← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 128

Sashe 92

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba yanda salman baiyi da inna ba amma sam taki yarda ta fito su gaisa da salmah don haka ya hkr ya fita.kawai yace salmah su tafi gida.

Tundaga ranar innah ta daina sa mana ido ta shafawa kanta lfy .ni kuwa koda taji labarin cikina ba karamin farinciki tayi ba don haka ba,a kwana biyu bata kira taji lfyta ba.tun ina danjin tsoron me zai biyo baya har na saba yanxu .

Salmah kam shiru ba labarin ciki don haka ta shiga nuna damuwarta da kishinta a fili ganin yadda ya salman ke kula dani duk da ba gidan nake ba .

Bangaren sadiya kuwa sam batayi murnar samin cikina ba daga ita har adda A'i domin su da so samune ya salman ya rabu dani ya auri daya daga cikin 'yanuwansu na kamaru.

Yanxu adda A'i da sadiya su biyu suka rage bakinsu daya innah kam tuni ta rabu da harkarmu .

Amma sadiya bata nuna min a fuska ba don tana zuwa ta dubani har ta wuni ma a gidanmu .yau da gobe har na saki jiki da ita in tazo musha hira da dariya .

Cikina na wata hudu na fara samun saukin laulayi yanxu sai dai kwadayi komai mama ta dafa baya burgeni .

Don haka sai incewa sa,a ta dafo min dambu ta kawo min wani lokacin kuma ince rogo da kuli har da su awara duk abinda bai dameni ci ba da yanzu sune abincina.

Ranar sadiya da kanta ta dafo dambu ta kawo min don sa,a bata da isashen lokaci sosai suna exams .

Naji dadi sosai nace lami ta dauko min plet .

Tana kawo min nayi serving har na diba a spoon zan kai baki sai naji wani irin tashin zuciya ..............

Hauly ce👍🏻🥰
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡83

***********Salmah ta fara tunanin bin shawaran kawayanta don haka ta yanke hukuncin bin malamai .amma wani abun takaici duk abinda tayi baya cinmu gabadaya abin ya daure mata kai gashi ta kashe kudadenta duka har ta koma sayarda gwala gwalanta amma shiru babu abinda ya sauya.

Zuwa yanzu na warware tass ba abinda ke damuna na laulayi sai nauyi da cikin ya kara yi kasancewar yanzu ina wata na bakwai
Ban kuma yin sakaci da kaina ba domin kullum cikin yi mana addua nake akan Allah ya tsare mu da sharrin dukkan makiya kuma dama nasan ya salman ma ba baya ba wurin riko da ibada.haka nan na biya kudina akayita mana saukan Al-qurani mai Girma akai akai .to Alhamdulillah komai na tfy normal.

Su sadiya ma sunyi sunyi abin ya faskara domin daga baya lagos din ma ta koma gabadaya saboda suji dadin kullah makirci .tun suna bin malamansu na nan arewa da kamaru har suka koma bin bokayen kudu mushrikai masu tsafi sunta kashe kudi amma a banza don haka kawai suka zubawa sarautar Allah ido.

A wnn lokacin Ruma ta haifo babynta katuwa mace karkuso kuga murna a familyn galadima kasancewar haihuwar yara mata ba yawa don haka ruma ta dinga samin kyauta tin randa ta haihu har zuwa ranar suna .

Nima aje suna inda baby taci suna ummul khairi anyiwa Goggo ummi takwara .fa,iza ma tazo mutanen london yanzu yaranta uku sakina kuwa hudu .sun sakoni a gaba da zolaya nidai ban kulasu ba ina ta kaina don sai kunga yadda cikina ya girma a lokacin wata takwas kai dama haka masu ciki ke fama bacci ma da kyar nake samu nayi.ga babyn cikina sai motsi yake sosai musamman da daddare.

ya salman kuwa tausaya min yake sosai ganin yadda nake fama tashi da kyar zama da kyar in dai yazo gidan mama ya dinga dawainiya dani knn duk nauyina dinnan haka yake kimkimata ya kaini toilet don yanxu shine mai min wanka lol! Jiransa nakeyi se yazo .

kwanana uku a Abuja na dawo kano ya salman duk ya bi ya damu da bana nan din sai waya yake ta min akan na kula da kaina.gaskia ina samun kulawa kota ina sai sambarka.

Nima cikina na cika wata tara da sati daya na soma nakuda bazan manta ba ranar ya salman yazo muna tare a daki muna dan hira kawai sai na fara jin marata da bayana ya fara ciwo kadan kadan ya lafa .haka na dinga cijewa don kar ya salman ya daga hankalinsa .

har karfe tara dare ya sallameni ya tafi .aikuwa tfyrsa keda wuya na fara jin zafin na karuwa nan da nan na gayawa mama aikuwa ba bata lokaci ta tattaro min kayana muka tafi asibity muna zuwa suka karbeni suka duba kawai wai na kusa ga kan baby.zaro ido nayi a tsorace duk da wani wahala nasha sosai ba.

don haka ko minti ashirin bamuyi da isa asibity na haifo babyna katuwa son kowa kin wanda ya rasa gashi ban.wani sha wahala ba sam.

nan aka kintsa mu aka nade baby cikin kayan sanyi overall pink da hula sai kun ganta katuwa jazir tubarkallah masha Allah duk da ba a cika gane kamannin jaririya ba amma kuna ganita sak!ya salman har da gashin kanta ikon Allah knn.

mama kam murna kamar tayi yaya da ranta sai shiga da fita takeyi ta rasa wa zata fara kira tsakanin ya salman da daddyna.tsabar farinciki .

murmushi nayi nace"mama ki gayawa yayana don Allah

tace"gaskia kam ya kamata bari na kirawoshi in mishi albishir in yaso se in kira daddyn ku.

ta fadi hakan tana murmushi yayinda ta lalubo layin ya salman ta kirashi ringing biyu yayi ya daga hade da fadin"goggo lfy dai kam ?

Tayi dariya tace"lfy lau salman yau Allah ya amshi adduarmu rumaisa ta sauka lfy ta samu diya mace yau kaima ka zama uba salman sai mu gode Allah.

Allahu Akbar" abinda bakinsa ya fara fada cike da farin ciki mara misaltuwa ta ce"goggo Amina ina fatan dai ba wata matsala daga rumaisa har babyn?

mama tace"lfy lau wlh babu komai rumaisa gats zaune tana shan tea baby kuwa tana gadonta ......

Yayi wani irin ajiyar zuciya hade da fadin Alhamdulillah Allah abin godiya goggo Amina ina zuwa yanzu don bazan iya bari gari sai ya waye ba.....

Mama tace" haba salman sha biyu fa ta kusa ka hkr mana sai da sa......

tuni ya katse kiran dariya nayi nace"mama yaya wai sai yazo ko?

Mama tace"ai bazai iya hkr ba .yanxu bari na kira daddyn ku kuma.

Nan mama ta kira daddy ta sanar dashi shima nan da nan ya warsake daga bacci ya fara tambayar lfy ta tukun mama tace Qalau nake yace "to amaryartawa fa?

mama ta dan tabe baki tace"gata can kan gadonta tana baccin ragwanci.

daddy yayi dariya yace"kodai baccin gajia wato kin fara kishi tun yanxu ko ?

Mama tace"me abun kishi a wurin wnn 'yar mitsisiya.

dariya sukayi daddy yace"masha Allah Allah mun gode maka Allah ya raya mana ita bisa sunnah ya Albarkaci rayuwarta tare da dukkan yaran musulmai.
Mama tace"amin .

yace"insha Allah gobe zanbi flight din safe nazo naga amaryata.

mama tace"Allah ya kaimu rai da lfy a gaida mutan gida.daga nan sukayi sallama.

Ta sake kiran Abbansu ya Salman ta fada masa shima sosai ya dinga farin ciki hade da kyawawan adduoi.daga nan mama tace shikenan sauran mutane sai da safe ta fada musu.

Ya salman kuwa yana katse kiran mama tashi yayi ya wuce toilet alwala yayi ya fito ya zira jallabiyarsa ya shimfida pray mat ya fara jera nafila na godiya ga Allah da ya bashi wnn babbar kyauta da kudi baya saya .

Bayan ya idar yayi adduoinsa ya tashi ya dauki wayoyinsa ya dura aljihu da makullin motarsa .

Snn ya kalli salmah dake ta sharar bacci har da minshari lol

Ya karaso a hankali yafara tashinta da kyar ta iya bude idonta ta kalleshi ganinshi cikin yasa ta fadin "honey in kuma zakaje cikin daren nan?

Murmushi ya sakar mata yace"asibty zanje rumaisah ta haihu....

Ba shiri ta mike zaune kirjinta sai bugawa yake tace"cikin daren nan?

Yace"dama haihuwa yana da takamaiman lokacinsa ne......

Tace"a....ina nufin....ince cikin daren nan zaka tafi bazaka bari da safe ba?

Binta yayi da wani irin kallo yayinda ta kuma cewa "honey kasan fa anguwan nan ba lfy kwanaki da baka nan 'yan fashi sunyi ta shigowa anguwan suna barna sai da ka dawo abin ya lafa snn yanzu kace zaka fita kai kadai cikin wnn daren ?

Murmushi yayi hade da fadin karki damu babu abinda zai sameni .sai na dawo ki tashi ki rufe kofa.

Ya wuce zai fita da sauri tasha gabansa a shagwabe ta fara magana"honey don Allah kar ka tafi ka barni ni daya tsoron gidan nikeji se dai mu tafi tare.

Yace"to kiyi maza mu tafi karki batan lokaci banda abinki gidan nan fa cike da securities yanzu snn hakim da munir suna nan ga mai aikinki.

Ita dai tuni ta daura zani kan kayan baccinta ta saka hijabi .daga nan fita sukayi zuwa harabar gidan har zasu shiga mota suka jiyo karar harbin bindiga ba shiri salmah tasa ihu ta kamkame ya salman .

Dan tsaki yayi yace"ke ba komai fa don Allah mu tafi .

Jikinta na rawa ta fada motarsa tuni ya shiga yaja motar suka fita.

Lokacinda suka iso ni kuma muna kokarin ba baby nono mama da wata nurse suke nuna min yadda zanyi tab ashe bada nonon ma wani aikine daban.

Su ya salman na shigowa na saki murmushi shima da sauri ya karaso tini na mika masa babynsa karbanta yayi ya rumgume a jikknsa cikeda farin ciki sai dariya yake.

Mama tace"salman sai da kuka zo cikin daren nan .Salmah sannunku da zuwa zauna kan kujeran can.

Salmah da tunda suka iso sai yatsunar fiska take taje ta zauna akan kujeran ta fara gaisheni hade da yi min barka snn ta gaida mama .

Ya salman kam ya manta damu gabadaya babynsa kawai yake karewa kallo hade da daukarta hoto a waya.yana murmushi sai Masha Allah yake ta maimaitawa.
Chapter 92 · 0% Book details