Sashe 49
Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na karasa fada cikin kuka ya samir ya girgiza kai cikin damuwa yace " babu komai Ihsan hakan nan zaki masa bayani duk da munsan abune mai nauyin gaske .amma ba komai addua shine zai warware mana wnn matsalar.
Na gyada kai nace " hakane yaya.
Daddy ya kirani ta wayar ya samir don bai sameni a tawa ba haka muka sake sallama.
Ya samir yayta rarrashina sai da yaga tashin jirginmu snn ya tafi.
Na isa Abuja lfy kasancewar daddy yayi goggo Ummi magana tuni driver ke jirana kawai muka wuce gidan goggo Ummi.
Ruma da gudu ta tarbeni cike da farin ciki domin sai yau Allah yayi haduwar mu don bana samunta.
Ta kalleni tana murmushi tace" yaruwa rabin jiki.
Nima murmushi na mayar mata amma na karfin hali nace" na,am 'yar uwa yau Allah yayi haduwarmu sau biyu zuwana baki nan.
Tace " eh wlh duk naji haushi.
Anan ta karbi jakata mu ka tafi ciki goggo Ummi cike da fara,a ta rumgumeni tana min sannu da hanya.
Sai bayan munyi isha muka hadu muka ci abinci mun dan taba hira kadan.
Muna shirin kwanciya knn goggo Ummi ta shigo dakin ta zauna kan gadon kusa dani ta kalleni tace " Mamana naji labarin mara dadi jiya lamido ke sanar dani.
Sunkuyar da kai nayi kawai bance komai ba.
Tace " kiyi hkr Ihsan duk bama son wnn hadin mun fi so ki auri zabin ranki.amma mai martaba yafi karfin mu bijire ma umarninsa.kiyi hkr Allah yasa hakan shine mafi alkhairi a gareku.
Nan da nan hawaye ya ciko ido nace " amin goggo.
Ruma tace " mummy me ye faru?
Goggo Ummi tace " mai martaba ne yace a hada Ihsan aure da yarima Abdallah......
Mikewa ta yi da sauri tace"what!!! Mummy Ihsan kuma a hadata aure da Yarima ? Akan me to?
Goggo Ummi tace " to gashi nan dai mai martaba ya Riga ya yanke hukunci.....
Dan tsaki ruma taja tace " ni bansan me yake damun tsohon nan ba.Wnn Yarima Abdallahn mummy in dai ba Allah ya shiryeshi bama Ihsan bazata iya zama dashi ba matansa ma hkr suke yi dashi don tsabar jiji da kai ga balain tsiya ga kuma shan taba da ya mayar kamar wani cin........
Goggo Ummi ta katseta da fadin ke dan Allah kyaleshi hakan nan wayace miki yana shan taba?
Na goge hawaye na nace " yana sha goggo dazu kamin na taho ma yazo kuma hayakin taban ya buson a hanci kuma inada athsma.
Goggo Ummi tace " subhanallah wai yaushe Abdallah zai shiryu ne ni Ummi ?
Ruma tace " mama yanzu shikenan raba Ihsan za,ayi da salman wlh mama salman yana da kirki don Allah mummy kar Ku bari ayi wnn auren don wlh basu dace ba babbane fa sa,anku mummy snn matansa uku ina Ihsan zata kaishi.
Ta karasa maganar cike da takaici ta ce" mama da kinsan bana son a kaini kano amma koda naji an ce Ihsan yaruwatace kuma zata auri salman mu zauna gida daya Sai naji dadi sosai a raina har hankalina ya kwanta amma mama kawai azo ace Yarima zata aura?
Goggo Ummi shiru ta yi don itama Sam bata so.
Ni dai kuka naci gaba da yi.
Yayinda ruma taci gaba da maganganunta.
Goggo Ummi rarrashina ta ringa yi har saida taga hankslina ya kwanta snn ta tafi.
Washegari kuwa da sassafe na gama kintsawa mukayi sallama driver ya dawo dani kano lfy ko ruwa bai tsaya sha ba ya juya Abuja ni kuma na shiga gida sashin mama.kawai ta ganni cike da mamaki tace " ke kuma daga ina da sassafe haka ?
Nace "daga Abuja gidan goggo Ummi can na kwana.
Tace " ai ban Sani ba da na kirata don ke dai layinki duk a rufe salman duk ya bi ya damu
Allah sarki yayana na fada a zuciyata snn na wuce daki na ina cewa mama" sauri ma nake zan wuce nakaranta yanzu motata batayi datti ba koh?
Tace " ba abinda ya sameta jiya da yamma ma da ita na fita unguwa.
Nace " to
Bayan na ajiye kayana na dau jakar makarantata da key din mota na fice ina mama Sai na dawo.
Lokacin da na fito da motata Sai ga ya salman cikin shirinshi tsaf da kakinsa ido na zuba mishi don tsabar yanda naga ya kara min kyau yau kuma ko dan kakin yana matukar amsarsa sosai.
Ina shirin fita in gaisheshi kawai saiga sukhaina ta fito daga cikin gida zata kai mishi breakfast tasha uban kwalliya ga daurin dankwali da ta kashe ta zuba gashi baya har canza tfy da ta ganshi.
Hmm binsu nake da kallo cike da yanga take masa magana amma Sam hankalinsa na kaina ganin banyi niyyan sauka ba yasa shi karasawa sauke glass nayi fuskata ba yabo ba fallasa nace" yaya ina kwana?
Shiru yayi tukun kamar mai nazarin wani abu.ni dai inda sabo na saba.
A hankali yace " baby yaushe kk dawo ?
Nace bai jima ba
Yace" OK yanzun school zaki tafi?
Nace" eh
Ya gyada kai snn yace "a dawo lfy.
Nace " na gode.
Naja motata na kara gaba ina lura da kallon da sukhaina ke bina dashi yau ma nace " hmm kyaji dashi.
Yau makarantan ma banji dadinsa ba duk lectu lectures da akeyi ba Wanda ya shiga kwakwalwata.
Bayan nayi sallar azahar ina shirin dawowa gida Maryam ta sameni tace " Queen yau ya na ganki very doll haka?
Nace hmm ke dai bari kawai Maryam gaba daya Na rasa me ya ke man dadi a rayuwa.
Tace " to me ya faru?
Kamar bazan yi magana ba sai naga kuma gara na fada mata ko zata bani shawara nan na gaya mata.
Gyara zama ta yi tace " tab babban magana Queen haka zaki zuba ido a rabaki da salman matashi jarumi kyakkyawa? Aje a hadaki da tsoho mai mata uku da yara shidda?
Nace "ba fa tsoho bane ke.
Tace" kk ce sa,an mamanki ke bari kiji wlh kika aureshi ba abunda zaki samu a jikinsa duk romon an kwashe salam zakijishi........
Tsaki naja cike da takaici nace " ke dan Allah dakata da maganganunki na banza ke ba daman a miki tadin arziki dake sai kin kawo iskanci a ciki?
Dariya ta yi tace " ai gaskia ne Salman shi ya dace dake kinga gashi jarumi kakkarfa soja yanaji da lfy zai gamsar dake hundred % wancan kuma wlh duk basir ya cika mishi ciki.
Takaicin Maryam yabi ya isheni shiru kawai nayi ina kallonta .
Bayan ta gama maganganunta na banza ta ce" kinga Queen abinda za,ayi akwai wani malamina aikinsa kamar yankan wuka idan mukaje gunsa a cikin sati guda zai wargaza wnn auran ke dai ki tanadin kudi kawai masu tsoka?
Harara na watsa mata nace "wai ni rumaisa kk tunanin zan dauki kudi na inje in kaiwa wani katon banza ya shirga min karya? Inzo daga baya ina dana Sani? To ba dani ba kema Allah ya shuryeki ki gane hanya madaidaiciyq.
Ta shi nayi na dauki jakata nace " kinga ni tfyta zanyi se gobe.
Jikinta a mace tace " to Queen amma ki daiyi tunani.
Nace" naji se anjima.
Ina isa gida wanka na yi na goge jikina na shafa mai na saka doguwar rigana na material sallar La,asar nayi snn na zauna gaban dressing mirror na fara gyara gashina .
Tsaki nayi nace " kai gaskia ya kamata inje saloon kaina ya cushe da yawa sai zafi yake min ina ta....
Ta cikin mirror na ga ya salman tsaye a bayana ya zuban ido ko kyaftawa bayayi.
Mikewa nayi na juyo muna fuskantar juna fuskana ba yabo ba fallasa nace " yaya.
Shikan murmushi ya min hade da fadin " yaushe kk fara magana ke kadai?
Sunkuyar da kaina na yi bance komai ba .
Yace " nazo karbar tsabar furana nasan kin kawo min.
Jikina ya mutu sosai domin ban kawo mishi ba.
Ganin nayi shiru sosai yasa shi fadin " ya dai?
Na daure nace " kayi hkr yaya wlh ban kawo maka komai ba amma zan sa a kawo.......
Hannu ya dagamin yace " aa ki bari kawai.
Na dago a hankali na kalleshi nace " kayi fushi ne?
Ya girgiza min kai yana kallona yace" rumaisa jikina yana bani akwai wani mummunan abu da yake shirin faruwa dani. Musamman dana lura da yanayunki daya sauya rumaisa me yake faruwa?
Ba shiri na saka mishi kuka. A rude yace " subhanallah me ya faru rumaisa ki gaya min don Allah.
Ya kamo hannuna ya zaunar dani gefen gado yace" Rumaisa don Allah ki bar kukan nan yana tayar mun da hankali .
Ya tsugunna gabana yace" kinga fada min me ne ne?
Kauda kaina na yi naci gaba da kukana.
Mikewa yayi jikinsa a mace ya fita ba jimawa ya shigo tare da mama yace" kingan ta nan goggo Amina taki ta gaya min me yake damunta sai kuka.
Mama ta zauna gefena ta jawoni Jikinta tace "rumaisa nima na lura tun dawo warki akwai damuwa a tattare dake ki fada mana me kk tattauna da mahaifinki ?
Na rasa ta inda zan fara fada masu kawai naci gaba da kuka.
Mama ta ce " to ko kina da Wanda tafini ne?
Girgiza kai nayi da sauri.
Tace"to kinga ki fada mana me ne yake faruwa.
Cikin dauriya na goge hawayena nace " mama daddy ne yace mai martaba yace za,a hadani aure da yarima Abdallah. ...
Ido ya salman ya zaro hade da fadin " what!!!!!
Kirjina sai da ya buga na sunkuyar da kai da sauri.
Mama ta ce"Hmm lallai ma wlh bazaiyiwu ba kawai daga ganin kin koma wajansu? Baki fadawa daddyn naki akwai maganar aure tsakaninki da salman ba?
Cikin muryar kuka nace " mama ya Sani.
Tace " OK yana sane ya take yabi son zuciyansa amma dai ai sunsan ba kyau nema cikin neman aure .
Nace "wai mai martaba umarni ya bashi ba neman izninshi yayi ba.
Ya salman dafe kai yayi da sauri sakamakon jinda yayi kansa ya Sara ya runtse ido.