← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 105 OF 128

Sashe 105

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

munir ya danyi murmushi yace"kannena ku tashi mu tafi sashina mu barsu suyi hirarsu anjima se mu dawo .

Ya tashi farida tuni ta shige gaba ta jera dashi tana cewa "ya munir nima in na gama secondary nan london zanzo karatu garin naku ya birgeni.

munir yana kallonta yace"really .

daga masa gira tayi hade da fadin"yeah.
Ya gyada kai yana murmushi yace"Allah ya kaimu lokacin.

Munir ya yi hira da kannensa sosai hade da tambayarsu labarin makaranta suna amsa masa.ranar kwana sukayi hira har gari ya waye.

Gaskia munir ya rikice akan farida sosai sai yanxu ya gane da can ma sonta yake ashe don ya dauka shakuwace kawai irin na yanuwantaka amma yanxu ya fahimci soyayya ce me karfi.

Haka nan faiza ta karance shi tsaf don haka ta gayawa rais suka kirashi suka tambayeshi don baya boye musu komai anan ya tabbatar musu yana son farida.ba karamin dadi faiza taji ba don haka ta sami ya salim ta gaya masa amma abin mamaki sam bai damu ba don cewa yayi ta bar maganar nan kawai jikin faiza ya mutu sosai ta gayawa ra'is shima ya tambayi salim din meyasa yace sudai bar zancan don haka sukayi shiru ba tareda sanin dalilinsa ba.

Munir kam ya gama rikicewa akan farida abin har ya wuce misali don gani yake in sun koma Nigeria kamar za,a kwace masa ita don haka ya fara tunanin furta mata.amma ya salim ya hanashi yace farida na makaranta kar ya raba mata hankalinta biyu.

Haka suka karasa hutunsu suka dawo Nigeria kano suka fara isa ranar na wuni ina musu girke girke na musamman.

Ya salman kuwa ya tura aka kwashesu a airport.a lokacin Abdulwahab dan sadiya ma yazo muna tattauna batun mahaifinsa da mamansu dashi don ya damu sosai yana son mahaifiyarsa ta koma gidansu.a inda ya salman yake ce mishi tunda yanxu ya girma shi ya kamata yasan yanda zai daidaita tsakanin mahaifinsa da mahaifiyarsa.

Muna cikin tattaunawa dashine yan London suka iso don haka gida ya kaure da murna tuni farida ta tafi ta rumgume mahaifinta tana"daddy nayi missing dinka sosai wlh.daddy ya munir ya gaisheka sosai.muje ciki na baka labarin hutunmu .

ta rike hannunshi wai su tafi sashinsa murmushi yayi yace"ai karki damu mamana anjima zan kiraki muyi hira sosai kinji?

Ya fada hade da shafa kanta tace daddy maganace mai tsawon gaske in muka bari se anjima kwana zamuyi muna hira.

yace"to fakice babbar maganace kike tafe da shi mamana?

ta daga masa kai hade da rike masa hannu tana jansa su tafi har tana ce mishi daddy na maka tsaraba mai yawan gaske sai ka gani muje daddy ciki in baka labarin london da saudi.

Harararta nayi nace wai ke farida yaushe zakiyi hankali ne?kina gani ko gaisawa dasu daddynki baiyi ba zakice ku tafi ? Kuma wnn ba yayanki Abdul bane tun shigowarku yana nan duk yaran nan sun gaisheshe amma banda ke.

Sai lokacin ta kai kallonta ga Abdul wanda shima tun shigowarsu yake ta binta da kallo duk inda tayi.

fuska a daure tace"ya Abdul yi hkr ban ganka bane ya kk ya aiki?

Cikeda fara,a Abdul ya amsa mata gaisuwan.

Ganin magriba yayi yasa gabadaya muka watse su yaya suka tafi masallaci mu kuma muka wuce dakina da ruma sai farida da mimi suma suka wuce dakinsu.bayan sallar ishane mukayi dinner anan muka shiga hira har sai sha biyu kowa ya tafi makwancinsa farida kam taso tayi hira sosai da babanta amma sam naki bata fuska.saida sukayi bacci gabadaya muka shiga hira da ruma ya salman kuwa jin shiru yasa turo min text wai inzo ya gaji da jira.don haka nay maza na kintsa ruma na cewa "kina tfy nima zan lallaba in tafi gun...

dariya nayi nace"kije kawai amma asuban fari ki dawo .

Tare muka fita ita ta tafi sashin baki ni kuma na wuce oda room inda na sameshi ya gaji da jira ina karasawa na fara bashi hkr cikin kwantar da murya nace "am sorry yaya wlh na dauka ko zaka hkr na yau dinnan....

Wani irin kallo ya min wanda ya sani yin shiru da wuri ina murmushi hade da toshe bakina.

A hankali na tafi na kwanto jikinsa nace"wlh yaya na gaji sosai yau massage nake bukata .

gyara min kwanciya yayi snn yace"kwanan nan kina wahalar dani sosai baby me yasa ne ? Ko kin manta irin mijin da Allah ya bakine ?

shiru nayi ina murmushi yace"ko kina bukatar in kawo miki kanwa ne mai tayaki hidima ....

Nan da nan na canza fuska na yunkuro zan tashi da sauri ya maidani ya kwantar yana dariya yace" kwanta da wasa nake miki dear.

ya fada yana dariya duk da hakan na kasa sakin raina.

nayi.don haka ya rumgumeni a jikinsa yayinda ya kai bakinsa saitin kunnena yace" ke kadai ce a zuciyata babynah ba wata.kin ishe ni komai a rayuwa bana bukatar wata don haka ki dada kwantar da hankalinki ni salman nakine ke kadai rumaisa.

Murmushi nayi na kara shigewa jikinsa na kwantar da kaina kan kirjinsa nace"yaya ina jin dadi sosai a duk lokacinda kake gaya min irin wnn maganar Allah ya barmu tare.

Yace "ameen babynah.
Murmushi nayi nace"yaya gaskia ni yanzu na girma a daina kirana da baby kaga fa akwai lokacin da ka manta ka kirani baby a gaban farida dariya ta dinga mana.

Murmushi yayi ya manna min kiss a baki yace"shareta kawai ni babyn nan bazan iya barin kiranki da shi ba.

Anan ya kashe wutan dakin ya jawo mana bargo daga nan topic ya canza.gaskia ya salman daban ne a cikin maza ya iya gwadawa mace soyayya gaba daya rikitani yake har in manta a wace duniya nike gabadaya.

Washe gari kasancewaar ranar asabar ne gabadaya muka tafi gidan mama mun sami ruky da imran (twins din mama)sunzo jiya .

Ya salman ya kalli ruky hade da fadin"ke kuma ya isheki ja mana rai haka kawai ki amsa a wuce wurin.

Ya salim yace"Wai a dole ita jan aji take mana mummuna ma irinki

Dariya tayi ta kalli mama tace"mama kinajinsu ko ya hakim yaje ya hadani dasu.

Mama tace"to ai gaskiane rukayya tun yaushe hakim ke binki da kin amsa tuni anyi auren nan amma kinki kice komai .

Tace"mama ni wlh ya hakim ya min tsufa da yawa .

Da sauri nace"amma bakida mutunci ruky yanxu hakim dinne zaki wani cewa ya miki tsufa?

Imran yace "ai gaskiane aunty ihsan gara dai ya nemi daidainsa.

Harararsa nayi nace"to waya sako bakinka wai kai mai yaruwa koh?

Na kalli ruky nace"ke kuma wlh zan fadawa daddy don gaskia ba za mu zuba miki ido kina abinda ranki yakeso ba.

Ya salman yace"da kin kyauta wlh .tama ci sa,a hakim yace yana sonta mummuna ma irinta.

Ya salim ya karba yace"ai nima na rasa me hakim ya gani anan.duk familynmu itace mummuna.

Turo baki tayi tace"mama kina dai jin su yaya abinda suke fadi koh?

Mama ta tabe baki tace"kun fi kusa ai rukayya.

Ruma tace"gaskia ya isa haka ku daina zagin kanwata.

Ta rike hannun ruky tace,zo muje ciki kanwata ki fada min mece ce matsalarki.

Daga gidan mama sai muka tafi gidansu innah.farida wani tsalle ta daka ta fada jikin innah ba shiri inna ta sakar mata dundu a baya tace"jaira so kk ki kasheni?

Farida tayi dariya tace"tsohuwa me ran karfe kina nan abinki.wlh ni duk tunanina kafin mu dawo hutu zamu dawo mu samu kin tafi.

Inna tace"uwarki ce zata tafi ni kam ina nan sai na goya yaranki.

Farida ta daure fuska tace"kinga matsalata dake ko.na gaya miki wasa wasa banda maganar zagi bana so ki daina sako uwata a cikin zancenki.

Inna tace"to yi hkr naga nan da nan har kinyi fushi .
Farida tace"nayi fushi sosaima yanxu kawai ki tashi ki mana dan wake muci snn in huce.

Innah tace"an gama shatu ai dole kawai in tashi da kaina in muku danwaken nan.

Innah tana kokarin mikewa nace"innah don Allah ki rabu da ita in zasu ci danwake suje su fadawa hajara tayi musu.

Ruma tace"gaskia kam inna kar ki biyewa farida .

Inna tace"karku damu sam da kaina zan mata.inaji da mai sunana dinnan sosai.

Murmushi mukayi nida ruma inna kam fita tayi farida da mimi suka bita a baya saura ni da ruma da sadiya don su ya salman da yara mazan nan suna sashin abba muka barsu.

Na kalli farida nace"sadiya meye labari ne? Jiya Abdul ya kai mana ziyara.

Ta danyi murmushi tace"wlh rumaisa ba wani labari yanxu Abdul din nake jira .

Nace"to Allah ya doraki a kan mahaifin nasu .

Tace"amin.

Mun dade a gidan sosai muna ta hira da sadiya kamar ba ita ba ikon Allah knn.

Da yamma muka raka mutanen Abuja airport suka tafi.

Munir kuwa a can london tunda su farida suka dawo hankalinsa yaki kwanciya gani yake za,a kwace masa ita don haka ya fadawa goggonsa faiza tace shifa kawai zai gayawa farida sonta yake don kar ya tsaya garin kallon ruwa kwado ya masa kafa.
Itama faiza ta bashi goyan baya amma tace ya bari sai ta tuntunbi ya salman .

Aikuwa ba bata lokaci ta fadawa ya salman komai amma tace masa ya salim yaki amincewa bata boye masa ba.

Gaskia ya salman yayi murna sosai saidai ya rasa dalilin da yasa ya salim yaki amincewa don haka yayi niyyan zuwa Abuja domin suyi maganar.......

Hauly ce🥰🙏🏻
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡92

*************Ya salman a cikin satin ya shiga Abuja suka zauna tattauna maganar farida da ya Salim.

Ya salim yace"dama nasan fa,iza bazata bar wnn maganar ba sai ta fada ma.amma ina son ka kwantar da hankalin ka kar ka fassara maganar da wata manufa.

Ya salman yace masa nifa ba wnn ya kawoni ba har yanxu baka gaya min dalilinda yasa baka so mu hada yaran nan auren zumunci ba.
Chapter 105 · 0% Book details