← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 128

Sashe 119

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nafisa ta dago ta kalli farida hade harararta tace"wai ke me yake damunki ne farida kinga ni fa ba sa,arki.......

Ya salman ya daga mata hannu da sauri yace"ki tashi kije ciki and kuma kar ki sake maimaita wnn kuskuren da kkyi yanxu.

Tashi nafisa tayi jikinta a sanyaye ta wuce part dinta ko kayan da ta siya bata dauka ba.

Nidai ina ta kaina don saida na dauki tsawon lokaci kamin numfashina ya dai daita har munir ma ya fito ya samemu haka suna zagaye dani sai da sukaga na koma normal snn hankalinsu ya kwanta.

Snn ya salman ya tashi yace munir yazo suyi magana.

A tare suka tafi .kallona na mayar kan farida nace"me yasa kika fadawa nafisa irin wnn maganar ?

Tace"mama fa tasani sarai ciwonki zai iya tashi in ta fesa miki turaren nan

Na harareta hade da fadin "ina ruwanki.farida nasha warning dinki akan nafisa amma ba kyaji to wlh ki kiyayi fushina kuma kije ki bata hkr yanxu.

Tace"kiyi hkr mama zanje yanxu.

Ta wuce ranta a bace.lokaccinda ta shiga dakin nafisa ta gama waya da nabila don haka ta kalli farida tace"me nene kuma.

Cikin jin haushi farida tace"kiyi hkr da abinda na fada miki dazun.

Murmushi nafisa tayi tace"babu komai farida ya wuce ya jikin momyn ku?

Farida bata amsa ba ta fita kitchen ta wuce don ta girkawa munir abinda zai ce gashi magriba ya kawo kai duk ta gaji gashi ranta a bace .

Nabila kuwa duk maganar da sukayi da nafisa suna gamawa ta kira adda A'i ta gaya mata komai tana"don haka kiyi saurin karbar wnn kudin a hannun nafisa in ba haka ba wlh zata kashe a banza da wofi.don har na roketa ta ban wani abu aciki taki.

Adda A'i tace"waya gaya miki ita zatai amfani dashi?hmm ai dan iskan nan nasan zata bawa wadan nan kudaden ko shakka banayi.kedai ki yi shiru nasan me zanyi akai.

Anan sukayi sallama adda A'i ta kira nafisa ta dauka ko gaisawa basuyi ba adda A'i ta fara kora mata bayani.

Sakin baki nafisa tayi don bata taba tunanin nabila zata mata haka ba don haka ranta ya matukar baci tace"adda kudin nan nawa ne kuma ina bukatar abina don haka ni bazan bayarba.

Adda A'i a fusace tace"kinsan Allah nafisa idan kk kuskura kika ba suraj kudin nan sai na matukar batamiki don haka ki turo kudaden nan maza na baki nan da kwana biyu.shashasha mara hankali kawai bazaki gane me nake fada miki ba se kinyi kuskuren raba aurenki da salman!

Ta katse wayar rai bace a bangaren nafisa itama ranta a bacen tace"hmm wlh bazan tura miki ba se dai ki kari jarabarki mutum sai shegen son kudi duk abinda kika samu baki gode Allah ba.

Mtswww taja tsaki yayinda ta kira nabila amma bata dauka ba cije lebe tayi tace"wlh adda nabila sai nayi maganinki tunda kin iya hada munafurci.

Daga nan fitowa tayi ta sameni a dakina tana min sannu hade da bani hkr.

Nace mata babu komai karta damu ya wuce .

Adda A'i kuwa jin har sati daya shiru nafisa bata turo kudin ba kuma in ta kira ma bata daga wayar yasa ta ajiye komai ta taho kano inna sai mamakin zuwan nata takeyi tace"A'i lfy?

Adda A'i tace wlh lfy lau goggo nazo na duba ku ne .

Tsaraba sosai tayiwa innah don haka inna baki har kunne ta dinga sanya albarka.

Sadiya kuwa jin zuwan adda A'i yasa gabadaya hankinta yana bata ba zuwan haka kawai bane.sai dai tayi tayi da ja,afar ya barta amma yaki yace idan ta kuskura ta fita to karta dawo mishi gida.don haka sadiya ta hkr amma hankalinta na gida.

Adda A'i salman ta kira ta sanar dashi zuwanta wai yabar nafisa tazo tunda ita ya hanata zuwan masa gida.

Yace"hmm ni ai bana gari adda ina lagos daga nan ma dubai zan tafi.amma lfy kk je kano a wnn lokacin ?

Tace"lfy lau nazo ne bikin gidan hajia fati.

Yace"ok to kawai zan ce taje ku hadu a gidan innan amma bayan nan banason kije koina da ita ba.

Dan tabe baki adda A'i tayi tace"ni dama ina zanje da ita kawai tazo mu gaisa ne .

Yace shikenan.

Daga nan sukayi sallama.
Don haka ya kira nafisa yace ta shirya driver ya kaita gidan innah.

Daga nan bai kuma yi mata karin bayani ba don harkokinsa nada yawa.

Nafisa tsaki tayi tace ni wlh goggon nan ta cika matsala ko uwar me zanje na matane oho.

Sai da tay baccinta iya son ranta har azahar snn ta shirya hankalinta kwance ta fito dakina ta shigo ta sameni ina kokarin shiga wanka muka gaisa tace"bari naje gidansu inna.

Nace"to lfy dai koh?
Tabe baki tayi tace"wayasan ma goggo da fitina kawai yaya ya kirani wai in shirya driver ya kaini gida.

Nace"to Allah sa lfy ki gaishesu .

Ta dauki hanifa tace "zamuje da babyna ki bata nono don kar muje tayi kuka.

Nayi murmushi nace"ai kuwa sunsha yanxu sun koshi kuje kawai ni wanka zan shiga.

Don haka da fara,arta ta suka fita.

Bayan driver ya saukesu suka shiga gida a palo ta tarad da inna ita kadai ta zauna suka gaisa innah ta karbi hanifa tana cewa " o nafisa ko arbain basuyi ba kk fita da ita.wato rumaisa dai bazata taba yin hankali ba.inke baki san komai ba ita ai ta sani yaushe zata bari ki fita da wnn jaririyar tun basuyi arba,in ba.

Nafisa tace"kai goggo sauran fa sati daya ne suyi arbain din kuma meye a ciki dan na dauketa munzo nan tunda naga ai gidane.

Inna tace" to kije ciki A'in na daki.
Nafisa ta dan zaro ido tace"adda A'i kuma yaushe tazo?

Inna tace au baki sani ba ai tun jiya ta zo .

Nafisa ta tashi zuciyarta cike da fargaba ta shiga dakin ta sami adda A'i tana waya da mutanenta na kasuwa tana ganin shigowar nafisa ta watso mata harara da ya kara tsoratata.don haka ta nemi wuri ta zauna .

Bayan adda A'i ta gama waya ta kalli nafisa tace"se yanxu kikaga daman zuwa?

Nafisa ta dake tace"aini adda bansan kinzo ba sai dazun yaya ya min waya.....

Adda A'i ta daga mata hannu tace ya isa haka ina kashe min waya kk in na kira a karshe ma kk sani a blacklist to gashi nazo yanxun kuma me zakiyi?

Shiru nafisa tayi ta rasa me zatayi adda ai ta gyara zamanta mai kyau ta kalli nafisa tace"kinsan Allah idan baki bani kudin nan ba zanyi mugun saba maki.domin wlh bazanyi dawainiyar karatunki a banza ba.dubi yadda kk koma kk yi clean duk cikinmu ba wacce tayi jamia ma sai ke irin kudin da na kashe a kanki ko yarana ban kashe musu ba amma yanxu ni zaki juya baya don kinga yanxu komai dina yana kokarin watsewa...

Nafisa tace"haba adda kuma shine da gori.amma ai kudinda nayita tura miki kike business dashi kina juyawa sun isheki don haka bance ki dawo min da ko sisi ba ki rikesu a madadin wanda kk kashe a baya kika yi dawainiyar tawa dashi nasan zasu isheki ai?

Adda ai ta hasala sosai wata uwar harara ta dokawa nafisa tace"har wani kudin kirki kike tunanin ki banine to bari kiji harda kudadena na cika snn kika business dinnan yayi karfi haka.don haka ni yanxu kikawo wnn kudin kawai in yaso idan kika ban wnn din se ki kashe auran naki kije ki zauna da matsiyacin suraj din inga uwarda zai tsinana maki tunda bakida hankali wawiyace ke.

Nafisa tace"hmm adda kudin can fa ki barma maganarsu don babu su a halinda ake ciki yanxu nayi bukatuna dasu.

A fusace adda A,i ta dauke fuskar nafisa da mari zuciyarta kamar zai fashe tace"kin dai baiwa dan iskan can zakice to wlh bari kiji na baki nan da wata daya ki nemo kudin nan duk inda suka shiga ki bani don bazan sha wahalarki a banza ba.in ba haka ba wlh sai na fadawa baba duk abinda kike shirin yi kuma kinsan matakin da zasu dauka akanki in sunji baze miki dadi ba.shashasha kawai mara wayo.ana miki gata baki gani an gaya miki samun miji kamar salman a wnn zamanin yana da sauki ne?

Nafisa tana dafe da kunci ta tashi da hawaye tace"shine xaki mareni akan dan kudinda kk kashe min ?to shikenan ince dai in na biyaki zaki kama gabanki ki rabu dani?

Adda a'i tace sosai ma in dai kk biyani to shikenan ba ruwana dake in yaso ki kashe auren kije ki auri dan iskan naki kamar yadda nace miki a baya.

Nafisa ta gyada kai ta fice zuciyarta na suya a palo ta sami inna karbar hanifa tayi inna na tambayarta lfy amma bata ce komai ba ta fice .

Nima da ta dawo ban gane mata ba duk da na tambayeta tace min babu komi.

Bayan sati da faruwan haka ya salman ya dawo daga dubai bazata sai ganinsa kawai nayi gashi nafisa bata nan tunda safe don haka na karbi dawainiyarsa.

A dakinsa na sameshi ya na kokarin rufe jakarsa me cike da kudi kuma dollars ne zalla.

Na kalleshi nace"yaya irin wnn kudi haka a gida?

Yace"no ba ajiyesu zanyi anan ba dama gobe zan kai bank kudin wani kwangilane....

Ya karasa rufewa ya mika min jakar yace ungo adana min bari inyi wanka inzo inji lfyrki momyn twins.

Na karba ina murmushi shikuma ya shige toilet yayinda nasa kudin a drawer na kulle na fita don shirya masa abinda zaici don yace min ya kwaso yunwa.

Bayan ya fito palo nan yace na kawo twins nace duk sunyi bacci yaci abinci tukun ya huta kan nan sun tashi .

Muna cikin hakan nafisa ta shigo gabadayq zuciyarta ta shiga fargaba wani karya zata mishi na fitarta.

Ina ganinta na tashi hade da fadin alhamdulillah mai fili yaxo mai taburma se ya nade.

Nayi mata sannu da dawowa daga nan na fita barsu na lura ransa ya baci da fitanta sosai .ko ya zasu kare oho.

Aikuwa sunsha drama don har kyawawan mari ta samu guda hudu masu kyau yayinda ya
Koreta daga part dinsa gabadaya.
Chapter 119 · 0% Book details