Sashe 115
Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta fada hade dan kwantar da kanta kan hannu kujera dab da ya salman a shagwabe tace "ko bacci banyi sosai fa.
Inna ta washe baki cikeda farin ciki tace"masha Allahu.aikuwa gashi na gani duk wata alama na mai juna biyu ya bayyana a jikinki.
Da sauri nafisa ta dago kai tana kallon innah ta rasa me ma zatace kawai ta maida kai ta kwantar ta kama sharbar hawaye.
daga innah har ya salman mamaki ne ya kamasu sai dai shi baice komai ba kawai tashi yayi ya fita domin ya je ya gana da yan anguwa.
Inna kuwa ta shiga rarrashin nafisa tana cewa ke ana samun ciki ana murna kin kama kuka? To kukan na miye?
Nafisa tace"haba goggo ni ko rabin shekara banyi da aure ba zan fara shan wahalar ciki?
Inna tace"wayace miki da wahala ? Haba yar autanmu ai haihuwa ba wahala tsantsar dadine kawai kwantar da hankalinki Allah ya raba lfy.ince dai waccan jarababbiyar bata musguna miki?
Girgiza kai tayi tace"ni bata min komai.
Yace"ta samawa kanta lfy.don wlh in ta tabaki wnn karon sai nasa salman ya saketa.
Tabe baki nafisa tayi batace komai ba.Innah tace"hmm yawwa nafisa ina son ki rokar min salman don Allah ya baiwa sadiya jari itama ta fara siye da siyarwa ta daina zaman nan na banza ga raihana tuni mijinta ya dorata akan harkar kasuwanci har mota ta siyawa kanta bayan wacca mijin ya sai mata a baya.amma sadiya don tsabar mugunta irin na mijinta ba ruwansa da ita bare ya bata jari .kullum na roki salman sai yace min sai ta shirya da kanta ta rokeshi snn zai bata kinsan shi da murdadden hali to ya ma ki ya bata fuska bare ta roke shin kullum suka hadu sai ya kama daddaure fuska.shine nace don Allah ki lallabashi mana ki masa magana ita ma ya taimaka mata ta sami abinyi.
Nafisa tace"hmm ai goggo ita adda sadiyan ne batada wayo ace duk kudin mijinta bata san yanda zata lallabashi ya bata wani abu ba se ta roki yaya wani abu haba dan Allah shima fa yaya yana da hidimomi da yawa a gabansa kuma kwanan nan duk se cewa yake baida kudi ma .
Inna tace"haba nafisa baki ganin halinda take ciki ne kwanan nan duk ya sake juya mata baya dama albarkacin yaranta takeci a gidan.
Nafisa tace"to shikenan goggo zan roki yaya ya taimaka mata karki damu.
Inna tace"yawwa yar autanmu Allah ya miki albarka ai tunda salman ya samu mace irinki yanxun zamuji da dadi sosai fiye da da.don wancan jarababbiyar.....
Nafisa ta katse innah da fadin don Allah goggo ki bar matar nan ta huta .bata da laifin komai ku daina aibatata .
Inna ta gyara zama zata fara magana se ga ya salman ya shigo don haka tayi shiru amma magana na cinta a rai.
Ya salman ya kalli nafisa yace"ke mu tafi .
Anan suka yi ma innah sallama suka tafi.
A hanya ya dan kalli nafisa data kwantar da kanta kan seat tana limshe da ido.ya dan rage gudu snn yace"ya kamata muje asibity a duba ki ko ?
Shagwabe fuska tayi snn tace"za,a min allura?
Yace"baza suyi miki ba ki kwantar da hankalinki ai nasan tsoron alluran ya hanaki ki fada min baki jin dadi.
Asibity suka tafi nan doctornda ya saba dubani ya duba nafisa sunyi gwajin ciki aikuwa nan da nan sai ga result ya tabbatar musu nafisa na daukeda ciki.
Murmushi ya salman yayi cike da jin dadi don gaskia yana son haihuwa sosai burinsa yaga gidansa ya cika da yara kota ina.nan da nan ya shiga hamdala yana godewa Allah.
Nafisa kam gabadaya hankalinta ya tashi kuka ta shiga yi mishi wai ita tsoran haihuwa takeji.
Murmushi ya salman yayi ya jawota jikinsa ya shiga rarrashinta yace"babu wani wahala nafisa.
Nan suka dinga mata magana da doctor suna fahimtar da ita.
Har suka dawo gida bata saki ranta ba.don ita kwata kwata bata kawo lissafin haihuwa a tsarinta ba so kawai take ta tara dukiya tayi gaba.
Farida kuwa bayan na fada mata yanda mukayi da salima sai na lura jikinta ya mutu sosai haka ta wuni sukuku yau ba walwala.
Da daddare duk waya da mukeyi da munir nida khalil kallonmu kawai take sabanin da takan ce in gaisheshi.domin bata yarda suyi waya har yanxu shima kuma ya daina tambayarta don ya rigada yasan komai akan abinda ke faruwa don haka yake fushi da ita sosai.ni dai bansan ya lamarim farida da munir zai kasance ba.
Nafisa kuwa ana can turaka ya salman sai riritata yake har da tsokanarta da cewa "maman twins Allah sa ki haifa min twins don ina sha,awar su sosai.
Bata fuska tayi tace"mummyn faridace zata haifa maka twins insha Allah .
Yace"ita triplets zata haifa min ba twins ba.
Dan zaro ido tayi tace"tab hmm bari ta ji ka ni ba ruwana.
Yace"ai ita tana son haihuwa sosai don haka murna zatayi ba kamar ke matsoraciya ba.
Murmushi tayi daga nan shiru ya biyo baya can ta dago ta kalleshi tace"yayah pls ina rokon wata alfarma a gunka.
Yace"fadi ko menene momyn twins zan miki in dai bai fi karfina ba.
Murmushi tayi tace"hmm dama yaya ina son ka dan kara min wasu kudi saboda business dinda nake son karawa .
Ya danyi shiru snn yace" naji zan baki amma da sharadi.
Tace"sharadi wane iri?
Yace"so nake ki kawo min business plan dinki na gani.domin tunda nake baki kudi har yanxu banga wani business da kk fara ba.
Murmushi tayi tace"aikuwa inada business plan a rubuce ma.domin so muke mu bude company buga turame kuma ni da kaina zan dinga zana designs masu kyau .
Yayi danyi murmushi snn yace"da kyau hakan yayi keda su waye zaku hada hannu?
Tace"nida Adda A'i da adda madiha .
Yace"nabila da sa,a fa?
Tace"hmm adda nabila komai na arziki idan an shigo da ita lalacewa yake.Adda sa,adatu kuma bata da lokacin wani business nasani.
Yace"amma ya kamata duk abinda zakuyi kusa ka nabila a ciki koda da shawarace zata taimaka muku kamata yayi ku hada kanku gabadaya ku tallafawa junanku.
Tabe baki tayi tace"hmm adda nabila fa bama sata a lissafin mutane ma domin komai ta taba lalacewa yake.Allah sarki dama dai adda Sukhaina nada rai ne ma ita kam bata da matsala gata wayayya.
Shiru yayi bai kuma yin magana ba sai ma tunanin maganganun nata da yakeyi.
Can tace"yaya se kuma maganar adda sadiya goggo tabi ta damu tana son ganin adda sadiya ta samu abinyi ta daina zaman banza.amma kuma sam na lura ita adda sadiyan bata wani damu da zaman banzan ba tunda ko damunta bayayi.ita babu abinda tasa a gaba sai dai ta dinga daukar maganganun mutane taje tana kaiwa goggo .
Nan da nan fuskarsa ta sauya cike da jin haushin sadiya yace"sai taci gaba da zama hakan ai.
Nafisa ta kwantar da murya cike da kirsa tace"haba yaya a taimaka mata dan Allah kaga fa har ta na gaya wa goggo wai baka sonta kana nuna mata banbanci tsakanita da adda Raihana da adda sa,a.
Tsaki yayi ya gyara kwanciyarsa bai kuma yin maganaba.murmushi tayi ta kashe wutan dakin ta kwanta itama taja bargo hade da fadin "don Allah yaya kayi hkr in dai akan maganar adda sadiya ce insha Allah bazan kuma kawo maka maganarta ba ka juyo dan Allah.
Bai sake kulata ba da haka har sukayi bacci.
Da safe farida tuni ta gama duk wani shirye shiryenta na tfy makaranta na lura sai fushi take tayi har yanxu.koda ta kawo min tea da maganina na kalleta nace"Farida wai menene yake damunki tun jiya kk ta fushi ?
Tace"babu komai mama kawai kaina ke mun ciwo .
Duk da nasan ba haka bane amma ban matsa mata ba nace"sannu Allah ya sawwaka yanxu kamin ki tafi kije kiyi breakfast se kizo ki sha pcm
Ta dan ja tsaki hade da fadin wnn nafisan don mugunta yau kosai tasaka akayi da kunu ...
Na katseta da fadin"kefa macece farida idan an dafa abinda ba kya so ba sai ki shiga kitchen ki dafa abinda ranki yake so ba.
Tace"kawai mama ki bar maganan nan wlh bata mun rai yakeyi.daddy zan gayawa domin ya fada mata duk ranar girkinta kamata yayi ta tambayi kowa abinda ransa keso a dafa masa kamar yadda kikeyi.ba wai kawai ta dinga kwaba abinda ranta yakeso ba.
Nace"ke dai kin fiye raki wlh ni har ga Allah banga laifin nafisa ba domin ta dafa abinda daddynku yafi sone don haka ki bar maganar nan ki dauko handbag dina ki kawo na baki kudi in kinje makaranta kici abinda ranki ke so shikenan.
Ta ce"inada kudi da daddy ya bani shekaran jiya.
Snn ta juya zata fita tace" don Allah mama ki kula da kanki se na dawo.
Nace"a dawo lfy.
Bayan ta fita khalil ma ya shigo ya gaisheni snn ya sallameni duk na bisu da kyakkyawar addua.
Inna kuwa tunda sukayi maganar sadiya da nafisa take ta zuba ido amma shiru ba abinda nafisa tace mata har ta gaji ta fara neman nafisa a waya amma sam layin nafisa yaki shiga hakama sadiya ta kirata shiru baya wucewa ta kalli innah tace"inna nifa na lura nafisan nan tana da wani mugun haline itama.
Inna tace "aa bana so karki fara aibatata don ke haka kk da son zagi da kushe mutane kina aibata su.karki ga laifinta salman ne baiga dama ba don haka se kiyi hkr na lallabashi a hankali randa ya ga dama ya baki .
Sadiya tace"haba innah ki duba fa duk yanuuwana sunci gaba sun barni.ace ina da dan uwa kamar ya salman a garin nan amma ko motar hawa ni banida ita har yanxu?
Inna tace"hmm hkrn dai zakici gaba dayi.
Haka sadiya ta koma gida da fushi ta kira adda A'i tana gaya mata adda A'i ta bata hkr snn tace insha Allahu zata san me zatayi akai.
Amma shiru da yin maganansu ya fi wata biyu yanxu.