← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 128

Sashe 30

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin mamaki ta sameshi kwance a Palo har da Karin ruwa aka masa.

Cikin tsoro ta karaso tace" salman me ya sameka?

Cikin karfin hali yace" goggo zazzabine wlh shine Na kira abokina doctor James kawai naga dare yayi kuma banson in daga muku hankali.

Mama ta girgiza kai tace"sannu Allah ya baka lfy .nasan duk sanadin rumaisa ne ka shiga cikin wnn hali.

Ya giigiza kai yace"aa goggo karkice haka kuma ma ai naji sauki sosai kinga ruwan kawai nake jiran ya kare na cire na tafi nayi breakfast ko inna ma basu Sani ba.

Mama tace " Allah ya baka lfy salman.
Yace"amin ina zakije goggo?

Tace " zamuje mu nemawa rumaisa maganin matsalartane.

Yace" me yake damunta?
Tace" ban Sani ba salman amma wadan nan abubuwa ba a banza takeyinsu ba.dole in tashi tsaye wurin ne ma mana mafita.

Shiru ya danyi sannan yace " goggo da dai kinci gaba da mata addua sai kiga koma meyene Allah zai yaye.

Ta yi murmushi ta ce" hakane salman addua kam kullum a cikin ta muke sai dai kasan Allah ma yace tashi in taimakeka.

Shiru yayi sannan ganin kamar hankalinsa bai kama bayasa tace" karka damu salman ba gun malaman tsubbu zanje ba ko kadan bazan yarda na kauce ba ka kwantar da hankalinka.

Yace " shikenan goggo na fahimceki Allah yasa a dace kuma.

Mama ta ce"amin

Anan doctor James ya shigo da sallama suka gaisa da mama.

Ta kalli salman tace " yawwa salman tunda naji kace salim ma zaizo ga nan makullin motarda rumaisa ta kawo a maida wa maishi kawai bama bukata.

Ta ajiye makullin a gabansa sannan ta fita.

Ina tashi na koma sashinta nayi wanka na shirya don maman sakina tace akwai inda zamuje.

A raina nace Allah ma yasa gidan Babana zata kaini in huta.

A palon Abba na sami mama nima na zauna na gaisheshi.
Nasiha ya dinga min sosai har da ayoyi ya dinga ja min.nikuwa ina karasa masa a raina.

Mama kam shiru kawai ta yi har Abba ya gama sannan muka tafi.

Nikam a baya na zauna mama da ke tukin mmn sakina a gefenta.

Suna hirarsu.har muka isa don kauyen ba nitsa sosai.
Gaskia har na manta rayuwar kauye.don haka komai sai ya dinga ban dariya.

Gidan da mukaje babban gidane na wani malami don harda almajirai muka tarar a waje suna karatu don haka muka wuce gidan.

Aka kawo mana tuwon dawa miyar kuka gaskia nikam zagewa nayi naci. Mama kam sun gagara ci.sai masara aka gasa musu sukaci.

Har sai bayan azahar Malam ya turo muje.

Sosai suka dinga hira da maman sakina ya na tambayarta labarin birni.
Sannan daga bisani ta yi masa bayanin komai.

Nan ya danyi shiru sannan yace"zaiyiwu asirin ne don gaskia bata da aljannu.amma akwai maganar sakaci da addini ma.
Ya kalleni yace" kafin hakan ta faru kin taba yin wani mugun mafarki?

Shiru na danyi sannan nace"eh nasha yi.

Yace " kamar me kike gani a mafarkin?

Na ce"eh na taba yin mafarkin wata mata ta sokamin wuka a ciki.sannan ina mafarki maciji ya sareni ko kare ya cijeni.

Ya gyada kai yace " Allah ya sawwaka yanzu zamu baku adduoi da zakuyi sannan za,ayi amfani da ganyen magarma insha Allah indai asiri ne to kome karfinsa bi.iznillah zai karye. Amma fa adduoin da yawa kuma sai kun jajirce kuma akwai na tofawa a ruwa tasha ta kuma shafa kullum har tsawon sati biyu.daga nan fa zakuga sauyi in Allah ya yarda.

Mama ta gyada kai cike da gamsuwa tace" in Allah ya yarda baba zamuyi kuma mun gode matuka.
Yace" ba komai sai dai kuma ina mai bata shawara ta yi riko da addini hannu bibbiyu azkar safe da yamma kar ya wuceta sannan duk abinda zatayi ta fara da addua.

Mama ta kalleni tace" kina dai ji koh.

Kai na daga mata don ni tuni na gaji da zaman maganar tasu ma haushi yake bani.

Sun jima suna tattaunawa.sannan daga bisani ya bamu komai a rubuce da bayani.

Sai kusan magrib muka dawo.

Mama kam ba alamun wasa a fuskarta duk wayoyina ta kwace ta kashe sannan tace a dakinta zan kwana.
Da kanta ta dinga min tofi a ruwa ta ban na shanye.

Da asuba kuwa ta tasheni bayan mun idar da sallah ta sakani gaba sai da nayi azkar din safe na karanta Qur,ani izu biyu don rabawa mana tayi tace ko wani Safiya zamu dinga karanta izu biyu.
Kitchen ma ranar tare mukaje.karfe shidda na gama shirin tfy mkrnta nayi breakfast duk abin nan idanunta na kaina har na gama ta karbi jakata ta duba sosai sannan ta kalleni tace jirani inzo in kaiki.

Ta shiga ciki ta dauko hijabinta da key din motarta muka fita.

A waje muka hadu da ya salim da ya salman suna shirin shigowa cikin gida.

Anan suka gaisheda mama nikam idona na kan ya salman yayi matukar kyau cikin kakinsa kamar na rumgumeshi wlh.

Shiko baima San ma inayiba na danyi gyaran murya nace " yaya ina kwana?

Ba tare da ya kalleni ba yace " lfy.
Nayi murmushi nace " ya jiki kuma?

Bai kuma ce min komai ba .
Na kalli ya salim nace " yaya jiya bamu ko gaisa ba kazo lfy ya kabarsu mummy?

Yace" kowa lfy .

Sannan ya kalli mama yace" goggo ina zakuje?

Mama tace makaranta zan kai ta.
Salim yace haba goggo gamu bari muje na kaita ki koma gida.

Ta girgiza kai tace" aa salim gabadaya yanzu na ajiye komai zan kula da tarbiyar rumaisa har ta gama makaranta!

Salman yace"aa goggo bazaki iyaba ki bar komai a hannuna.na miki alkawarin baza a kuma samun matsala ba .

Nan suka yi gefe sunata maganganunsu ni dai tabe baki nayi a zuciyata nace " kwaji da shi yan sa,ido.

Sai naga mama ta koma ciki ya salim ya kalleni yace" dan jiramu bari muje mu gaida su Abba sai mu tafi.

Bata rai nayi nace ni gaskia nayi letting.

Ya salman kam tuni yayi shigewarsa fuskar nan a daure.
Ya salim yace" ki jiramu nace ba dadewa zamui ba.

Ya shiga ciki shima na bisu da harara.

Basu jima ba suka fito muka tafi a motar ya salman.

Ya salim a hanya shima fada ya dinga yi min .
Ni dai gani nake kamar kowa ya tsaneni.

Har muka isa ya salman kam baice komai ba!!!

Hauly ce🤝🏻😍

🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*_Dedicated_* *_to_* *_Ummi_* *_Abdallah_*

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```

Page ➡27

***************Haka sukaci gaba da sanya ido a dukkan lamurana na fuskanci takura sosai a kwanakin.

Ahmad ya nemeni a waya har ya gaji kawai ya sameni a school anan ya nuna bacin ransa akan wai ya salman da ya salim sunje sun maida mishi motarsa kuma sun masa kashedi akaina.
Nima na gaya mishi yadda suka takura min a gida kwanan nan amma nace ya kwantar da hankalinsa so nake a gama exams ne nasan yanda zan bullo musu.haka na lallabashi ya tafi.

Salima da kawayenta ya kasance duk inda muka hadu sai sun zageni suce min karuwa saboda Ahmad ya kasa rabuwa dani alhalin ba aurensa zanyi ba.Ni dai bance komai ba.

Tunda muka fara exams nakejin kaina na ciwo kadan kadan addua kawai nake kar ya hanani jarrabawata don wani lokaci haka kawai sai inji kan ya Sara har naji hankalina ya bar jikina sai a hankali nake dawowa dai dai .

Anan naje nayiwa doctor hakim complain kasancewarsa general doctor ya rubuta min magunguna.kuma na sha amma shiru kakeji.

Allah ya karbi adduata randa muka gama exams ina fita kawai na yanki jiki na fadi ji nake duniyar na juyawa dani.

Jin dalibai nake sama sama sun kewayeni suna me ya sameta ko ta suma ne? a zo a kaita clinic.

Daga nan ban kuma sanin inda nake ba har tsawon kwana 2

Sannan na fara gane wayanda suke kaina.

Mama na gani sai fa,iza da sakina .

A hankali na bude baki nace"sis yaushe kuka dawo?

Sai naga fuskokinsu cike da mamaki suna kallona mama ta rike hannuna tace"rumaisa kina nufin kin ganemu?

Nace" mama na ganeku mana ai nasan lokacin da na fadi dazu ne aka kawoni nan kuma a ka sanar daku.

Ta girgiza kai tana share hawaye tace " rumaisa yau kwananki biyu anan baki San inda hankalinki yake ba.ba kya gane kowa.

Na mike da sauri sai naji kaina na juyawa.

Da sauri mama ta rike ni tace" kwanta kwanta bari na kira doctor. Sakina Ku lura da ita.

Mama ta fita anan su fa,iza suka shiga yi mun sannu.

Doctor hakim ne ya shigo.

Nan ya kalleni yayi murmushi yace"Rumaisa ya jiki?
Nace,da sauki doctor.
Yace" yanzu me kk ji ?

Nace ciwon kai kadan kadan sai jiri kuma ina jin tsigar jikina na tashi.

Anan ya gwada min bp sannan ya kalli mama yace" mama kinga jininta ya fara sauka ma.yanzu dai alhamdulillah.abinda za,ayi a sama mata abinci taci tasha magungunanta mugani zuwa anjima zan dawo in dubata.

Mama tace" to doctor mun gode.

Yayi murmushi yace " babu komai mama Allah ya bata lfy.

Mama ta ce amin.
Anan ya fita.

Mama tasa min abinci na danci nasha magunguna na kwanta anan bacci yayi awon gaba dani.

Har yamma na tashi anan ya salman da ya salim da Abba suka shigo suka min sannu.

Naji sauki sosai Ahmad ma yazo don su ya salman na fita ya shigo cikin shigan many an kaya kamar bashi ba.
Ya gaisheda mama sannan ya kalleni yace"Queen ya kika karaji?
Nace" da sauki waya fada maka banda lfy?

Yace" Juliet ce.
Daga nan shiru na masa. Har ya kari zamansa sannan ya tashi bandir din dubu dubu ya fitar ya ajiye a gefena sannan ya kalli mama yace " mama Allah ya bata lfy na tafi.

Mama tace " kuma har da dawainiya haka ? Mun gode a gaida gida.

Ni dai ban kuma ko kallonsa ba har ya fice.

Mama ta kalleni tace" wai waaye wannan din kuma?

Nace"Ahmad ne......
Chapter 30 · 0% Book details