← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 128

Sashe 2

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya mike ya karaso gabana ya zuba min manyan idanunsa da sukayi jazir Dan bala'i yace " sai yanzu na fahimce ki rumaisa wato saboda Ahmad tsohon saurayinki ne shine kk son dansa ya auri 'yarki ko?
Kai tsaye nace eh hakane sai me?kasancewar Mahaifiyar Farouq din Salima tsohuwar budurwarkane don haka me a ciki?

Na juya zan tafi ya fincikoni da iya kacin karfinsa wani irin kykkyawan riko ya min.

Sai faman kwatar kaina nakeyi na kasa.

Murmushin mugunta yayi yace "yanzun kin fahimci banbanci dake tsakanina dake?

Ya sassauta min rikon yace ni ne nakeda ikon aurad da fareeda ga duk Wanda naso bake ba don na fiki karfi a wajanta.ke kanki a karkashin ikona kk don haka bakida ikon zartar da komi a gidan nan.

Hawayene ya ya ciko idona fal har ya fara saukowa don takaici.

Yana kallona yace kina da wani abu da zakice kuma?

Na girgiza mishi kai.

Ya sakeni hade da fadin good girl haka nake so.

Fita nayi na tafi daki kuka na kama yi kamar raina zai fita

Karar wayata ce na jiyo a kan bedside drawer ban kula ba har ya tsinke.

A Jere aka kira sau uku ana hudun na lalubo wayar ban lura da kowaye ba nayi answering.

Muryana a sarke nace Salamu alaikum.

Muryar Inna na jiyo tana " to uwar makirai annamimiya ba sallamarki na ke bukata ba ki fada min me yasa kk ce Salman ya dawo da Nafisa kano alhalin jiya jiya aka kai ta Abuja ?

Cikin muryar kuka nace inna banine nace ya dawo da ita ba nima jiya mukayi sallama akan sai bayan sati daya zaizo kano kawai sai gasu sun yo sammako.....

Ta katse ni.da fadin don Allah rufe min baki da zancen wofi .Wai kawai ganinsu kk yi makarciyar banza to bari kiji na gaya miki idan kk kuskura ko ciwon kai Nafisa tayi sai kin gane kurenki wlh .don haka ki kiyaye don hakane na kira ki.Sannan abu na biyu ga 'yarku nan taxo ta fada min komi.wato bazaku mata aure ba sai ta yi karatu.to me karatun zai tsinana mata? Ke kanki lokacin da uwarki ta nace sai kinyi jamia ina karshenta a karuwanci da shaye shaye kk kare ko an gaya miki na manta ne.to wlh bari kiji ahir dinki daga ke har Salman Ku kiyayi fushina.

Ka min nayi magana tuni ta kashe wayar.

Tirkashi!

Wai ni yau da wanne zanji ne?
[05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: _🌹RUMAISA SALMAN_🌹

👨🏻‍🚒 ```MATAR``` ~```SOJA```~ 👨🏻‍🚒

(_Labarine da ya kunshi soyayya,tausayi, fadakarwa,Ilmantarwa da kuma Nishadantarwa_)

Story and written
By
Maman khausar✍🏻

( *INTELLIGENT WRITErs ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**
[ ```~BISMILLAHIRRAHMANI RAHEEM!~```

➡page 2

🌹 _LABARINA_ 🌹

Rumaisa Ibarahim sunana knn.

Na taso a kauyen.Gano Jahar kano mahaifiyata sunanta Amina.

Na tasone cikin kulawa da samun kyakkyawar tarbiyya daga mahaifiyata.idan ka ganni bazaka ce a kauye nake ba saboda yadda Mamana take kula da suturata tun ina karama .kasancewar ta mace mai zafin nema na tashi naga tana sana,a sosai kusan duk abinda ake so a kauyenmu tana kawowa har irin kayan sawa na gwanjo ,takalmi,su 'yan kunne ba irin kayanda bata sayarwa na amfanin yau da kullum.

Ta na shiga birnin kano sati sati don haka ko wani zuwa sai ta saya min kaya masu kyau irin na 'yan birni.

Ta sakani a makaranta da islamiyya. Allo kuwa tun ina primary na sauke.

Ya zamanto a kauyen duk inda na shiga bina ake da kallo wasu na shan,awata wasu ko bakin ciki sukeyi dani.

Tun ina karama wasu lokuta na kanga mama na tana kebe kanta a daki tayita kuka in na tambayeta tace min kanta ke ciwo.

Har yanzu da na girma shekarata goma sha shidda ina SS2.

Watarana mun taso daga makaranta ina ta sauri in dawo gida don mkrntan akwai nisa da gida

Jinayi ana kiran sunana a na juya da sauri don inga waye sai naga ashe Bello ne makwaftanmu ya nace min kullum sai ya aika a kirani gashi mama tace kada in kuskura koda wasa in saurari wani a kauyen nan bataso

Ina cikin wnn tunani ya karaso yana murmushi yace har kun taso ne?

Fuskata ba fara,a nace eh mun taso.

Yace Rumaisa baki ga sakona bane?

Nace na gani mn.

Yace amma baki ce komi ba.

Shiru nayi sannan nace nifa mama ta hanani kula kowa tace karatu zan yi kuma sai na gama Jami,a

Dariya yayi sannan yace jamia a kauyen nan ne har zaki yi jamia?kinga rumaisa bari in gaya miki gaskia aure shine ya kamaceki yanzu ba wani book tunda Allah yasa kin sauke Qur'ani.ki amince in rufa miki asiri in aureki ba sai an tsaya tone tone.watakila shine mamanki take tsoro yasa tace makaranta zakiyi.ni ba ruwana da Asalinki haka nake son ki.

Jikina ya mutu tunda ya fara maganan domin gaskia ni bansan waye BABANA ba .wani bai taba zuwa wai dangin Babana ba.kai harma mama ban San kowa NATA ba.

Hawayene ya zubo min da Na tuna kusan kullum Na kan ga mama a damuwa in ta kebe ita daya.

Gaba daya Na manta da wani bello da sauri Na barshi a gurin yana ta kwalan kira nayi banza dashi.

Tfy sauri sauri nake har na isa gida ina haki mama tana ganina tace ke lfy Na ganki haka ? Waya koroki?

Na girgiza kai nace babu Na shige ciki Na kwanta .

Shiru shiru tags ban fito Na nemi abinci ba ta shigo ta zauna kusa dani tace Rumaisa me Nene yake damunki ne kin shigo cikin yanayin damuwa ko abinci baki nema ba.
Na girgiza kai nace" bab.......

Ta katseni da sauri ta ce akwai abinda kk boye min.rumaisa bakida kowa a garin nan sai ni don haka dole ne ki fada min damuwarki.

Na mike na zauna snn na kalleta nace mama tambaya zan miki zaki ban amsa ?

Ta ce in har na Sani me zai hana na baki amsa.

Nayi ajiyar zuciya nace "mama WAYE MAHAIFINA?

Nan da nan naga fuskarta ta sauya ta mike rai bace tace " uban Wa ya saki kizo ki min wnn tambayar fada min .

Tsoro ya rufeni ganin yadda ta fusata.

Tsawa ta daka min"nace uban Wa yasa ki zo ki min wnn tambayar.

Na kara rikicewa da kyar bakina ya iya fadan bello ne dama yace........

Na fada mata komi

Ta gyada kai tace OK wato har yanzu baki rabu da bello ba ko?ba na fada miki cewa bazakiyi aure ba sai kin gama Jami,a?to bari kiji ko kin gama ma ba a kauyen nan zakiyi aure ba don haka ko da wasa kar na kara jin ko ganinki da bello kai kowa ma indai anan kauyen ne.

Tunda ta fara magana nake ba ta hkr.

Tace tashi ki fita kije ki debi abinci kici.

Ina cin abinci naga ta dauki hijabinta ta yi waje rai bace.

Daga wnn rana na shiga damuwa ba abinda nake son illa in San wacece ni.

Uwa uba kuma gidansu bello yan,uwansa sun Sani a gaba tunda mama taje ta fadawa mahaifiyarsa maganganu akaina.ya kasance duk inda suka ganni sai sun zageni hade da yi min gorin asali.

Na shiga damuwa sosai har ya kasa boyuwa kana ganina ko baka sanni ba kasan ina cikin damuwa.

Bayan na taso daga islamiya don yanzu banda kawaye ma duk sun juyan baya.

Kannen bello suka tareni a hanya zainab da Kulu .

Na kallesu nace yau kuma me ya faru?

Kulu ta harareni tace kudaden da yayanmu ya kashe miki zaki tattara ki bamu.

Cike da mamaki nace wane kudade kuma?ni bello bai taba bani ko sisi ba....

Zainab ta katseni da fadin karya kikeyi shegiya munafuka dole ne kawai ki fito da kudin nan ki bamu ehe!

Kulu ta karba tace "duk karuwancin da akace mamanki takeyi a birni ta dawo da lodi lodin kaya da kudi bai isheku ba sai kin kara dana ya bell......

Raina ya balain baci na kallesu nace gaskia Kulu abinda kuke min ya isheni don kun fara wuce gona da iri .zaku min komi in shanye amma banda naganar zagin mahaifiyata .

Zainab tace an zageta sai me ? Waye ita a garin nan banda karuwa?idan karya muke mata gaya mana waye ubanki?

Kulu ta karba tace tunda muka taso a garin nan bamu taba jin Wanda yace ya sanku ba.......

A fusace na tsinka mata mari.
Nan da nan muka kaure da kokuwa.

Dama hakan suke so don haushina da sukeji .

Nan aka taru a wurin ana rabamu sai zagina suke suna cewa mama na karuwa ce.

Da kuka na bar wurin Allah Allah nake na isa gida don wlh hada kayana zan yi in bar garin nan in shiga duniya Neman asalina.

Horn din mota nakeji tun dazu a kunne na Wanda ya ki karewa nan da nan na birkice na rasa ina zan yi.

Kawai na tsaya cak! Idona rufe ina sauraren ta inda motar zai kwasheni.

Sabanin hakan sai na ji takun mutum ya na zuwa inda nake kamshin turarene mai dadi ya daki hancina da sauri na bude idona

Rass! Naji zuciyata ya tsinke da ganin Wanda ke gabana.

Wayyo wani saurayi ne sai kun ganshi in tsaya kwatancen kyaunshi bata lokaci ne. Kawai dai ya hadu ga kwarjini.

Sai dai na lura kamar ransa a bace yake don wani irin kallo yake min kaman zai dauke fuskata da mari.

Sai lokacin na gane a tsakiyar hanya wucewar mota nake ta tafiya gashi sun ta min hon amma ko a jikina don ma mota basu cika shiga layin sosai ba ko adaidata sai da su sauke ka can babban hanya basa shiga saboda gargada da yashi.

Shine ya sauko ransa a bace.

"Wnn wane irin rashin hankaline haka?

Ya fada a fusace.yaci gaba da fadin

"Yar kauyen kawai don Allah tashi a hanya zamu wuce.
Chapter 2 · 0% Book details