← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 128

Sashe 4

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nace mama ina tare Zamu tafi ?

Ta girgiza kai tace ni aure zanyi kwanan nan rumaisa.

Cike da mamaki nace" a ina mama?

Tace a birni gara nayi aure kawai da in koma zaman gidan yaya da matarsa.ke kanki naso ace gidan ya kasim wato mahaifin salim aka kaiki don matarsa mutumiyar kirkice amma salman ya fi so ki zauna a gidansu.

Nayi shiru na rasa me zance can nace "mama to ki tafi dani gidanki mn.

Tace baxai yiwu in Dora mishi dawainiyarki ba alhali ba shi ya haifeki ba.

A raina nace to ki kaini gidan Babana mana.

Ta lura da yanayinda na shiga tace" karfa ki dani kanki ke dai ki taka tsan tsan ki zauna da kowa lfy kinji.

Haka ta dinga kwantar min da hankali har bacci ya daukeni.

Sati biyu akai ya salman ya dawo daukana shi kadai na tambayeshi ya salim yace ya koma Abuja.

Dama na shirya kuma na sallami kowa wasu na min fatan alheri wasu ko kallon arziki basuyi min ba.

Haka muka sallami ta rakomu har waje tace "to Salman ga Rumaisa ka kula da ita sosai kar ka sassauta mata idan ta kauce don bana son ka shagwabata ba gata bane.

To,kawai yace yayinda yake sa kayana a mota.

Ta kalleni tace ke kuma kiyi taka tsan tsan da kowa domin birni ba kauye bane ki maida hankali ki nitsu banda rawar kai ki girmama kowa ki mutunta kowa kuma sai kiga kin zauna qalau sannan ki maida hankali wurin karatunki sosai banda wasa.

Nace to mama

Hawaye ya cicciko min ido .

Ya bude min gaban motan na shiga ya rufe .

Ya sallami mama sannan ya zagayo ya shiga ya tashi motar mama ta daga mana ta yi ciki.

Na goge hawaye da ya gangaro min ya kalleni yace" daura belt.

Bansan me yake nufi ba na shiga dube dube.

Bai ce komi ba naga ya Dan kwanto yasa hannu ya jawo igiya ya zagayeni hannunsa na taba jikina naji wani iri.

Ya kalleni yace "sorry belt din zai taimaka miki sosai.

Naga shi ma yaja ya daura daga nan muka fara tfy.

Sanda muka isa gidansu a Gadon kaya rana ta yi sosai.

Ya sami unuwa yayi parking

Sannan ya bude min yace sauko ga gidan nan.

Na kalli gidan da ya nuna mun babban gidane gsky wata ce ta fito daga cikin gida zamuyi sa,a da ita cike da fara,a ta karaso tana min sannu da zuwa.

Ya Salman yace " yawwa sakina zo ki tayata Ku dauki kayan nan ki kaita dakin Inna ta huta.

Rass! Naji zucuyata ta tsinke bansan sanda na tsaya ina kallonshi ba har sakinan ta dauki kayana tana mu tafi banjita.

Ya karaso gabana yace"me ne ne?

Girgiza kai nayi nace ba komi.

Yace OK shiga ciki.

Na dauki ragowar kayana na bi sakina ciki.

Abinka da Dan kauye sai kalle kalle nake ta yi.

Har muka isa gidan a tsakar gida naga wata mata tana wanke shinkafa wata yarinya kuma ba daka tattasai.

Na hangi wata kuma can tana wanki sai wake wake take.

Matar ne data ganmu cike da fara,a tace "sannunku da zuwa lallai kun shawo hanya sakina ki wuce da ita dakin innarku.

Na Dan russuna na gaisheta da fara,a take amsawa har tana tambayana mama.

Wancan da take wankin ta dago a yatsune tace " sannunki da zuwa.

Na amsa sannan na gaisheta ta amsa min a wulakance.

Sannan matar ta kalli wacce take daka tace"zainab baki ga yayarki ba?

Wacce aka kira da zainab ta kalleni cike da fara,a tace sannu da zuwa.ina wuni.

Na amsa mata ina murmushi sannan muka shiga dakin innan da yake ciki da Palo ne mun sami wata kuma kwance akan kujera da kyar ta amsa mana sallama sakina tace mata "raihana kicewa inna ga bakuwa.

Ta dago ta kalleni tace ki zauna mn innan zata fito yanzu ai.

Na zauna sannan na gaisheta.

Sakina kuwa tana ajiye kayana tace ina zuwa rumaisa mama ta aikeni shago.

Na ce " ko in rakakine ?

Tace aa ya salman yace ki huta tukunna.

Ta fita da sauri.

Muna zaune shiru da raihana.

Sai ga wata mata ta fito daga dakin.kyakkyawar mace fara jikinta dai dai batada tsawo sosai ga gashi bakinta baki irin na 'yan kamaru daga gani ma 'yar kamarunce.kamanninta da salman yasa na fahinci itace innar Sam bata tsufa ba har matar wajen nan ta fita girman jiki.

Da sauri na sauko daga kujeran nace"ina wuni.

A wulakance take kallona sannan daga bisan tace lfy sannunki da zuwa.

Na amsa kaina a sunkuye gaba daya na tsorata da irin karbanda yan dakin suka min ni wlh da dakin su sakina ma aka kaini mamarsu tafi fara,a.

Munfi minty talatin zaune ba Wanda yakara cewa komi har mai wankin ta gama ta shigo ta na cewa inna sabulu na ya kare naga wani a leda na dauka na karasa wankin.

Inna tace "ke dai sadiya wlh baki da tattali duk girman sabulun har kin karar? To ba ruwana wancan da kk dauka na salman ne ba ruwana ki tanadi amsa in ya tambayeki don yace in yaron nan mai masa wanki yazo a bashi sabulun.

Raihana ta mike tana cewa tab! Yarinya kin taro aradu sabulun ya salman? Hmmm yau zamu sha kalli a gidan nan.

Sadiya ta harareta tace " ba abinda zaiyi ai wanki nayi kuma sabuluna ne ya kare.Inna ina akwai wani sabulu a karkashin gado Wanda su nenne suka kawo miki da kamaru?

Inna ta harareta tace ba duk kun karar ba ko Maman sakina ma ban basu ba kwaya daya ya rage na bawa salman shine kk dauka.dama ai abu a dakin nan baya dadewa ko man shafawa abbanku ya siyo ya raba sai Ku karar nasu sakina na nan sabulun wanka haka man goge baki ma haka kafin ace me wnn kun karar sannan kuce na fiye korafi kuna dai ganin su sakina a dakinsu yadda suke tattalin kominsu.alhalin ba Yawa muka fisu ba

Sadiya tace wlh inna ba wani tattali suka fimu ba makon tsiya ne dasu.

Inna ta tabe baki tace ai shikenan Ku kuka Sani gashi yanzu mun karu kuma .

Raihana ta ce kai wnn yar kauyen a dakin nan zata sauka?

Inna tace a to ga dai kayanta nan kun gani.

Sadiya tace tab sai dai ta kwanta a kasan kafet wlh

Inna tace oho kunfi ni kusa da ita.

Nikam duk naji ba dadi na kara takurewa wuri daya.

Sakina ta shigo da kulan abinci ta ajiyae tace Inna ga abincin yaya salman.

Inna tace"baya nan ne?

Sakina tace eh abokansa sunzo sun tafi tare .

Sannan ta kalli su sadiya tace kuzo muje waje muci abunci rumaisa zo muje waje.

Da sauri na mike nabi sakina waje ta shimfida taburma an saka abinci a babban tire da miya a roba sai ruwan Leda me sanyi a cikin wani tire.

Sakina ta kalleni da fara,a tace bimillah muci su sadiya kam sai sun gama yanga zasu zo.

Munacin abinci suka fito bayan sun wanko hannu suka karaso sadiya tace sakina da 'yar kauyen nan zamu ci tuwo?Allah ya sawwaka.

Ta wuce kitchen ta dauko plet ta diba gefe har zata sa miya sai ta yatsuna fuska tace hmm miyan duk ta jagwalgwala bari inje in dibi na tukunya.

Ta wuce kitchen.

Raihana ta kalleni tace "ke kar ki kuskura ki taba min gabana don naga baki iya cin tuwo ba kuma ki rage loma da kk yankowa kato sai kace an sakoki daga igiya ko da yake baki saba da jar miya ba.

Nidai bance komi ba sakina ne tace wlh duk abinda kk fada a kunnen ya salman ko Abba

Sadiya dake zaune can tace to munafuka ai sai ki fada din tunda karya aka mata.

Ni dai na har naji gara min kauyen mu.

Don zama da wayan nan sai anyi da gaske!

*Muje*zuwa* !!!!

Hauly ce😍
[05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: _🌹RUMAISA SALMAN_🌹

👨🏻‍🚒 ```MATAR``` ~```SOJA```~ 👨🏻‍🚒

(_Labarine da yA kunshi fadakarwa,Ilmantarwa da kuma Nishadantarwa_)

Story and written
By
Maman khausar✍🏻

( *INTELLIGENT WRITErs ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**
[ ```~BISMILLAHIRRAHMANI RAHEEM!~```

➡page 4

Satina biyu a gidan na fara zuwa makaranta da Islamiyya ajinmu daya da sakina da raihana sadiya na gabanmu don yanzu zata zana ssce

Gaskiya rayuwa bata min dadi a yanzu .a inda nake samun sassauci shine idan na tafi mkrnt ko islamiyya.

Amma in muka dawo gida ko motsi kwakkwara ban isa inyi ba Inna da sadiya sun sakoni gaba sosai.har gara in Abba na gida .gashi ya salman tun randa ya kawoni washe garin yayi tafiya.ni a bakin sakina ma naji tace min ya koma makaranta a Lagos.

Bazan mata wata rana muka wayi gari ana ruwan sama kamar da bakin kwarya.duk muna zazzaune a palon innah su sakina suna dakinsu suma.

Inna ta kalleni tace niko rumaisa ina son in miki wata tambaya tun tuni.

Nace to innah.

Tace ko mamanki ta taba baki labarin mahaifinki?

Na girgiza kai zuciyata ta shiga bugawa.nace bata taba bani ba.

Tace " Hmm Amina knn ai bazata gaya miki ba domin labarine Mara dadin ji rumaisa bakida kykkyawan asali mahaifiyarki ta cuceki ta sameki ta hanyarda bata dace ba.

Na dago da sauri na kalleta .Sadiya ma ta yi farat tace "inna knn rumaisa shegiyace.

Raihana tace hmm kuma shine a rasa inda za,a kawota sai nan don aja mana abun kunya ayita nuna mu.

Sadiya ta kalleni sannan tace ni dai kar ki kuskura ki nunani matsayin 'yar uwarki ehe.

Sunkuyar da kai nayi bansan sands na saka kuka ba .me yasa mama tayi min haka ta sameni ta kaxamar hanya dama wnn shine dalilinda yasa batason in tambayeta waye mahaifina kuma ta na yawan kebe kanta tayita kuka adaki...

Inna ce ta katseni da fadin " ke don Allah bama son kukan munafurci tashi kije ki hura huta maza ki Dora tuwo .
Chapter 4 · 0% Book details