← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 128

Sashe 69

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri ya dagani a rikice gabansa ne yayi mummunan faduwa ganin yadda siket dina yayi stain din jini!!!!!!!

_Masoyan_ _Rumaisa_ _salman_ _ku_ _kara_ _hakuri_ _don_ _Allah_ _akan_ _irin_ _matsalolinda_ _Rumaisa_ ke _fuskanta_ _amma_ _inshaa_ _Allah_ _komai_ _zai_ _daidaita_ 🤗🤗🤗🤗

Hauly ce👍🏻🥰
[9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡63

**************Ba bata lokaci ya kaini asibity dake cikin barrack din.

Wnn karon ma cikin ba rabon mu bane snn a wnn karon nasan zafin miscarriage don nasha azaba sosai yayin wanke ciki ya salman tausaya min sosai da ana karbawa mutum ciwo da ya karba min .

Gashi nayi ta bleading har saida aka debi jininsa aka kara min.

Saida yaga na fara samun lfy snn ya buga ya gayawa Mamana.

A ranar adda A'i ta zo ta dubani wai taje gidanmu bama nan shine ta tambayi neighbors sukace muna asibity.

Har tambayar ya Salman takeyi wai mai yake janyo min bari?
Shiru yayi ya rasa wani amsa zai bata

Tace " amma in an sallameku ya kamata ta koma gida domin ta sami jinya mai kyau in yaso sai ta dawo .

Yace " eh zata koma.

Tace " to Allah ya bata lfy ni zan tafi .

Yace "amin
Nima nace " na gode adda a gaida mutan gida.

Ya salman ya rakata ya danjima kan ya dawo .

Ya kalleni cikin kulawa yace " baby ya kamata ki tashi kici wani abu lokacin shan maganinki yayi kan doctor yazo ya sallameki.

Nace " to yaya

Ya riko hannuna snn ya dagani na zauna mai kyau yace " sannu Allah ya baki lfy.

Hawayene ya zubo min nace " amin .

Jikinsa a mace yace " kiyi hkr baby ina iya kokarina wurin kiyaye bacin ranki tunda wnn shaidaniyar matar ta fara matsa min wlh ko kadan banida wata alaka da ita hasalima a dalilinta na bar Lagos na koma kano tun kan muyi aure ba na son ta na tsaneta amma taki ta fahimceni bansan wani irin zuciyane da ita ba.

Na goge hawaye dake zubo min nace " yaya rayuwa tayi min kunci bansan ina zan sa raina inji dadi ba yaya a tunani na idan munyi aure dukkan matsalolina ya kare amma sai gashi matsalolin sai kara yawa yake bansan ya zan yi da raina ba .

Rumgumeni yayi a jikinsa yace " baby karkisa damuwa a ranki komai zai wuce insha Allah ke kadaice matar da nake so kuma zanci gaba da so har karshen rayuwata ba Wanda zai rabamu kuma insha Allah zansan yadda zan yi in sanyaki farinciki da nutsuwa babyna.batun khabirat ki cireta a ranki zan dauki mataki na karshe a kanta don bazan kuma barinta.

Haka yaci gaba da lallabani har sai da yaga na daina kuka snn ya saka min abinci a plet ya zauna gefena yace " yanzu kici abinci kisha magani zan miki wani albishir da zai faranta miki rai.

Haka ya dinga bani a baki har saida na koshi ya bani magani nasha yayi murmushi yace " Alhamdulillah kar ki so kiga yadda naji dadi da kk ci abinci baby.

Nace " yaya kaima kaci.
Yace " zanci amma kamin nan albishirinki?

Nace " goro fari Sol.

Yace " yawwa hankalinki ya kwanta yanzu kam Goggo Amina sun maida aurensu da daddy.....

Da sauri na mike daga kishigidar da nayi fuskata daukeda fara'a nace " really! Wayyo Allah na gode maka kai yaya wnn albishir din yayi min dadi sosai.

Rumgumeshi nayi ina dariya shima murmushi yakeyi yace " sai muyi musu fatan Allah ya basu zaman lfy da zuria ta gari.

Dagowa nayi na kalleshi nace " yaya kana nufin Mamana zata iya haihuwa yanzu?

Ya gyada kai yace " sosai ma ai bata wuce haihuwa ba ki shirya samun kanne.

Dariya nayi nace " kai yaya. To Allah yasa.wlh naji dadi sosai

Yace " masha Allah Allah ya kara miki lfy ina son ranar Friday mu tafi kano insha Allah.

Nace "to Allah ya kaimu

A ranar aka sallamoni muka dawo gida ya barni a daki ina dan gyare gyare Ashe gidan hassan ya tafi .

Tunda hassan ya ganshi haka yasan ba lfy ba don yayi yayi dashi ya zauna ma yaki

Yace " suleyman nasan maganar khabirat ne ko........

Ya tari numfashinsa da fadin " tunda Allah yasa ka gane meke tafe dani fine ! Hassan ina so ka gargadi khabirat ta fita daga rayuwata ta daina zuwa gida na idan kuma ka sake baka dauki mataki ba ni zan dauki mataki da kaina kuma bazai muku dadi ba dukanku!!!

Yana gama fadan haka ya fita hassan ya bishi a baya yana kara bashi hkr amma ko sauraronsa baiyi ba.

Don haka hassan yana komawa gida ya kira khabirat da matarsa silfa nan ya shiga fada yana jawa khabirat kunne akan ta fita harkar ya salman .

Amma sai cewa tayi " yaya ni wlh ba wani abu bane sonshi nake kuma har in zai amince aurensa zan yi don Allah yaya ka taimaka min ka rokeshi ya aureni wlh bazan taba iya rabuwa da suleyman ba.

Hassan yace " khabirat rabuwa da suleyman ya zama dole domin.suleyman bazai taba auranki ba don haka ki sawa zuciyarki hkr ki auri Wanda yake sonki

Girgiza kai tayi tace " yaya bazaka gane bane rabuwa da suleyman mawuyacin abu ne a.........

Ransa a bace yace" ni dai na fada miki ki rabu dashi idan kinki kuma duk abinda ya miki karkice ban gaya miki ba.

Daga nan ya tafi dakinsa khabirat kuka ta fara yi tana " aunty Silfa wlh ina son Suleyman bazan iya barinshi ba.

Silfa tace " to khabirat ni bansan ma me zance miki ba .

Ta kara fashewa da kuka tana " O my God suleyman why why why me yasa bazaka soni ba ?

Khabirat ta zama tamkar mahaukaciya sai sambatu take silfa na bata hkr a karshe cewa tayi wlh sai tayi komai ma domin taga ta mallake zuciyar salman ya zama nata ita daya.

Koda ya dawo gida ya sameni ina kwance yanayinda na ganshi na fahimci ransa a bace yake nan na fara tambayarsa me ya faru.

Bai kulani ba ya wuce toilet.

Kamar yadda ya fada kuwa ranar Friday muka shirya abokinsa David ya kaimu airport wai sai gamu a kano dama na yiwa mama waya nace sa,a da zainab ta basu mukullin gidana suje su share su goge koina.

Gida muka fara zuwa palon kawu muka gaisheshi cike da fara,a ya amsa hadi da yi mana jajen rashin lfyta.

Maman sakina ta kawo mana ruwa mai sanyi muka sha itama muka gaisheta snn muka tafi dakin inna suna Palo da Sadiya sai Abdul dake ta kiriniya.

Nayi mamakin ganin yadda inna ta tarbemu da fara,a muka gaisa har tasa Sadiya ta kawo mana tuwo .

Ta kawo ta ajiye inna ta ce " to saka musu man bakiga sun kwaso gajia ba.

Tasa mana tuwon masara mai laushi da miyar busashen kubewa yaji kifi da wake ga man shanu .gefe kuma furace aka damata da kyau a kwano tasha sugar Sadiya tasa mana a Kofi.

Ya salman tuni ya wanke hannu ya fara ci cikin jin dadin girkin har yace " innah nayi kewar girkinki wlh .

Murmushi tayi tace " ai shiyasa na shiga kitchen da kaina na dafa maku da yake nasan itama Rumaisa 'yar gargajiyace.

Ya salman yace " tashin kauye kuma lol!

Ya fada yayinda ya kalleni yana dariya hade rai nayi don yasan banson ace min tashin kauye.

Inna tace " Rumaisa ya kk zaune bakici ?

Sunkuyar da kai nayi nace " zancine innah.

Tashi tayi tace " keda baki sabawa da mutane wnn kunyar taki har yaushe?

Ta shige daki anan ne na fara ci ya salman kam har ya kusa cinyewa ya dora Abdul a kafarsa yana ci yana bashi. Gaskia ya salman na son yara sosai.

Sai lokacin ya kalli Sadiya yace " ke zoki kara ma Rumaisa abinci wnn mun cinye da Abdul.

Kamin ta tashi nace " aa ki bari wnn ma zaiyi nafi son insha furan nan da yawa.

Sadiya tana zaune tana kallonmu sai zumbure zumburen baki takeyi kallonta yayi yace " wai lfy nazo na sameki anan?ko kin sake halin ne?

Tace " aa fa yaya nazo ne in gaida inna

Ya kalli agogo yace " to gashi magriba ya kusa uban me kk jira da bazaki koma gidanki ba?

Tace " yaya dama jiran isowarku nake dama ina so.......

Katseta yayi " ki tashi ki dauki yaron nan ku tafi koma me kk so ki hkr sai gobe kizo ki sameni tunda ke ba,a rabaki da matsala kullum.

Tashi tayi tace " Abdul zo kasa takalmi mu tafi.

Abdul mannewa ya salman yayi yace " uhm uhm.

Ya salman yace " kinga rabu dashi ki tafi zainab ko sa,a zasu kawoshi.

Sadiya ta fita tana ta faman fushi ko na meye ne oho.

Bayan mun gama ci na tattare gurin ina sharewa ya salman ya fita don zuwa masallaci.

Inna ta fito tana cewa " ai da kin bari zan share.

Nace " na gama ma innah.

Daga nan na sallameta na wuce side din Mamana.

Nayi mamakin ganinta a wnn lokacin tasha ado cikin atamfa Holland purple mai kyau dinkin ya karbeta ta zuba gold dinta tasha kitso da lalle ni dai bayan na idar da Sallah ina kan praymat sai bin mama da kallo nake har da sakin baki .

Bayan ta gama abinda take yi ta zauna bakin gado ta kalleni tace " wnn kallon Rumaisa na mi nene?

Nayi dariya nace " mama wlh naga kinyi kyau ne sosai kamar wata budurwa ..

Na tashi yayinda na cire hijabi na dawo gefenta na zauna ina murmushi nace "mama yaya Salman ya gaya min labari mai dadi bakiga yadda nayi murna ba mama Allah ya sanya alhairi .

Tace" Amin.

Nace " mama yaushe zaki tare?
Chapter 69 · 0% Book details