← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 128

Sashe 64

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta dago a hankali ta kalleni snn tace " yau satinki daya knn kina kwance........

Bata boyemin komai ba hankalina ya tashi matuka kuka na dinga yi ina" mama me nayiwa inna ta min haka? Ni yaushe zan daina fuskantar matsala a rayuwa ta.yaushe su inna zasu barni na huta?

Kuka sosai na dinga yi mama bata ce min komai ba sai da nayi mai isana snn tace" shikenan ya isa haka ki godewa Allah ma tunda duk abubuwa da suke miki Allah yana bamu ikon gane makircinsu Alhamdulillah ni dai na barwa Allah komai kema kuma sakacinki ne ya jawo miki da ace kina riko da addininki yadda ya kamata da Allah bazai basu ikon cin nasara akan ki ba.amma ba komai Allah ya saka miki.

Ni dai dafe kai kawai nayi hawaye na bin kumatuna.

Mama kuwa a cikin daran ta kira ya salman inajinta tana ce masa " salman rumaisa ta tashi don Allah yau kam ka samu kayi bacci.

Yace " Alhamdulillah Goggo gani nan zuwa ki buden get .

Tace "aa salman kaidai sai da safe na fada maka ne don ka samu yau dai kayi bacci.

Ba don ransa naso ba ya amince a in da yaci gaba da sallolinsa.

Daddy ma a lokacin yana kan sallaya mama ta kirashi ta sanar da shi daganan fa duk sukaci gaba da nafila suna godewa Allah .

Ana idar da sallar asuba yaya ya shigo a lokacin na idar da sallah ina kan praymat mama kuma tana kitchen .

Ina shafa addua na juya mukayi ido biyu tattausan murmushi na sakar mishi .

Ta shi nayi na nufi inda yake da sauri ya kamoni ya rumgumeni kamar zai maidani cikinsa yace " masha Allah babyna kin sami lfy Allah na gode maka.

Muka zauna bakin gado na dago na kalli fuskarshi nace " yaya me yasa ka rame haka.

Ya dan shafa wuyansa yace " baby dole kawai na rame halunda kk shiga ya tayar min da hankali sosai .

Nace " to yanzu kaga na warke yaya zaka dinga cin abinci akai akai banson ganinka cikin damuwa.

Murmushi yayi yace " nagode babyna .

A hankali na kamo hannunsa na dora kan marata nace " yaya yau baka taba kaji lfyn babynmu ba.

Na karasa fada ina murmushi hade da kallon fuskarsa amma sai naga yanayinsa ya sauya bai dai ce komi ba sai marata da yake shafawa.

Nace " yaya lfy?

Sauke numfashi yayi yace " baby kiyi hkr amma babu babynmu a jikinki tun randa kk shiga wancan yanayin doctor James ya tabbatar min da hakan ......

Nan da nan hankalina ya tashi na fara hawaye tausayin ya salman ya kamani irin yanda ya kwallafa ransa a kan cikin nan.

Ya shiga share min hawaye yace " lfyrki ta fi min komai rumaisa don Allah ki daina sakawa kanki damuwa Allah zai sake bamu wani kinji?

Haka ya dinga lallabani har mama ta shigo hannunta rike da tire .bamusan ma ta shigo ba.

Dan gyaran murya tayi da sauri na tashi daga jikin ya salman shima ya cire hannunsa da na dora kan marana.

Cikin jin kunya na gyara zaman rigana.

Mama ta kalleshi tace" Salman har ka shigo.

Ya amsa snn ya gaisheta ta amsa snn tace " to Ku sauka kuci abinci duk kun rame wlh .

Ya salman yace " mun gode Goggo.

Daga nan fita tayi ta barmu .

A baki ya dinga bani har saida na koshi dam nayi gyasa yace " Alhamdulillah.

Nace " saura kai .

Nan na fara bashi shima saida ya koshi snn ya kalli time yace " bari inje in shirya tfyn aiki baby Allah ya kara lfy kuma kici abinci sosai .

Kai na daga mishi hade da fadin " to yaya sai ka dawo Allah ya kiyaye hanya.

Yana fita gidansu ya shiga ya gaida Abba da Maman sakina snn ya tafi dakin inna.

Bayan sun gaisa tace" ya jikin rumaisan ?

Murmushi yayi yace " inna rumaisa ta warke.sai mu godewa Allah.

Ba karamin girgizata maganar yayi ba tace " kana nufin ta warke har tana magana?

Yace" kwarai kuwa inna ai yanzu ma daga gunta nake zaki iya zuwa ki dubata.

Kan inna yayi wani irin sarawa ba shiri ta dafa kan hade da fadin " wash.

Ya salman yace " subhanallah lfy inna ?

Cikin dauriya tace " ba komai kaina ne yake mun ciwo duk kwanan nan.

Yace " sannu inna Allah ya baki lfy bari in dawo aiki zan gwada miki bp dinki amma kan nan kisha maganinki kuma Dan Allah ki rage yawan damuwa.

Cikin kosawa tace " naji jeka Allah ya kiaye.

Daga nan fita yayi yaje ya shirya ya tafi aiki.

A ranar daddy na yazo da su ya awwal munyi hira sosai daddy ya dinga godewa Allah ya hadani da su Haj rumaisa muka gaisa.

Zuwa yanzu na lura mama da daddy an fara dasawa hira suke ta yi cikin fahimtar juna dadi naji a raina sosai.

A ranar suka tafi acikin kwanakin anyi ta zuwa duba jikina .

Inna kuwa tun ranar ciwon kai yaki sarara mata jininta ya mugun hawa har aka cire mata sammani ya salman ya sake birkicewa Allah sarki yayana gaskia ba don jarumtarsa ba matsalolin rayuwa ya isa ya kwantar dashi shima.

Sadiya hankali ya tashi sosai adda ai ma tazo gani suke kamar mamace ta yiwa inna asiri kunsan abinda mutum keyi sai yaga kamar kowa ma shi yakeyi.

Inna taji jiki sosai jini kuwa yaki ya zama normal ta ramene na fitan hankali ciwon kan nata in ya tashi kamar zatai hauka sai an rirriketa.

Wlh koni sai da na tausaya mata amma nafi tausayin yayana da kyar nake samu ya danci abinci.

Hauly ce🥰👍🏻
[9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~`

*PAGE* ➡59

*********** Inna ciwo kamar wasa har ya kaita sati biyu a asibity saida aka kaita Abuja duk Wanda yasan inna a da yanzu in ya ganta sai ya zubar mata da hawaye tasha wahala sosai kamin ta fara samun sauki.

Ni dai zuwa yanzu har na maida Jikina na koma gidana babu abinda yake damuna sai rashin kwanciyar hankalin ya salman .

Satin inna biyu a Abuja aka sallamota ta sami sauki sosai don ban Wanda bai cire mata tsammani ba .

Don haka inna tayi likis yanzu ko magana bata so banda yawan istighfari ba abinda take dama ance jiki magayi.

Yayinda Adda A'i da Sadiya kuwa wutar fansa ke dada ruruwa a zuciyatsu gani suke kamar mamace tayiwa inna wnn aikin .

Inna dai ce musu tayi " bata yarda su maida martani ba .

Sadiya tace " wlh inna ko zan tafi tsirara bazan bar rumaisa taji dadi a gidan ya salman ba .Inna kina ganin yadda suka bi suka maida yaya wani iri sai yanda suka so sukeyi dashi yaya da kk Sani baya dariya yanzu wlh in kin ganshi da rumaisa sai kin rike baki .

Hawaye ne ya zubowa inna tace" ni dai banida abinda zancewa Amina sai dai Allah ya isa tunda suka maida min da kamar wani bawansu .komai ya taso indai akan amina da rumaisa ne jikinsa na rawa.

Adda A'i takaici ne yabi ya rufeta ta kalli inna tace " ai Goggo da kk cewa a rabu da su so kk su kasheki ? Goggo wlh malamina ya gaya min magana data girgizani don ce mun yayi salman ne da kansa ya tono wancan asirin kuma kuma Goggo Amina ce tasa shi ya tono suka kona.

Inna da Sadiya suka zaro ido cike da tsoro inna tace " to waya fada mata an binne abu a gidan ?

Sadiya tace " haba biri yayi kama da mutum nayi mamakin samun lfy rumaisa lokaci guda.

Adda A'i tace " to yanzu Goggo dabara ya rage naki sai ki tashi tsaye akansu ko kuma watarana idan sun gaji dake su kasheki gabadaya.

Inna ta dafe kirji ido waje tace " na shiga uku na ni shatu .

Nan da nan taji kanta ya fara ciwo .

Raihana da ke kwance tun dazu tana jinsu sai yanzu ta tashi hade da fadin " adda don Allah Ku bar sakawa inna damuwa ko bakuji abinda likitoci suka fada bane ? Meye amfanin wnn maganar da kk yi.ai kune kk shirin kasheta da wayan nan maganganun naku .ba komai ke damun inna ba sai ciwon zuciya da hawan jin ba wani asiri don haka addua zamu mata Allah ya bata lfy ba wai Ku zauna kuna wasu maganganu marasa tushe ba.

Sadiya ta cika fam har wuya harara ta watsawa raihana hade da fadin " ke Dan Allah wa ya sakoki cikin wnn maganar?

Adda A'i tace " hmm ni tsoro nikeji kar a hada baki da raihana a cutar damu watarana don itama an gama da ita tuni.

Inna tace" da kuwa sai na tsine mata wlh.

Raihana ta mike da sauri tace " don Allah inna ki daina ambatan zaki tsine mun kiyi hkr bazan kuma sa bakina cikin maganarku ba Allah ya huci zuciyarki.

Ta dauki Jakarta ta kallesu tace " ni na tafi.

Sadiya tace " umma ta gaida assha.

Inna kam da harara ta bita har ta fita.

Bayan fitarta sa,a ta shigo da warmers din abinci daga gidana ta ajiye snn tace wa inna " Goggo aunty rumaisa tana gaidaki .

Inna ta zubawa sa,adatu ido snn tace " banso gaisuwarta kuma ki dauki abincin nan maza ki maida mata karta kuma turo min tunda kasheni suke shirin yi da uwarta.

Kallon ta sa,a ta tsaya yi yayinda adda ai ta buga mata tsawa tace " ko bakiji me aka ce maki bane inci ubanki!

Sadiya tace " anya wnn yarinyan itama basu gama da ita ba ? Nifa na daina yarda da sa,an nan hmm.

Adda A'i tace "lallai kuwa dana maida ta kauye taci gaba da talle inga ta yanda zarayi bokon har ta zama likitan.
Chapter 64 · 0% Book details