← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 127 OF 128

Sashe 127

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta tashi da sauri ta fita.
Munir da hankalinsa ke kan latsar waya tunda muka shigo sai yanxu ya dago ya kalleni yace"mama jikin daddy Alhamdulillah sosai ko yau daddy ya ga dama zai koma aiki.pls hankalinki ya kwanta don gaskia kin rame ga rashin cin abinci kuma.

Nace"Hmm munir kai dai bari.Allah dai ya karawa daddyn lfy insha Allah yanzun hankalina ya kwanta sosai ma.Allah ya maka albarka.

Yace ameen mama nagode.

Ya salman ya shafa kansa yace"ina alfahari da kai good boy.

Dariya mukayi gabadaya daga nan tashi yayi ya sallamemu cike da girmamawa ya fita don yace zai koma asibity ne anata jiransa.

Yana fita ya salman ya dawo kusa dani ya zuba min ido hade da fadin"baby kinganki kuwa ? Irin wnn kyau haka.
Ya kashe min ido daya hade da fadin "gaskia ban gaji ba mu koma ciki .

Dan zaro ido nayi nace"Wayyo yaya dama so nake mu je mu gaida innah fa.

Fuskarshi ce ta dan sauya kadan amma baiyi magana ba.

Don haka na kauda zancen da fadin"yawwa yaya idan ba matsala ina son in rokeka alfarma guda biyu.

Yace"uhm ina jinki.

Nace"ina son dama farida taje yola ne tayi 2weeks akwai shirye shiryen da zasuyi da aunty samira.snn abu na biyu kuma don Allah yaya idan ba matsala a daga bikin nan zuwa next month don kaga gabadaya dis month muna da bukukuwa Abdul din sadiya da amira snn ga nabilan raihana.ana gama nasu da 2weeks sai na gidan sakina kuma wanda gabadaya inaga bazaiyiwu a hada da nasu farida anan ba zirga zirgan zai mana yawa.so pls yaya a duba dai a daga zuwa next month din don Allah.

Shiru yayi kamar bazaiyi magana ba snn yace"sai na tuntubi salim tukun na.

Murmushi nayi don nasan ya salim baida matsala .

Daga nan na sake masa maganar zuwa gaida su innah haka dai na lallabashi driver ya kaimu.Inna taji dadin ganinmu sosai sai nan nan take dani ta kawo mana lemo kala kala ta sake kawo mana fruits .

Ta kalleni cike da fara,a tace "rumaisa ko akwai abinda kike sha,awa ne insa a dafa muku.

Fuska sake nace"babu komai inna wnn ma yayi.

Na fada yayinda na dauki apple na fara ci.

Muka gaisa ta tambayi ya salman ya jiki ya amsa mata da Alhamdulillah.

Hmm zakusha mamakin yadda mukayita shan hira da inna kamar ba ita ba har tana bani labarin rashin lfyr mijin adda A'i yayi tsanani sosai yanxu har sun fita kasar waje jinya.

Cewa nayi Allah ya bashi lfy.
Tace"ameen ita wancan shashashar ince dai ta nitsu a gidan yayan naki ?ko dai tanayi musu rashin kunya da fitsara?

Nan na fahimci nafisa take nufi nace"aa wlh lfy lau suke zaune inna kinsan fa ita nafisa bata da matsala gaskia yanxu haka ya hafiz yace mun ta samu bazawari wani abokinshi doctor ne babba yana Abuja ya dage yana sonta zai aureta.

Inna ta tabe baki tace hmm ni tsorona kar taje taja mana abun kunya don wlh tsoron wayan nan yara nike ji.

Murmushi nayi nace"babu komai innah ki musu fatan alkhairi.

Tace "to hakane Allah sanya alkhairi.

Nace amin daga nan muka dauki hirar bikin farida.ya salman dai bai sa mana baki ba dama shi bai cika sa baki ba a maganar da ba tashi ba.sai dai ya fara jin sassauci a zuciyarsa ganin yadda inna ta fara sona gashi a cikin kankanin lokaci har na saki jiki da ita muna hira sosai.fatansa Allah sa hakan ya dore.amin.

Tuni na tura farida yola nan fa muka shiga hidimar bikin gidan sadiya ga na raihana.wnn karon fa,iza ma tazo ga ruma a gidana suka sauka.kusan komai a gidana akeyi sadiya komai sai ta bani shawara takeyi .don haka nasha hidima sosai har muka kammala lfy.mun huta na sati daya kawai muka sake tfy zaria bikin yaran sakina anan ma mune kirjin biki anyi komai cikin kwanciyar hankali aka watse daga nan muka dawo kano harda ruma saboda shirye shiryen auren munir da farida wacce har yanxu tana yola tana shan gyara hmm wnn bikin special ne.

Fa,iza tace "ai dolene muyi mothers night domin zan cashe ba karya.

Dariya mukayi nida ruma snn nace"zamu cashe 'yar uwa a matsayina na uwar ango ace bikin dana guda ban cashe ba ai ban kyauta ba.

Dariya mukayi harda tafawa ruma tace ku dai Allah ya shirya ku wlh gani kuke kamar baku girma bako ?

Fa,iza ta harareta da fadin"ke fa se mun cashe ehe garama karki bata bakinki .

Muna cikin haka ya salman ya leko dakin da sallama muka amsa duk suka gaisheshi ya amsa fuska sake snn ya kalleni yace rumaisa kizo ina da magana.

Daga nan fita yayi fa,iza tana dariya tace"wayyo yaya ya yi missing diin matarshi shiyasa ya zo da kanshi bai tura yan aike ba.don Allah tashi kije asha soyayya lfy.

Harararta nayi bance komai ba na tashi na gyaggyara jikina har zan fita faiza tace"hmm in munji shiru mu rufe kofa ko?

nace"bansani ba?
Dariya sukayi nikam tuni na fita

Ina zuwa dakinsa na sameshi zaune bakin gado hannu ya miko min na karaso na kama hannunsa na zauna ina kwantar da kai a jikinsa a hankali yace"kina min horo kwanan nan my dear .ganinki ma fa da kyar sai na yanki ticket.

Dariya na danyi nace "yaya na zama busyne ai kwanan nan.yanxu ma kaga muna maganar walima ne da dinner.....

Yace"kuma ita amaryar yaushe zata dawo kunje kun boyeta a yola ko bikin yanuwanta bata zo ba.

Murmushi nayi nace"kasan ita amarya boyeta ake dama anfi so ta kasance cikin hutu.kaga inda ace anan take ta dinga zirga zirga knn tayita tarawa kanta stress.amma yanxu acan ba ruwanta da wani zirga zirga mun fiso sai ana sauran kwana hudu daurin aure ta dawo.

Gyada kai yayi cikeda gamsuwa yace"gaskiane.to shi ango ba,a boyeshi ya huta ne? Good boy tausayi yake bani kwanan nan baya ko hutawa sai zirga zirga ga abokansa duk sunzo .

Dariya nayi nace"ka taba ganin ango ya huta lokacin bikinsa?ai shi dolene kawai ya zama busy.itama faridan da ba don mimi na nan zata kula da duk wani abunsu na kawaye ba da dolene kawai ta dawo.

Yace"gaskiane.itama mimi naso a hada bikinsu da farida in yaso in anyi bikin fadyl din ya koma karatun nasa amma yanxu sai an jira ya gama har zuwa next year sai nakega yayi nitsa.

Nace"babu komai akwana a tashi sai kaga nan da nan lokacin yazo ai ko ita sakinan taso fadyl din ya hkr ayi bikin duk da na kannesa da mukayi kwanaki.amma ta lura yafi son sai ya kammala karatunsa ya dawo kuma kaga itama mimin bata damu ba.don haka muyi musu fatan alkhairi dukansu.

Ya gyada kai hade da fadin "hakane Allah ya sanya alkhairi.

Murmushi nayi nace"ameen maigida ran gida.
Dariya yayi yace kodai uwargida ran gida?
Nace"duka.

Snn na dan taso daga jikinsa nace"kaga bari naje su fa,iza suna jirana ....

Da sauri ya rikoni da fadin ina zakije kuma ai kawai su hkr sai gobe yanxun lokacinane.

Nace"yaya wlh zolayata zasuyi tayi suce har yanxu bamu tsufa da soyayya ba.

Murmushi yayi yayinda ya kwantar dani kan gado shima ya kwanta muna fuskantar juna sosai yace"hakane bamu tsufa da soyayya ba kuma insha Allah in da rai da lfy baza mu tsufa da soyayya ba my dear.domin kullum jinki nake kamar wata budurwa Allah ya baki ni,ima da wata baiwa wanda ni kadai nasan kayana.a cikin mata 100 samun irinki yana matukar wahala.karkiga laifina idan ina miki sambatu hmm ni kadai nasan irin dadin da nishadi dana keji yayinda na kasance dake my dear.don haka pls a daina min horo da yawa.

Ya fada yayinda ya hannayensa ke yawo a dukkan sassan jikina cikin wani salo mai rikitarwa dole na limshe ido ina sakin ajiyar zuciya.

Fuskarsa ya matso dashi daf da tawa sosai muke exchanging numfashi yayinda kamshin turarenmu ya gauraye wuri daya yana fitar da wani kamshi mai dadi da sanya zuciya cikin shauki.

A hankali yace"my dear ke din special ce bazan gaji da gaya miki ba.

Ya manna bakinsa da nawa.daga nan fa..........

Su fa,iza sai da safe suka ganni aikuwa tayita zolayata harda ruma.ni dai bance komai ba a ranar sakina ma tazo.

Haka muka ci gaba da gudanar da shirye shiryen bikin cikin farin ciki.tuni gida ya cika da yanuwa da abokan arziki amarya ma ta dawo hmm sai kunga yadda ta koma fresh fatar nan tayi kyau ga laushi wani haske ta kara na musamman yayinda kamshi ke tashi a jikinta ta ko ya ya ta motsa gashi tasha kunshi mai kyau da jan hankali haka gashinta ya sha gyara.batun can kam ba,a magana wnn sai ango ne zai bada bayani lol!

Su madiha sunzo nafisa kam tayi sati ma a gidan don duk wasu hidimomi da ita mukayi tareda sa,adatu yadda ta saki jikinta damu kamar ba abinda ya taba faruwa a baya.adda A'i ce kawai bata zo ba itama saboda jinyar mijinta da suketayi.ciwo dai yaki ci yaki cinyewa don sunce ciwon koda ne.sai faman kashe kudi ake tayi.

Haka hidimar bikin ta kasance cikin farin ciki yayinda yaya salman ya baza sojoji ta koina ana bamu tsaro ta musamman don mun sami halartar manya mutane na kasa.salima ma tazo hakama Ahmad yazo daurin auren kuma ya nemi ya salman da ya yafe masa abubuwanda suka faru a baya ya salman yace babu komai ya wuce shima kuma ya yafe masa.Allah sarki rayuwa.

Haka bikin ya kare babu wata tashin hankali ko hayaniya Amarya ta tare a gidanta na nan GRA don bamu da nitsa sosai ya salman yace baison suyi nitsa damu.

A hankali aka dinga watsewa har ya rage gida sai mu kadai .khalil ma Abuja ya koma don sun gama secondary suma can za,a turasu malaysia karatu shida salman junior.
Hanif da Hanifa kuwa har lokacin suna gidan mama don sun saba da ita ko ya salman ya kawosu yini basu yarda sun dinga kuka se an maida su gun mama.

Nafisa ma an yi bikinta da abokin ya hafiz doctor jalal.a Abuja suke zaune hankali kwance.
Chapter 127 · 0% Book details