yanzu na zama expert kai da kanka shaida ne .

Dariya yayi snn yace " hakane yanzu kam saura ki jira zuwan motarki.

Nace " wa! Rufa min asiri me zance a gida?

Yace,ke wai yaushe zaki waye ayi harka dake?

A raina nace" hmm ai kawai biye maka nake inci rabona kuma in kece raini inyi suna kuma a BUK.in kafa tarihi in zama abin kwatance .

Na kalleshi nace" ba wnn ba my king.Ashe kai kuma tsakanina da kai har akwai wani boye boye?

Yace " me ya faru Queen?

Nace " hmm naji ance aurenka da Salima har saura 3 weeks shine baka sanar dani ba?

Dariya yayi yace O my Queen come on dama akan wnn ne kk ta daure fuska tun dazu? Ni wlh ban dauki aurena da Salima da mahimmanci ba don wlh ni bana sonta amma su dad sun dage sai nayi aure wai don in shiryu kuma in nitsu.bayana na fadawa daddy duk abubuwanda nakeyi dinnan ina son in more kuruciyata ce kawai amma nayi mishi alkawarin in nayi 40yrs duk abinda nake zan tuba in bari kuma nayi aure.amma dad yaki saurarena sai lika min ita sukeyi kawai na rabu dasu suyi kawai ni ba ruwana da shirye shiryensu don haka kar ki damu.

Murmushi nayi a raina nace" Salima ina tausayinki. ba,a banza ya salman ma yake tausayinki ba ashe.

Na kalleshi nace" to ni dai ina rokon alfarma daya a gunka idan ka min wnn ka gaman komai.

Yace" wane irin alfarmace?

Nace" so nake ka nisanceni har tsawon wata biyu.kaje kayi hidimomin bikinka kuci amarcinku in kun gama sai ka dawo kaga ai ban shiga hakkin Salima ba ko?

What! Ya fada sannan ya girgiza kai yace" bazan iya ba Queen.kuma waya gaya miki ina sha,awar sex yanzu? Ni faa ban gama more rayuwata ba tukun don haka bazanje in kula Salima ta yi ciki ba.haka kawai azo ana kirana da daddy kwana biyu na tsufa ? No ba haka na tsara rayuwata ba Sam don haka karki damu kanki da zancan wani amarci not now.

Hmm Ahmad knn na fada a raina snn nace" to naji wnn ra,ayinka ne .amma ni ina son ka nisanceni mu kasance a waya kawai in ba haka ba wlh ' yan uwanka suka gane muna tare ko ya salman akwai matsala tunda gashi zasuce kayi aure kamata yayi ka nitsu.don haka dole mu canza taku.

Yace,waya gaya miki ina tsoron wasu su gane muna tare wlh ni duk duniya in zasu San ina tare dake ba damuwata bane.

Nace to don Allah ka taimaka min ni dai bana son a Sani.

Ya danyi shiru snn yace hmm matsoraciya ce ke wasu lokutan to naji indai wnn ne tunda kince zamu kasance a waya.

Na saki murmushi nace" yawwa my king Na gode sosai

Daga nan yace mu tafi ya ban key din mota da kaina na tuka har cikin mkrta nan mukayi sallama.

Tun ranar bai kuma zuwa ba sai dai mu yita vedio call da daddare .

A kwana a tashi sai gashi an soma biki ni dai banje ba duk da magiyar da ya dinga min amma na ki yarda.

Ranar Saturday sai ga wayan ya salman abin har ya ban mamaki don mun dade bamuyi waya ba.

Bayan mun gaisa yace " nazo ina gari tun Monday amma baki Sani ba .

Nace,wlh kuwa yaya ba Wanda ya gaya min

Yace " to ki shirya anjima in ba kida lectures zamuzo da Wanda na fada miki din domin Ku fahimci juna.

Nan take yanayin fuskata ta sauya kamar nayi kuka ni me yasa na amince masa ne ?gashi kuma ina tsoron ince mishi na fasa.

Haka na daure jikina a sanyaye nace" to yaya sai kun zo .

Ya amsa hade da katse wayarsa.

Nafi awa daya ina zaune ina tunanin mafita.kai nifaa inaga zan fito baro baro ince mutumin baimin ba kar in cuci kaina a banza.

Can karfe uku da rabi ya sake kira wai har sunzo ya fada min inda suke.

Kirjina sai dukan uku uku yakeyi na daure dai na tafi gaban mirror na sake gyare fuskata da powder na shafa lipstick kadan dama less ne a jikina swiss mai kyau army green da adon pink don haka takalmi na da gyalena pink ne masu kyan gaske gaskia ba laifi nayi kyau sai dai ban damu da in birge Wanda yazo da yayaba .

Dan humra kadan na shafa dan ciwona baison turare mai karfi ko Wanda ake spraying shi yasa nafi amfani da humra da kuma kulacca marasa tashi sosai ma,ana masu sanyin kam shi

Lokacinda na karasa mamakine ya bayyana karara a fuska ganin shi da ya salim ne kawai duk sunsha jumper da hula sunyi matukar kyau sosai.

Ya salim ya fito daga cikin mota cike da fara,a yace" you are welcome gimbiyar mata.

Murmushinda bai kai zuci ba nayi na shiga waige waige ko zan ga wani na duba motar ma ba kowa sai ya salman din kadai ya kame fuskarnan a murtuke ko kallo ban isheshi ba .a raina nace" to Allah na me ke faruwa.

Na daure na gaishesu ya salim ya kalleni cike da fara,a yace kina ta dube dube kina neman wanda yayanki ya kawo miki koh.?
Shiru nayi

Yace" rumaisa karki wahalar da kanki NI NE!!!!!

Ido na zaro cike da mamaki na kalli ya salman wanda har lokacin bai ma juyo ya kallemu ba .na sake kallon ya salim Wanda sai murmushi yake tayi min.

Na shiga uku !!!!

Na fada a raina......

Hauly ce👍🏻😍
[05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

Page➡18

**********Kwanana biyu a gida Sadiya ta haihu.ta sami da namiji.

Wai murna gun inna abun ba magana.hakama Abba don wnn shine jika na farko a gidan.

Amma abin mamaki Sam uban yaki zuwa hakama danginsa abinda ya dami kowa knn don sadiya har kuka ta yi Saida inna tayita lallabata.

Ya salman cewa yayi ita ta jawo.

Ranar suna ma shiru ba uba ba danginsa anan fa inna tace sai taje ta samesu taji dalili.Abba yace kar ta kuskura taje bama ita ba kowama yaje ko ya tanka bai yafe ba abarsu kawai.don haka ya sawa yaro suna Abdulwahab.

Bayan mun gama hidimar suna ne Auren Ahmad ya tashi da salima.
Abinka da bikin manyan mutane duk inda kaje zakaji anata sanarwa tuni hotunansu ya yadu koina na pre wedding a social media's.

Ina zaune a palon inna ina shirya Abdul bayan an mishi wanka Ahmad ya turon hotunansu.

Gaskia sunyi kyau sosai ina kallo ina murmushi a raina nace ba girin girin ba dai ta yi mai.

Sadiya ta shigo na kalleta nace" yawwa ki shirya ki zo ki karbi Abdul zan wuce makaranta ina da lectures shadaya.

Tabe baki ta yi tace" ke dai baki son rike yaro na lura ko ya zakiyi da naki oho.

Ban kulata ba ta wuce ciki ta shirya ta dawo Palo ta zauna ta karbeshi ta fara bashi mama.

Har zan tashi ta kalleni ta yi kasa da murya tace" yawwa rumaisa don Allah in kin fita kina ganin ja,afar?

Nace" eh ina ganinsa sai me?

Tace" kiyi magana a hankali kar inna ta jiyo ki.

Ta shiga dube dube snn tace " so nake ki rakani gunsa da daddare.

Tabe baki nayi nace" ki masa me.

Harara ta sakar min snn tace " in masa me kk tambaya.to bari kiji zanje ne na mashi wankin babban bargo daga shi har iyayensu bazan ragawa kowa ba sai nai musu rashin mutuncinda basu taba tunani zan iya ba....

Na tari numfashinta da fadin" to shine me inkinyi hakan?

Tace" kinga in zaki rakani ki rakani in kuma baza ki rakani ba ki fada min kawai .

Tsaki naja nace " bazanje ba ko da kuwa neman tsulhu zaki bare kuma neman fitina.bari kiji Sadiya in kin manta ni ban manta ba anan nayiwa raihana magana kikazo kk hada ni da inna kuka zageni don haka ba ruwana da abinda ya shafi rayuwarku........
Chapter 18 · 0% Book details