Sashe 29
Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kauda kai yayi fuskarsa a daure yace" motar waye a wajen nan?
Mikewa nayi na isa gabanshi muna fuskantar juna Nace" motatace any problem... ...
Ya tari numfashina da fadin " waya baki?
Juyar da idona nayi nace " Allah ne ya bani ta hannun Ahmad.
Duk maganar da muke kallonsa nake har cikin ido yanda shima ya kafe ni da ido.
Ya gyada kai yace" kin tanadi amsar da zaki ba mamanki da Abba da sauran mutan gida in sun tambaya?
Murmushi nayi nace"yes of course amsar nan dai dana baka shi zan basu ko dai ?
Ya girgiza kai cikin bacin rai yace " RUMAISA me yake damunki?
Rike kafaduna yayi yana jijjigani da karfi runtse idona nayi ina jin zafin jijjigar har cikin raina.
Ban Ankara ba naji saukan mari guda biyu masu rai da lfy har saida na yanki numfashi na.
Ban gama dawowa hayyacina ba ya sake sauke min wata yayinda ya hankada ni da karfi .
Allah yaso ina saitin gado don haka kan gado na fadi naji kaina sai juyawa yakeyi .da kyar na dawo dai dai.
Cikin karfin hali na tashi ina kallonsa nace" don me zaka mareni ? Me na maka?
Idanunsa sun kada sunyi jazir yace" saboda ki dawo cikin hayyacinki kisan dawa kike magana.
Murmushi nayi na karaso gabanshi nace" ko kadan ban fita hayyacina ba nasan kuma da Wanda nake magana SALMAN ne ko? YAYANA kuma mijina in Allah ya yarda.wai me yasa kk abu kamar baka waye ba yanzu don nazo da mota shine laifi? Ko kishi ke damunkane?
OK na gane kishi ke damunka. Amma bari na tuna maka kuskuren da ka tafka.Yaya Kaine mutum na farko dana fara kai maka kaina amma kaki amincewa.da ace ka amince wlh ba abinda zanyi da wasu mazan kai kadai ka isheni domin nasan SOJA na jarumine!
Na karashe maganar ina murmushi. Shi kam gabadaya yanzu tsoro ma nake bashi don haka ido kawai ya sanya min.
Juyar da idona nayi cikin salon Jan hankali nayi juyi a gabansa sannan na kara matsawa dab dashi.nace" ka ganni na hadu sosai in ka amince zan mantar da kai dukkan hayaniyar duniya.
Na riko hannunshi nace" zo mu zauna na fada maka irin tanadin da na maka yayana.
Fizge hannunshi yayi da karfi.
Murmushi nayi nace " karka damu ko a tsayenma zamuyi.
Ina shirin rumgumeshi ya ja baya hade da fadin " Auzubillahi mina shaidanir rajim!!! Rumaisa kinyi nitsa ba kyajin kira .Na lura ba ma a cikin hayyacinki kike ba Allah ya shiryeki .
Dariya nayi nace " amin amma ni ina cikin hayyacina.duk da ma dai nasha amma ban bugu ba dan kadan nasha kawai.
Girgiza kai yayi cike da takaici ya juya zai fita kawai sai ganin mama yayi ta daga labule ta karasa shigowa ta kalleshi tace,duk abinda kukayi ina jinku salman.
Tabe baki nayi a raina nace" wnn kuma matsalarkice tunda kin cika bin kwakkwafi.
Juyawa nayi na wuce wardrobe don dauko rigata .
Ta kalleshi tace"Salman har yaushe zaka ci gaba da boye min halinda rumaisa take ciki? Salman kana ganin kai kadai zaka iya gyara wnn al,amari mai girma?
Ta girgiza mishi kai yayinda hawaye ya cicciko idanunta tace" Salman dole ne in San halinda rumaisa ke ciki koda kuwa zan hadiyi zuciya na mutu.nasan kana tausaya min ne gudun kar na shiga wani hali.....
Ta karasa hade da fashewa da kuka.
Ya girgiza kai idansa ya kara yin jazir yace " don Allah goggo amina ki bar kukan nan.
Ina jinsu na musu banza sai da nasa rigana sannan na zo gabansu nace" mama don Allah kiyi hakuri ki daina kuka ya salman yana son saka miki hawan jinine kawai shiyasa ya saka min ido idan kika biyeshi zuciyarki zai buga ki mutu ba shine da asara ba nine......
Ji kake Tass! Ya kuma wankeni da mari.
Mama ma ta shararamin wata marin hade da fadin " da ba don gudun karki fi haka lalacewa ba da na TSINE miki rumaisa amma bazan miki baki ba Allah ya shiryeki.
Ta fada cikin kuka.
Ni kam raina ya masifan baci duk da ma kaina ya fara daukan caji.
Nace" mama kika bude baki kika ambaci tsinuwa? To wlh bazan kuma zama dake ba ki fada min inda ubana yake in koma gurinsa tunda kin daina sona.
Na kalli ya salman nace" kai kuma munafuki azzalumi se ka zuba ruwa a kasa kasha kayi nasarar raba uwa da 'yarta.
Mama kam dada sananta kukan tayi ta na " na shiga uku ni Amina me zan gani ?
Tsaki nayi nace" wlh bazan barka ba bari naje na gayawa inna ta shiga tsakanina da kai.
Na kalli mama nace" kema zanje na hadaki da yayanki ki maidani gun ubana duk Ku huta tunda na zame muku matsala.
Na fita yayinda jiri ke dan dibana.
Ta kalli salman tace"kaga ta tafi.
Da sauri suka bi bayana.
Aikuwa a tsakar gida suka sameni ina zazzagewa inna dukkan abinda ya faru.
A haka Abba ma ya shigo ya samemu yana tambayan me ya faru.
Anana na fara kai mishi karar mama da ta maidani gidan ubana.
Kwata kwata bansan me nake fada ba maganganu kawai masu nauyi ke fita a bakina.
Abba ya girgiza kai cikin tashin hankali yace" innalillahi wa inna ilahirrajiun!
Mama kam kuka take ta yi kamar ranta zai fita Maman sakina ke ta bata hkr
Inna da Sadiya kam murna fal zukatansu don wnn shine babban burinsu dama.kuma gashi nan sunci nasara.sun jefa tsanata a zuciyar kowa bama salman kadai ba.
Abba ya kalli mmn sakina yace" Rabi zo ki rike yarinyar nan ki kaita dakinki ta kwanta ta sami isasshen bacci har sai ta warware.
Maman sakina tace to.
Anan tazo ta kamoni muka tafi dakinta.
Abba ya kalli mama yace " amina tun yaushe hakan ke faruwa.
Ta dan tsagaita kukan ta fara gaya mishi abinda ke faruwa duka salman kam har yana mamaki don har randa na kwana a dakinsu ta sani.
Abba kam sai salati .
Yayinda ya salman ya dafe kansa dake matukar yi masa ciwo.
Inna ta tabe baki tace" hmm ai dama nasan za,ayi haka kun dauki yara kun turasu jamia alhalin kun Sani sarai yanda rayuwar tamu a yau ta zamo.musamman wnn yarinyar na Dade da karantarta tsaf alhaji daga kai har salman na fada muku Ku mata aure tun wuri kukace sai tayi jamia tunda mamanta naso kun hadu gabadaya kin fifita duniya akan lahira to gashi nan kun ga sakamakon.
Ta kalli mama tace " Amina ba kuka zakiyi ba kamata yayi ki tuba ki gyara halinki domin abinda kika shuka ne kike girbewa.kin dauka abubuwanda kikayi a baya Allah zai barki ne? Hmm ai bazaiyiwu ba don haka gashi nan 'yarki ma.....
Abba ya katse ta da fadin "don Allah ki mana shiru tunda ba alkahairi zaki fada ba .wai baki ganin halinda take cikine?
Mama ta girgiza kai tace" yaya ka barta ta fadi duk abinda take so rumsisane taja min.
Inna ta tabe baki tace " bari ma kuji na fada muku wlh salman bazai auri 'yar iska karuwa mai shaye shaye ba .uwa uba kuma shegiya.don haka Amina ki raba 'yarki da dana don salman dana kamili ne ba watsasse ba.
Tana fadin haka ta juya ta koma dakinta.
Abba ya bita da kallo cike da takaici sannan ya kalli mama yace"amina kiyi hakuri nasan da zafi amma babu abinda ya gagari Allah kima rumaisa addua Allah ya shiryeta muma zamu yi mata don bazamu kyamaceta ba.
Mama ta share hawaye tace"Na gode yaya.amma maganar shatu gaskia ne bai kamata salman kamili ya auri rumaisa ba don haka kawai batun aure tsakaninsu ma abarshi don bata dace dashi ba.
Abba ya girgiza kai yace"wnn ba maganarmu bane in dai salman yana sonta to wlh ba Wanda ya isa ya hana ayi auren nan!
Jin maganar Abba yasa salman mikewa rai bace ya fice. Sosai yake jin tsanata!
Ni kam tuni nayi bacci abina.
Mama kuwa ta koma sashinta taci gaba da kukanta.
Yayinda inna da Sadiya suka kwana zuciyarsu fal farinciki.
Hauly ce👍🏻🥰
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹
👨🏻🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻🚒
*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚
~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```
Page➡26
***********Maman sakina ne ta je ta sami mama a side dinta ta shiga bata hkr.
" Amina matsalar da rumaisa ke ciki fa kamar asiri ne.
Mama tagoge hawaye tace"nima abinda nake tunani knn rabi domin lokaci guda rumaisa ta sauya.
Mmn sakina tace"Amina ance zato zunubi amma inaga abinnan kamar a gidan nan aka mata.
Mama ta tabe baki tace" kin rigani a baki na riga ki a zuci ne rabi.amma Allah mun tuba .
Mmn sakina ta Dan waiga bayanta taga ba kowa sannan tace " da dadewa na jiyo hirarta da sadiya naji tana cewa" indai ta yi amfani dashi shikenan bukatarmu ta biya.wlh Amina a lokacin ban kawo tunanin komai ba nama dauka ko raihanace don a kwanakin da ta dawo kamaru raihana ta yi ta zuwa kiji sunyi kus a daki na dauka ko itace .amma fa da naga halinda rumaisa ta shiga sai na fara tunanin ko dai ita suka bawa wani abun.
Mama tace" zai yiwu ai rabi don kina ganin rumaisa kamar wayayyiya wlh muguwar wawiyace yarda da mutane take da wuri
Maman sakina tace" kinsan Allah amina matar nan abar tsoroce wlh ni kaina da kika ganni da kyar na sami lfy ni da yarana a gidan nan. Sai da na tafi kauyenmu gun wani kakanmu na nemo mana taimako sannan muka sami lfy.
Abinda za,ayi in rumaisa ta warware gobe muje kawai koma me yake damunta insha Allah zamu dace.kuma ba malamin tsubbu bane irin mutanen nan ne da aljanu suka budewa ido wlh baya duba adduoi kawai yake badawa sai rubutun sha kuma.sannan yasan magungunan gargajuya sosai.
Mama ta danyi shiru sannan tace to ba matsala Rabi sai muje ai.
Mmn sakina tace" to yanzu ki kwanta ni zan koma sai da safe.
Sukayi sallama .ni dai ina ta sharar baccina ko a jikina.
Da safe mama tuni ta shirya tsaf ta dauki makullan mota ta fita sai gidansu ya salman.