← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 128

Sashe 70

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace " anan zan zauna sai dai daddynki yace zai sayi fili yayi min gini anan kano don nace bazan iya zaman yola ba.

Nace " gaskia kam mama ko don nima zamanki a kusa yanada mahimmanci snn banson ki koma yola kar aunty samira ta shiga matsala kinsan tana matukar kishin daddy.

Dariya mama tayi tace " hmmm tanada gaskia .to ya Lagos din ya jikinki?

Nace" Alhamdulillah na warke.

Muna cikin hira ya salman ya leko da Sallama yace " Goggo Amina daddy yace zai wuce masauki .

Mama ta kalleni snn ta ce " au na manta Rumaisa daddynki na gari muje ku gaisa.

Murmushi nayi a raina nace " shiyasa mama ta cancara kwalliya haka knn.

Ya salman tuni ya fita mama ta nufi wurin dressing mirror tana gyra dankwalinta ta kalleni nima ita nake kallo tace " ki tafi man ina zuwa.

Murmushi nayi har zan fita tace " au na manta ki kara yi masa Godiya ya biyawa inna da Maman sakina kujeran hajj.

Murmushin jin dadi nayi nace " kai gaskia na tayasu murna.

Ashe shiyasa yau inna ke mun fara,a haba nasan ruwa bata tsami banza.

Fita nayi na bar mama tana fesa turare.

Ina zuwa Palo na sami daddy da ya salman suna hira kamar wasu abokai na gaida daddy ya amsa da fara,a yace " mamana ya jikin ?

Nace " Alhamdulillah daddy naji labari mai dadi Allah ya sanya alheri.

Cike da fara,a yace " amin Mamana na gode

Anan na kara yi masa godiya hajj da ya biyawa su inna hadi da yi masa kyswawan addua.

Ya salman ma yaji dadi sosai kuma yayi wa daddy Godiya.

Mama ta fito ta samemu ya salman ya gaisheta snn yace inzo mu tafi gida.

Mukayi musu sallama .

Daga nan muka koma gida side din ya salim ikon Allah cikin ruma har ya girma .

Duk inda tayi binta nake da kallo ya salman kam zolayarta yake yana" ki dinga tfy a hankali fa kar ki wahalar min da baby naga yanda kk ta fizgar jikinki kamar ba mai juna biyu ba .

Dariya tayi tace " to sweety zan kula.

Ya Salim yace " ainima fadan da nake mata knn kullum .

Ya salman yace " daukanta zaka dinga yi ba wai ka barta tana wahala ba kai kuma.

Ya salim yace " tab mai daukan ruma yanzu ai sai yaci damara.

Dariya mukayi gabadayanmu ruma tace " kai honey.

Sai bayan isha muka koma side din mu 'yanmatan nan mun samesu a Palo suna kallon series sun gyare koina tsaf don haka sashin ya salman muka wuce mukayi wanka a tare snn muka shirya bacci don mun gaji.

Hauly ce🥰👍🏻
[9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡64

************Washe gari kuwa da daddy zai tafi muka tafi tare don ya Salman zai koma Lagos ran Sunday.

Na sami 'yan yola cikin koshin lfy sai hamdala .

Anan na fara samun special kulawa gunsu aunty samira kunsan bata wasa ta nan .

Ko abinci sakoni a gaba suke sai na cinye kamar wata karamar yarinya .

Koda yake na rame kam sosai gashi na dada haske sosai daddy har cewa yake kodai jinin ne bai isheni a kara ya samir yace mishi aa kawai abinci masu karin jini zanci ba sai an sake kara min wani jini ba tunda ga kuma magunguna na.

Abinka da 'yar gata satina daya na warke tass nayi jiki na dada kyau abina.

Yaya kuwa kusan kullum muna manne a waya sai dai in aiki ya masa yawa.

Yanzu ma shi nake kokarin kira don jiya yace mun ya kwana da ciwon kai ko hira mai kyau bamuyi ba .

Karfe 6:00 ne na safe na kira har sau biyu bai daga ba ana ukun ne ya daga ina shirin yin magana kawai naji muryar mace tace " hello ya shiga wanka fa.

Damm naji kirjina ya buga cikin dauriya nace " wacece ke?

Dariya tayi tace " khabirat ce da wa kk tunani?

Hawayene ya cika idona fal na sake duban agogo snn nace " ina salman din?

A tsiwace tace min " bakiji nace miki ya shiga wanka bane?

Da sauri nace" OK OK shikenan.

Na katse kiran jifa nayi da wayar bansan ko a ina ta fada ba na kifa kaina a fillow na kama rusar kuka kamar an aiko min da sakon mutuwa.

Haka aunty Samira tazo ta riskeni anan ta shiga tambayata me ya faru.

Ko kadan ban boye mata ba duk na kwashe na fada mata don bazan iya kumsan wnn bakinciki a raina ni kadai ba.

Itama hankalinta a tashe tace" kaji matsalar ai zaman bariki baiyi ba snn cikin kabilu se a hankali Ihsan ni dai shawara daya zan baki kisan duk hanyan da zakibi ku dawo kano zakifi samun kwanciyar hankali .

Ni dai ba abinda na Sani sai kuka aunty samira tace " ta iya yuwuwa kuma makircine irin nata don ta hadaki da mijinki .

Haka ta dinga rarrashina hade da bani shawarwari har saida taga na dan sami nitsuwa.

Har kusan azahar ya salman ya kirani kamar bazan daga ba na dai daure na daga .

Shi ya fara fadin baby yau banji muryarki ba sorry wlh bacci nake tunda safe bsnjima da tashi ba.

Nace" yaya ko dai zazzabin ne ?

Yace " shine fa kamar da wasa wlh .
Nace " wayyo to Allah ya baka lfy ai na kira amma baka dauka ba.

Yace " ikon Allah aiko missed calls kuma ban gani ba how comes?

Na tabe baki hade da fadin " Allahu alamu .yaushe zaka zone kafa ce min zaka zo ka daukeni.

Ya danyi shiru snn yace "zanzo baby ayyuka ne suka min yawa da ba don rashin lfyn ba da ina Maiduguri ma cikin week in nan.

Nace " to yanzu ba rana knn?

Yace "eh gaskia sai na sami natsuwa tukun na.

Hawayene ya zubo min na rasa me zan kuma ce masa kawai na kashe wayar gabadaya .

Kwana biyu wayata a rufe aunty samirace tasaka na bude abin mamaki ko text din ya salman ban samu ba.

Da daddare ne wata number ta kirani na dauka macece muka gaisa tace " kin ganeni kuwa ?

Nace " kai aa

Tace " madame Fatima ce daga army barrack neighbor dinku .

Nace " o Allah sarki matar oga bello ko ?

Tace " eh ya kk ? Ya jikin kuma?

Nace " da sauki wlh.

Tace " to Allah ya kara sauki .wai yaushe zaki dawone amarya?

Nace " babu rana gaskia akwai wata matsalane madam?

Tace" eh to gaskia akwai matsala domin ina yawan ganin khabirat tare da maigidanki kuma har tana zuwa gidanku da daddare abinda kuma bai taba faruwa ba sai dis time shine nayi deciding na kiraki na fada miki domin ki bar komai ki dawo inaga zaifi domin kinga ke bakuwace a barrack dinnan bakisan komai ba mazajenmu na yanzun nan fa ba irin yadda kk tunani bane don haka karki sake ki sake nitsa da mijinki domin akwai matsala so ki dawo kawai.

Tunda ta fara magana nake kuka sheshshekar kukana dataji ne yasa tace" no don't worry ba wani abu bane normal ne daddayane a zamanin da muke yanzu ki sami miji kamili .kinma ci sa,a don suleyman baida neman mata shikam bai kuma shan komai na maye and ba ruwansa da shiga harkar mutane kowa ya shaidesa amma wnn karon an sami akasi domin wnn khabirat taja ra,ayinsa sosai shiyasa na yi maza na kiraki gara ki dawo kar abin yayi muni gara kizo ki dauki mataki.

Cikin muryar kuka nace" to ni madam wace mataki nasan zan dauka anan ni me na sani ? Kawai ni inaga rabuwa zamuyi......

Da sauri ta katseni da fadin " kash ! Da wuri haka ? Hmm Amarya ke yarinyace har yanzu bakisan komai ba .mu munsha gwagwarmaya da karuwai har ya zame mana jiki don haka kema dole ne ki cire duk wata tsoro ki tashi tsaye ki daura damarar yakar ko wace ' yar iska idan tazo kusa da mijinki.amarya zaman bariki ya wuce tunaninki fa .don ma yanzu Alhamdulillah mun dan sami 'yanci ba kamar da ba namiji yasa hannu yayi ta jibgar matarsa akan karuwa ko in yaje yasha giyarsa ya dawo.amma yanzu da zaran mijinki ya tabaki kina da right ki kaishi ga manyansa su hukuntashi to kinga mun sami sauki .snn mu matan barrack mun hada kai munada kumgiya tamu ta matan sojoji da muke meeting sau 2 a month in kinaso ki tamvayi mijinki ki shigo cikinmu na tabbata zaki zama jaruma kuma duk tsoron nan zaki bari.wnn kuka da kk yi duk zaki daina tunda nima na bari.don haka ki dawo kawai.

Tsabar kukan da na ci har kaina ya fara ciwo don haka nace " to madam zanyi yadda kk ce din Allah ya saka da alheri na gode sosai.

Anan mukayi sallama tashi nayi na shiga kai komo a dakin ina tunanin mafita .

Gaskia naga tashin hankali yadda nake ganin rana haka nake ganin dare hankalina gabadaya a Lagos yake gani nake kamar kullum ya salman na manne da waccan 'yar iskar.

Don haka ya samir nayiwa magana nace " ni gaskia ina son komawa ya salman kuma yace ba yanzu ba.

Don haka ya samir ya kirashi sukayi maganar yace masa ga ni nan na matsa zan koma Lagos ba yanda ya iya da ransa yace to kawai in dawo din amma shi bazai samu zuwa ba don ayyuka sun mishi yawa.
Ya samir yace ba komai.

Don haka ya gayawa daddy daddy yace ba damuwa sai in tafi tunda jirgine .

Nan na fara shirye shiryen tfy wnn karon da kaina nace aunrty samira ta hadomin dukkan magungunan nan in tafi dasu

Ranar Saturday daddy ya kira ya salman ya sanar dani ina tafe.

Haka nayi sallama da kowa ya samir ya kaini airport .
Chapter 70 · 0% Book details