← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 128

Sashe 42

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan tfyrki shatu ta maida yayyunki kamar remote control sai yanda tayi ni nan bata barni ba duk da ba kulata nake ba amma saida tasa yayanki ya tsaneni Amina ba abinda bangani ba na makircin shatu sai da na tashi tsaye da rokon Allah ba dare ba rana snn Allah ya ya kawo min sauyi ba kiga tun kan salim ban kuma haihuwa ba? Sai yanzu dana samu faiza wlh yayanki munfi shekara biyar da yayanki a gidan can ko hannuna baya rikewa.

Amina ta zaro ido cike da mamaki tace " kuma kika jure?

Zuwaira tace " gidanmu na koma wlh amma abin mamaki bai taba nemana ba sai da nayi good 3 years ance ya sakeni yaki karshe dai haka Abbana ne yace in dawo inci gaba da addua don sunsan abin ba haka kawai bane.don haka sai na dawo shatu kam sai abinda taso takeyi a gidan bayan tfyrki ta haihu har sau biyu amma yaran Allah baiyi zasu rayuba.
A lokaci guda Allah ya amshi adduata .komai ya dawo normal.
Inda reshe ya juya da mujiya shatu ta somagirbar abinda ta shuka ita da yayanki har dukanta yayi da cikin Sadiya sannan yaje ya kawo mata kishiya wato rabi matar kirki wlh batada tashin hankali da kowa kinga lokaci guda da zuwanta guda ya canza .shatu bayan ta haifi Sadiya ta sake samun raihana ta haifi raihana da wata daya na haifi faiza sati daya akai itama rabi ta haifi sakina sune kika gansu gabadaya suka taso Kansu daya yanzu shekarunsu bibbiyu da dorin watanni.

Amina ta jinjina kai tace " aunty kinyi matukar kokari wlh gaskia na jinjina miki don shatu babu alkhairi a tare da ita zama da ita sai an jajirce.

Zuwaira ta sauke ajiyar zuciya tace "yanzu dai Alhamdulillah mun gama gininmu a Abuja ma zamu koma har da salman don ni na ke kula da dukkan lamarinshi shida salim yadda suka taso kamar twins haka muke so har su girma yanzu mu da kano sai dai muzo Hutu.

Amina tace " gaskia aunty Zuwaira na tayaki murna kuma nauyin tarbiyyan salman da kk dauka Allah ya biyaki.

Zuwaira tace " amin yanzu ki kwanta nasan kin gaji da yawa.
Da haka suka kwanta Amina dai bata yi bacci ba sai juyi take ta rasa me yake mata dadi a rayuwa.

Gari na wayewa Zuwaira ta tashi ta shirya wa amina breakfast mai rai da lfy yayinda ta duma ruwa tayiwa rumaisa wanka ta shirya ta tsaf cikin pink din Riga da wando masu nauyi don ana sanyi daganan ta bata maganinta.

Ta kalli amina tana murmushi tace " meenah wnn yarinya tana kama da Ibrahim ko dai 'yarsa ce bani labarinki.

Amina ta gyara zama da niyyar baiwa Zuwaira labarinta kawai sai ga shatu ta fado dakin ko sallama babu ta kalli amina fuska daure tace " kin wani mimmke kafa kin dauka zamu barki kici gaba da zama ne ki tashi yayyun naki na kiranki.

Amina ta zubawa shatu ido daga bisani tace " shatu ki dinga sa tsoron Allah a lamuranki ni yanzu banda lokacin ki.

Ta be baki shatu tayi tace " kima ce wani abu mana ki gani.

Zuwaira tace kinga shatu kawai kije tana zuwa.

Shatu tace " wlh Zuwaira ki taka tsan tsan da Amina in ba haka ba igiyar aurenki na daf da tsinkewa .

Zuwaira tace" tunda ke kika kulla ko?

Shatu ta fita tana fadin " ki dai bi a sannu.

Amina ta tashi ta fita zuwa palon Mohd a tsakar gida ta gaisa da rabi cike da fara,a.

Tana shiga palon ta samesu zaune dukansu biyu fuskarsu kamar an aiko da mutuwa ta zauna tana shirin gaishesu Mohd ya daga mata hannu hade da fadin " bamu bukatar gaisuwarki Amina kawai ki fada mana me kk zo yi nan gidan?

Amina ta sunkuyar da kai hade da fadin " na dawo ne yaya....

Kasim ya karba "saida kk gama yawon iskancinki da Ibrahim din zaki dawo? To bari kiji idan har kina so zama da mu to sai dai ki dauki shegiyar yarinyarki ki maidata gun ubanta!!

Amina ta dago a tsorace tace " aa yaya don Allah Ku rufan asiri wlh bazan iya rabuwa da 'yata ba.

Mohd yace " to kuwa zaki bar gidan nan don bazamu rike shegiya ba zabi ya rage naki.

Amina ta sa kuka tace wlh yaya rumaisa ba shegiya bace .

Kasim yace " kinga kar ki manna mana hauka kawai mun baki nan da 24 hrs ki zaba ko ki maida wnn shegiyar yatinyar inda kk sameta ko kuma ki tattara ta Ku bar mana gida.

Amina ta fusata sosai don haka ta mike ta share hawayenta ta kallesu tace " wlh babu Wanda ya isa ya rabani da 'yata kwaya daya da nakeji da ita kamar rai don kawai na dawo shine zaku wulakantani saboda kunga iyayenmu basa raye wnn shine wasiyyar da mahaifinmu ya bar muku a kaina? A tunanina ko me zan yi a rayuwa baza Ku gujeni ba.amma na gode kuma in dai na amsa sunana Amina ni kuma daga yau na yanke duk wata alaka dake tsakanimu bazan sake nemanku a rayuwa ba HAR ABADA!!!!!

Tana fadin haka ta fita cikin fushi taje ta dauko kayanta tana kuka Zuwaira ma kuka takeyi tana don Allah amina ki tsaya Ku fahimci juna.

Amina ta ce " wlh bazan tsaya ba kawai ki barni zanje inyi rayuwata ni kadai da ',yata har abada.

Ta fita da sauri ta bar gidan tana kuka ba tare da ta San inda zata ba.

********************

Mama ta kalleni yayinda ta share hawayenda ya zubo mata tace " kinji dalilin zamana a kauyen gano knn don bazan iya zama cikin gari dangina suna nunani ba .

Bayan tafiyata momynku hajiya Zuwaira bata hkr har bayan sun bar kano sun koma Abuja anan ta dinga bama salman da salim labarina da yadda na ke sonsu tun suna kanana.da taimakonta dana salman da salim yayyuna suka sauko daga fushin da suke har sukaje kauye suka nemeni muka yafewa juna snn suka ce suna son na dawo gidan nan da zama.ni kuma bana son dawowa nan saboda shatu shiyasa na amince wa Marigayi Alhaji aminu kawai don ya Dade yana son muyi aure ina kauce masa saboda ke don bana son abinda zai taba mutuncinki RUMAISA.

Sannan ina son ki Sani na baki labarin ki ne domin hankalinki ya kwanta ki daina zargina amma ko kadan bana son tunawa da rayuwa da nayi a YOLA.

RUMAISA yanzu me kike ga yafi dacewa dake zaki hkr da neman mahaifinki ne ko kuma zaki nrmeshi?

Nima kuka nake sosai na daure na goge fuskata nace " mama gaskia kin fuskanci tsananin rayuwa amma inshaa Allah komai zai zo karshe ni na yanke shawaran neman mahsifina koda kuwa bazai karbeni na tabbata dangina suna sona.mama zan tafi yola goben nan kuma ki kwantar da hankalinki zan dawo cike da farin ciki in Allah ya yarda Kuma INNA zataji KUNYA !!!!!!

Mama tace " da kyau ni kuma ina miki adduan fatan alkhairi kuma da kaina zan kaiki ki hau mota amma kamin ki tafi ina son ki daure kije ki fadawa salman da kanki kuma ina son ki daina jin haushinshi ki masa uzuri dik abinnan da yake miki ba laidinshi bane rumaisa salman na sonki sosai matsalar daga mahaifiyarshi ce sai dai muci gaba da addua.

Na goge hawaye daya sauko min na ci gaba da kallon photon mahaifina IBRAHIM AHMAD GALADIMA ( LAMIDO)
haka kawai na tsinci kaina da sakin murmushi na kalli mama nace " mama amma kinsan daddyna ba,ason sa ba ya miki haka ba asiri aka muku don a rabaku kuma nasan zuwa yanzu asirin ya karye.

Mama tace " to amma a tunani ya kamata ace ya nememu ba wai nitsan guri ba.

Jikina a mace nace " eto amma Ki kwantar da hankalinki komai zai daidaita insha Allah!

Tace "to Allah yasa.

Da haka muka kwanta gaskia ranar nayi baccin dadi don har mafarki nayi wai ina hanyar tfy YOLA!

Hauly ce🥰👍🏻
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰

*Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤*

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```

Page➡37

******** Gari na wayewa kuwa tun shidda na gama shirina tsaf cikin bakar Riga doguwa mai kyan gaske yasha stones nayi mflng din gyalen na fito tamkar jinsin larabawa.

Tea kawai nasha nacewa mama bari inje in sallami ya salman.

A harabar gidansu na sameshi yana goge motarsa .

Jin takuna yasa shi juyowa karaf mukayi ido hudu saida naji gabana ya fadi kai ya salman akwai kwarjini.
Da sauri na cire idona shikam ya shagala da kallona har ya manta mota yake gogewa.

Ina shirin karasawa gunsa kawai naji an bugeni da karfi saura kadan in fadi Allah ya rufa asiri.

Dubawanda zan yi sai naga ashe nabila ce ta shigo da saurinta ta kawo ma ya salman break fast shine kamar an korota tsabar rawar kai.

Bata ma San ta bugeni ba tuni ta isa wurinsa tana kaudi shikam fada ya shiga yi mata da fulatanci kamar zai daketa duk da bajin su nake ba amma na fahimci yana fada ne akan tureni da tayi kuma bata ce min ko sannu ba.

Ta juyo jikinta a mace ta kalleni hade da fadin "Isa wadu munyal( sannu kiyi hkr)

Na gane hkr take bani murmushi nayi na girgiza mata kai nace " babu komai .

A raina kuwa cewa nayi wnn abun ne ya salman ze aura lallai akwai kallo .

Ta wuce palonsa don ta ajiye mishi abincinsa .

Gabadaya binta mukayi da kallo tfy take bazar bazar har tana tuntube.abun ya ban mamaki lokacin da ta zo wata wawiya da ita shiru shiru bansan a yaushe ta koyi rawar kai haka ba.

Na Dan numfasa snn na karaso gabansa nace " yaya ina kwana?

"Lfy lau kin gama shiryawa ne?

Nace " eh

Yace " to ki dan je ki jirani barin inyi breakfast nayi wanka.
Chapter 42 · 0% Book details