← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 128

Sashe 84

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya salim ne ya shigo ashe yana jina.

Na dan turo baki nace"haba yaya dan hutun nan da good boy yazo shine dubi har ya rame.

Murmushi yayi yace" saboda bai cin tuwo ne kinsan mu bama cin tuwo saboda nauyi munfison abinci marasa nauyi ku kuma gidanku tuwo kukeci so ya saba da tuwo nan kuma babu shiyasa ya rame.

Tabe baki nayi nace "turawa ba.to nidai gaskia zan tafi dashi bazan barshi ya karasa satin ba tunda na lura ya takuraku ku ba kwason yara .

Yace"inji wa ? Don Allah karkije ki hadani da salman yazo ya kama min bala,i dama yana cike dani kwanan nan.

Na kwantar da murya nace"to don Allah yaya salim ku daina family planning din ya isa ka duba fa good boy yana neman 5 yrs yanzu.

Yace" ke fa tuntuni bamayi dama inplan ne aka saka mata kuma mun cire tun last year rabon ne baizo ba don haka in kinje hajj muma kisa mu a addua.

Daga nan yace "in kun gama shiryawa kizo mu wuce oganki duk sai damuna yake a waya wai bayaso ki kara kwana Abuja.

Yana gama fadin hakan yafita na kalli ruma nace" kingani ko Allah ya baku haihuwa kun kama kuna wani family planing yanzu gashi tunda kk bari shiru .

Jikinta a mace tace" ke dai bari ihsan duk na shiga damuwa wlh gani nake shima kamar za,a zuga shi ya kara auren.

Nace"ba wanda zai zugashi ku dai dage da addua kawai.

Daga nan ta karasa parking kayan munir ta rakamu mota daga nan tace " to ihasan Allah ya kaddara saduwar alkhairi ki mana addua baki daya.

Nace"insha Allah!

Daga nan muka kamo hanya ya salman sai damuna yake da kira na rasa me zanje in masa a gidan.

Koda muka shiga kano ma gidan mama muka wuce don bana son munir ya koma gidanmu har sai an gama ribibin biki don gudun kar su sadiya suyita hantararsa nasan halinta ba son yaran mutane take ba kamar ba uwa ba.

Bayan mun huta mama ta ce muci abinci ta gama shirya dining don haka mukaci abinci ya salim yace"mu tafi ba oganki ya matsa min.

Na dan yamutsa fuska nace"don Allah ya salim ka rabubdashi in ya matsu yazo ya sameni anan ni bana komawa gida yanzu sai da daddare bana son fitinarsu adda A'i.

Ya salim yace"yaushe sukazo?

Nace"tabdi ai tuni sun jima anan don tsabar zumudi kuma don wulakanci su rasa inda zasu zauna sai gidana.

Ya salim yace"ai laifin salman ne da ya barsu a tsohon gidanmu ai part dinku na da ai zai ishesu duka.

Dariya nayi nace"hmm wlh don baka je gida kaga uban gayyan da inna tayi bane ni wlh na dauka duk yan uwanta na camaroo sunzo don gabdaya sun cika part din mama na da snn sun cika gidanmu da kk magana.section din kawu ma ba don momy zasu zo bikin ba da an bude musu .

Shima dariya yayi yace"da kyau ashe bikin zaiyi arnashi .

Nace'a sosai ma Allah dai ya tabbatar da alkhairi.

Yace"amin ke kuma saiki kara hkr tunda kin fahimcesu wani abi duk sunayi ne don su kuntata maki.

Nace"wlh babu komai yaya inda sabo ai na saba yanzu.

Da haka yayi mana sallama ya tafi mama kuwa tana can da su Amira da khalil ga munir ma don haka ta biye musu suna ta mata shirme.

Na samesu a dakin nace"mama ya salim yace a sallameki ya wuce sai ko gobe zaizo.

Tace"to ke me ya hana ki bish?

Nace"ya salman nake jira kamin nan zan dan kwanta na huta don Allah kar amira suzo su dameni.

Tace "to munji uwar son hutu.

Dariya nayi snn nace"aunty rukaiya wai tayi missing din yaranta su koma don Allah.

Mama tace"hmm ai nima fitinarsu ta isheni daddynku yace in yazo daurin auren nan zai koma dasu ai karta damu.

Tabe baki nayi nace"wai harda su daddy a zuwa daurin auren fisabilillahi?

Mama ta watso min harara tace"to ya son ranki? Ko shima din so kk ya tayaki kishi?

Shiru nayi na sshafawa kaina lfy na wuce dakina wanka nayi na dan shirya jikina nasha maganina snn na kara powern Ac na haye gado na kwanta nan da nan bacci yayi awon gaba dani

A cikin baccin na dinga jin kamar ana shashsha fani da kyar na iya bude idona na kalleshi murmushi ya sakar min .

Limshe idona nayi na dada shigewa jikinshi nace"yaya yaushe kazo?

Yace"bai jima ba.

Ya cigaba da shashshafani snn yace "sai jiranki nake tun dazu ashe ke kina nan kinata baccinki.

Nace "wlh yaya na gaji sosai ne shiyasa na sauka gidan mama don in huta kadan.

Yace"to yanzu tashi zakiyi ki dauki hijabinki mu tafi gida akwai important issue da nike so muyi discussing......

Na katse shi da fadin" anan ne zamufi samun freedom mu tattauna ai yaya ko ka manta su adda A'i suna gida baza su taba bari ni da kai mu kebe ba?

Yace"sun isa su hanamu kebewa?

Nace"to ai gani nayi motsi kadan sai suyita kiranka a waya in muna tare duk da ma na amince za,ayi auren.

Na karasa fada ina tura baki yace"ki rabu dasu tashi mu tafi don Allah baby na matsu fa...

Nace"kai yaya ni dai ban yarda wani tattaunawa zamuyi kawai dai ka ce....

Sa hannunsa yayi a baki yace"keep quite ! Tashi kawai mu tafi .

Na tashi na dauki jakata da hijabina muka je muka sallami mama daga nan muka tafi gida.

A main palour muka same adda A'i da sadiya da wasu sun baje da yaransu suna abinda sukaga dama.

Tunda muka shigo suke ta kallonmu gashi sunga ya salman na rikeda jakata.

Ganin basuda niyyar yin magana yasani fadin"sannunku da hutawa.

Na zauna muka fara gaisawa ya salman tuni ya haura sama bai ko kulasu ba.

Adda A'i tace "rumaisa yanzu saura kwana hudune daurin auren nan amma ke na lura ba wasu shirye shirye da kk yi ko 'yanuwanki da kawayenki ma baki gayyacesu ba me yasa?

Murmushi nayi nace Adda ai ni bana nan yana iya kasancewa kafin a daura aure ma na wuce saudi yau nefa kadai nakeda lokaci fa to in nayi gayyan da wa zasu zauna ?

Sadiya tace "hmmm ke dai fadi gaskia ko dai kishine? Ai ba haka akeyi ba dannewa zakiyi .

Nace"hmm ba damuwa ke dai in ma shi din ne.dama ni bukatata inga hankalinku ya kwanta tunda na lura yanzu hankalin naku ya kwanta ai shikenan Allah ya tabbatarda alkhairi.

Amin suka fada yayinda na tashi na wuce can side din ya salman na tafi ina shiga dakinsa naji an rumgumoni ta baya nace"wayyo yaya ka tsorata ni.

Yace" kefa na lura bakisan halinda na shiga bane a dan kwanakin nan da ba kya nan shiyasa kk ta ja min aji.

Nace"kai fa yaya ango ne amarya za,a kawo maka dal a leda.

Dada matseni yayi a jikinsa yace"inji waye ?ba dal a leda bace kece dal a leda shiyasa ban gsjia dake.

Lumshe ido nayi inajin yadda yake ta faman yamutsani nace"kai yaya amarya fa amaryace dadinta daban ne.

Bai kuma yin magana ba kawai ya shiga kissing dina ko ta ina yana sauke numfashi da kyar ya fara magana cikin kasalallliyar murya"I'm going to miss you baby don Allah na yau daya ki barni na more.

Yayi cak dani zuwa kan gado ya shiga juyani son ransa nima na biye masa muka shiga faranta ma juna rai har mun so mu makara da sallar magrib da kyar ya daure ya sakeni ya wuce toilet nikam ina kwance jikina duk ya gama mutuwa.

Wayarsa na gani yana haske kasancewar yasashi a silent ina duvawa naga sunan *SALMAH*!

har naji kirjina ya buga don haka na mayar na ajiye yana fita ma ban gaya masa ba har yasa jallabiyarsa a gurguje ya tafi masallaci ya bar wayan.

Bayan na idar da sallar magriba na fita palo har lokacin su sadiya na nan ko sun yi sallahne oho nidai kitchen na wuce ina tunanin me zan dafa simple da zamuci kawai na yanke shawarar dafa macaroni da dankali haka kuwa nayi nasa hanta na hada kayan kamshi nan da nan kamshi ya gauraye koina sai ga sadiya ta shigo tana cewa"uwar gida me kk dafa mana ?kamar kuwa kinsan yunwa mukeji don yau ba,a kawo mana abinci daga gida sun san kin dawo dama da ba kyanan innah take turo mana wasu lokutan adda A'i ta tura driver dinta ysje ya siyo mana gasassun kaji muci da drinks.

Kamar bazanyi magana ba na daga baya nace"hmm kema a gidan nan kk kwana knn?

Tace"eh kinsan mune kirjin biki.

Nace"gaskia kam Allah ya taimaka .

Tace "amin ta fita" na bita da kallon mamaki lallai mijin sadiya ya shiga hannu sosai a yanda nasan jafar da wlh bazai taba barin sadiya tayi duk abinda taga dama ba Allah dai ya kyauta .

Na gama gikina knn na dauko fruit na fara yankawa sa,adatu ta shigo murmushi nayi nace"sai yanzu?

Tace"hmm bari kawai aunty tailor dinnan yana wainamu nida zainab yau kusan yini mukayi muna zaune a shago da kyar ya hada mana kayan da zamusa jibi .

Murmushi nayi nace"au haka fa jibine sisters daya ko?

Tace"A wlh aunty naso kina nan kiga rawar su adda A'i kici dariya har cikinki yy ciwo wlh adda A'i bata iya rawa ba saboda tsabar kiba amma ta dage sai anyi har da dinner ma.

Dariya nayi nace"wlh bakida mutunci sa,a to kidaiyi a hankali kar ta jiyo mu tazo ta balbalemu .

Tace "wlh kuwa dama yanzu ma da zan shigo sai faman hararata take.yaya ne ma yace in kirawo ki kawo fruit din na karasa ysnka miki .

Anan na bar mata komai na wanke hannuna na dauki kulan abinci na fita a palo nace "sadiya na gama sa,a zata kawo muku .

Sadiya tace"to uwar gida ran gida.

Na wuce banyi magana ba.

Ina zuwa na sami ya salman yana waya da alama da amaryar yake waya don haka nai sallar isha kafin na idar ya gama waya .
Chapter 84 · 0% Book details