← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 128

Sashe 89

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni dai ban kwana a asibityn ba muka dawo kuma na warware tass sadiya kuwa tuni ta debi kayanta ta koma gida tun ya salman bai dawo ba don tasan in har ya dawo ya sameta zata yabawa aya zakinta.

Tana xuwa gida ta fadawa innah komai innah ma ta tsorata sosai ta shiga yiwa sadiya fada tana cewa wlh duk randa kk bari kk hadu da salman a gidan nan karki nuna kin sanni wai ke baki da hankaline ?

Sadiya dai ta rasa ina zata sa ranta taji dadi a ranar.

Salmah kam tana can gidansu sai magani ake tayi hade da rukiyya wasa gaske sai da ta share two weeks a gida snn ta warke ta dawo .

Sai lokacin hankalin ya salman ya kwanta don haka ya je gida ya sami sadiya yana tambayarta labarin hayaki .

Kame kame ta soma yi da farko sai da ya wanketa da kyawawan mari guda biyu masu kyau snn yace"zaki gaya min ko sai na kakkaryaki?

Anan tace"yaya wlh turaren wutane aka kawowa salmah daga maiduguri......

Ganin ya fara kwance belt yasa sadiya ta tashi da sauri tayi bayan innah tana "wayyo innah yaya zai kasheni da duka.

Inna ta kalli ya salman hade da fadin"yanzu kai ko kunya bakaji ba a gabana kazo kana tuhumar 'yar uwarka akan laifinda bata aikata ba.......

Sosai maganar inna ta kara fusatar dashi yace"haba inna har yaushe zaki daina goyan bayan wnn shaidaniyar..

Inna tace"au 'yar uwar taka ce shaidaniya ? To bari kaji shaidanu suna can gidanka ka tara su.don haka ka fita ka bani guri tun kamin raina ya baci don zan mugun bata maka.

Kai tsaye yace"zan fita innah amma daga yau ki gargadi sadiya bani ba ita kar ta kara zuwan min gida idan kuma ta kuskura na kara ganin kafarta a gidana duk abinda na mata karkiga laifina na fada muku kuma zan gayawa abba ma....

Inna tace"kai dai kaji kunya salman akan wasu banzaye kake ikirarin ba bu kai ba 'ya uwarka .

Yana fita ta kalli sadiya tace "ba kinga abinda kk je kika janyo ma kanki dan tsabar rashin hankali to ai shikenan se ki zauna anan din gaki ga abbanku tunda shima har yau yana cike dake bama ke kadai ba ni kaina bai barni ba.

Haka kuwa akayi abba na dawowa ya rufan musu daga innah har sadiya bai raga musu ba don har cewa sadiya yayi wlh ba don ina tsoron karki fi haka lalacewa dana koreki daga gidana don matsalarki ta isheni wlh duk cikin ku ba mara ji irinki addua nake miki dare da rana sadiya Allah ya shiryeki.

Ya kalli inna yace "ke kuma shatu ke kk daure mata gindi tana tana abinda ranta yakeso to wlh ki kiyayeni.daga yau ina dada ja muku kunne ku fita daga tsabgar gidan salman don suna cikin zaman lfynsu sadiya ta kashe aurenta taje ta tare a gidan don ta rusa musu zamansu don haka daga yau kar ta kara zuwa gidan salman banaso !

To tunda akayi wnn case din aka gama sadiya bata kara zuwan mana gida ba don haka muna zaune lfy na ciki na ciki.competition kawai mukeyi wurin kwalliya da girki da kuma kyatatawa oga .

Sadiya kuwa duk yadda taso ta kara jan salmah a jiki abin ya gagara salmah taki bata hadin kai kamar da don haka sai ta koma kullawa salmah munafurci a gun innah tana cewa "innah yau da gobe sai Allah auren ya salman da salmah kinga har ya cika shekara daya cif yanzu.

Inna ta ce"hmm haka fa nayi lissafi jiya jiyan nan kamar kin shiga raina.amma shiru itama salman ba labarin ciki.

An sosawa sadiya inda yake mata kaikayi ta gyara zama tace"innah salmah fa ba matar da zata haihu bane wnn matsalar aljanun nata bazasu taba barinta ta haihu ba domin tunda tazo gidan ya salman ko 'yawu bata taba tsartsarwa ba har gara rumaisah tayi bari sau uku .

Inna tace"ai kuwa kina da gaskia snn ma ni ba wnn ba tunda kuka samu matsalar can ta daina min waya da kuwa tana kirana akai akai mu gaisa to me yasa?

Sadiya ta tabe baki tace hmm inna dama munafurcine kawai fa da neman gindin zama yanxu kuwa kinga tunda ta sami kan mijinta kinga ta daina kulaki .

Inna tace"lallai kam munafurcine na yarda.amma babu komai da ni suke zancen.

Sadiya tace"hmm ai tunda kikaga nima ta hadani da yaya har yana cewa babu ni babu shi kinsan ba karamar munafuka bace innah kinaga har yau yaya ko gaisuwata baya amsawa ni narasa ma da wanne zanji innaah ga matsalar jafar ya hanani inje inga yarana ya hana suzo in gansu abba kuma ya ki ya dauki mataki akai.

Inna tace "karki damu sadiya ki kwantar da hankalinki duk zanyi maganinsu.amma kamin nan salman zaizo ya sameni a gidan nan ta kansa zan fara domin ya isheni takaici da bakin ciki da yake cusa min .

Sadiya tace"ai sun gama dashi kinga ma ko zuwa ba ya son yi kamar da.

Inna tace dauko wayata ki masa flashing.

A lokacinda innah ta kira ya salman muna tare ranar nice da girki da safene ina kwance kan gado a dakinsa duk na rasa me yake min dadi .

Tunda suka fara wayar hankalina na kanshi a zuciyata nace hmm yau kuma innah waya da sassafe Allah sa ba laifi mukayi ba.

Yana gama wayar ya turata aljihu ya karaso inda nake ya zauna bakin gadon ya taba wuyana yace " baby kwana nan duk na lura kamar baki jin dadi sosai me yake damunki?

Nace"wlh yaya ba komai ke mun ciwo ba kawai dai kasala nike ji bana son yin komai wlh.

Dagoni yayi daga kifuwar da nayi ya juyo dani ya kwantar kan kafarsa ya daga rigana ya shafa cikina yace"ko dai akwai ajiyata ne a wnn shafaffen cikin?

Shiru nayi yace" yace nasan dai kinyi mensis last month dis month kuma in har baki yi ba nan da five days zamuje asibity a duba ko Allah ya amshi adduar mu da muka dade munayi .

Jikina ne ya kara mutuwa tausayin ya salman ya kamani sosai domin indai ba tsananin rabo ba yanzu a inda nake kwance ma ina jin sign din period dina zaizo don bayana da marata sai ciwo yake min bana son fada masa ne kar ya daga hankalinsa.

Bayan ya taso daga aiki gidansu yaje don amsa kiran innah ba zato ba sammani inna ta bijiro masa da batun wai ya sake aure ya auri madiha.

Maganar ya matukar girgiza shi cike da mamaki yace "innah me ya faru kuma?

Tace"kai har yanzu baka san mai ya faru ba tsabar sun gama da kai ba kama damu da rashin haihuwar nan ba duk sa,oinka sai haihuwa suketayi gwanin ban sha,awa amma banda kai.

Yace"Inna haihuwar nan fa daga Allah ne ba wai daga rumaisah ko salmah bane don haka kawai addua zakici gaba da yi mana sai kiga inda rabo za,a dace.......

Ta katseshi da fadin ya isa dan Allah ko yaushe aka taboka sai ka nuna kafi kowa sanin Allah to bari kaji aurene sai ka kara kuma madiha zaka aura .

Yace" haba inna ni fa nace miki madiha ba matar aurena bace kinsan halinta banda yawon iskanci a lagos ba abinda ta iya.....

Inna tace"eh ai dole kace haka idan yawon iskanci ne wani iri ne rumaisa batsyi ba bayan karuwanci ina har da shaye shaye ma amma ba gashi da ka aureta ta shiryu ba kamar ba ita ba to itama madihar idan ka aureta zata nitsu.

Tashi yayi ransa a bace yace"ni gaskia innah abar ma batun madiha bana bukatar mata uku biyun ya isheni haka kawai ki hkr kici gaba da yi mana addua.

Yana gama fadin haka ya fice da sauri ransa a cunkushe.

Ya dawo a lokacin na gama komai ina zaune a palon kasa muna hira a waya da ruma tana bani labarin tana daukeda ciki tsawon wata uku gaskia na tayata murna ba kadan ba don suma har sun fara damuwa tundaga kan munir shiru yau ga munir shekara shidda.

Shigowar ya salman ya katse mana hira mukayi sallama na tashi da sauri na karasa gabanshi fuska sake nace"yaya ka dawo......

Da kai kawai ya amsa min ya wuce side dinshi jikina a mace na bishi a baya.

Ranar ko abinci ya kasa ci na tambayeshi amma bai gaya min ba don haka ban matsa mishi ba.sai dai duk bamuyi baccin kirki ba ranar .

Da asuba kuwa bayan idar da sallah na shiga kitchen na shirya mana breakfast kamin na gama duk naji bacci ya cika min ido don haka a daddafe na shirya dining na bar sa,a da gyaran kitchen na koma part din ya salman na kwanta na barshi yana ta faman waya da abokan aikinsu.

Bacci ne ya daukeni har ya gama abinda yake ya shirya cikin kakinsa yazo ya dan tattabani yace"baby tashi ni zan tafi muje muyi break fast

Mika nayi sosai hade da salati idona a lumshe nace" yaya ni bacci nakeji sosai kuma na koshi ma.

Kallona ya keyi snn ya danyi murmushi yace"to shikenan gimbiya asha bacci lfy.sai na dawo.

A hankali nace a dawo lfy .

Naja bargo na kara rufe kaina naci gaba da baccina.

Ban tashi ba har shadaya nayi wanka snn na fita na kulle sashin ya salman na wuce nawa sashin na na zauna na bata lokaci wurin tsarawa kaina kwalliya.

Ina daura dankwalina sa,a ta turo kofa hade da sallama na amsa ina murmushi nace" yau ba lectures ne?

Tace"yanzu ma nakeso nazo na tafi .aunty su innah sunzo fa yanxu suna zaune a palon kasa da sadiya.innah tace kije.

Nan da nan fara,ar da ke fuskata ta gushe.

Kamar bazanje ba na dai daure na fita ina ta addua a zuciyata ina ganin yanayin fuskokinsu nasan akwai matsala.

Nayi musu sannu da zuwa basu amsa ba sadiya sai hararata takeyi .
Chapter 89 · 0% Book details