← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 128

Sashe 71

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai gashi nan na sauka lfy na sami ya salman don haka ba bata lokaci muka kamo hanya har mun danyi nitsa yaga ko kulasa banyi ba don haka ya gaji yace " ya kk bar mutanen yola?

Nace " lfy

Ya dan numfasa snn yace " why are you so quite ne yau ?

Tabe baki nayi nace " Kaine naga kamar baka yi murnar dawowata ba.

Yace " hmm Rumaisa case.

Daga nan bai kuma yin magana ba nima haka har muka isa gida muna fitowa daga mota sai ga khabirat tana tahowa hannunta rikeda warmers na abinci a raina nace watakila anan ta samu ta ciyar dashi magani.

Ganina baisa taji komai ba don koda mukayi ido hudu harara ta watsa min nikam kauda kai nayi na dauki jakata na wuce ciki na barsu .

Ya jima a wajen kamin ya shigo nidai da na duba koina fes fes wanka nayi nazo na saka kayana snn na fara canza bedsheet .

Ya shigo ya sameni snn yace "ai wnn bedsheet din a wanke yake ko baki gani ba?

Nace " na gani mana.
Yace " to me yasa zaki canza?

Ba tare da na kulashi ba nace " to nasan ko su waye da waye suka kwanta akai?

Ya gintse fuska yace " bangane ba akwai wanda kk bari a gidan nan ne bayan ni?

Nan ma ce masa nayi " oho.

Hannu na ya rike ya fizgoni jikinsa da karfi na fadi kirjinsa na runtse ido cikin jin zafin fizgoni da yayi

Kallona yake snn yace" zargena kk yi ko?

Shiru nayi masa don haka ya hankada ni na fada gado yace " karki kuma yi mun irin wnn maganan!

Daga nan fita yayi nikam kuka na shiga yi.bansan sawan lokacin da na dauka ina kuka ba kamin daga baya na rarrashi kaina.

Shi kuma bansake ganinsa ba har karfe sha daya da ido kawai nake binsa har ya gama shirin kwanciya ya dauki bargo da pillow ya fita palo to fa!!!

Aikuwa ranar banyi bacci ba har gari ya waye tsabar tashin hankali.

Da safe kuwa ina hada mana break fast a kitchen ya shigo ya dauki flaks din ruwan zafi ya tafi dining ya hado tea ya kama sha da bread ganin haka yasa nayi masa na saka masa chepps da plantain dana soya da wsinar kwai a plet na kai mishi dining hade da fadin " yaya yau fa Sunday ina kk sauri zakaje?

Yace " zanje wani wuri ne.

Na danyi shiru snn nace " to kaci dankalin mana bari in kawo ma pepper soup....

Yace " na koshi sai dai in na dawo anjima.

Ya fada yayinda ya mike tsaye ya kalleni nima shi nake kallo yace " any problem?

Kai na daga masa yace " ina jinki.

Nace " so nake inje gun madam Fatima ina son shiga kungiyarmu......

Yace " ba damuwa kina iya zuwa koina a cikin barrack din nan na baki dama ko da bana nan sai dai fa ki kula da kyau da irin mutanen da zaki dinga muamala dasu.

Gyada kai kawai nayi nace " zan kiyaye dama gidanta kawai nake son zuwa don tana da kokari wurin zumunci.

Baiyi magana ba ya juya hade da fadin sai na dawo.

Bin bayansa nayi da kallo nace a dawo lfy.

Yana fita na zauna kan kujeran dining na zuba tagumi ina kallon plet din abinci dake gabana gabadaya kaina ya daure na rasa ta inda zan fara nema mana mafita.

Da kyar na lallaba na gama abinda nakeyi na tafi gidan captain bello

Na sami matarsa ta karbeni da fara,a sosai inda ta kaini har daki ranar kam ba abinda bata sanar dani ba akan rayuwar Lagos ko ince barrack tarihin mata daban daban da suka sha fama akan mazajensu da karuwai.gaskia na karu da abubuwa da yawa.kuma ta koya min dabaru da yawa

Har la,asar na dawo a gaggauce na dora girkin dare bayan na gama na shirya a dining .naje nayi wanka naci adona cikin English wears wando da riga mai kyau ya matse ni sosai ya fitar da duk wani shape na jikina.

Karfe biyar ya shigo da sallama hannunsa rike da ledoji na tashi da sauri ina mishi sannu da zuwa na karbi ledojin hannunsa amma na lura ko kallo ban isheshi ba.ya wuce daki abinsa.

Snn da daddare kuma muna zaune a Palo bayan mun gama cin abinci khabirat ta kirashi wai gata nan tazo nan da nan ya tashi ya zira jallabiyarsa ya fita tashi nayi nabi bayansa ina yaya ina kuma zakaje?

Yace " ina zuwa ba nitsa nayi ba.

Tsayawa nayi a jikin window ina lekonsu mota suka shiga ina jiran ya tashi motar amma shiru shiru suna ciki ko me sukeyi oho

O ni Rumaisa naga ta kaina tunda na dawo bangane kan ya salman ba sai yawan fushi da fada snn ya daina kulani ba wata alaka ta aure dake shiga tsakanimu to a Palo ma yake kwana abinsa.

Ranar da ya isheni na dawo palon na sameshi na cire dukkan kunya da fargaba nace " yaya don Allah me nayi maka ne ka sauyamin gabadaya?

Shiru yayi kamar vazaiyi magana ba snn yace " na sauya miki kamar ya?

Nace " yaya tunda na dawo yola babu wani abu da ya shiga tsakaninmu alhalin da ba haka muke ba gashi gabadaya baka kwana a daki tare da ni don Allah ka sanar dani dalili zan gyara.

Tashi yayi ya zauna yace " Rumaisa tunda kin tambayeni to bazan boye miki ba .duk sanda nazo kusa dake na kanji wani warin magani da bansan meye sa kk shafawa ba kuma ni banson warinsa.

Zaro ido nayi nace " magani kuma yaya to ai ni bana amfani da kowane irin magani nidai in nayi wanka maine nake shafawa sai turare shima ba kowanne ba tunda kaga ina da........

Katseni yayi da fadin " nidai na fada miki ki daina kawai don banson warinshi.

Jikina a mace na tashi na koma daki ina zubar da hawaye.

Tun ranar duk wani turarena na ajiye amma bai fasa ce mun ina warin magani ba.

Snn kullum sai ya fita gun khabirat su shige motarsa Allah kadai yasan me sukeyi .

Abubuwa sai kara tsanani suke don daga baya har turaran wuta na gida in nasa ce wa yake nasaka magani kuma yace min bayaso ranar gabadaya ya balbaleni da masifa da nace tak! ma nasan duka zan sha saboda nasa turaran wuta

Ranar bai kwana a gida ba hankalina ya tashi sosai na kasa hkr kiran mama nayi a cikin Daren na sanar da ita komai ban rage ba.

Abu na farko data fara ce mun shine " yaushe rabonki da ki tashi dare kiyi sallah ki gaya wa Allah matsalarki ?

Shiru nayi na rasa mai zance.

Ta sake fadin " yaushe rabonki da ki bude Quran ki karanta koda aya dayace ?

Nan ma shiru nayi ta sake fadin " azkar fa ?

Nace " mama inayi

Tace "azumin litinin da alhamis fa?

Shiru nayi
Tace" hmm nasan bakida amsar da zaki bani Rumaisa ya kk dauki rayuwane ? Waya fada miki a zamanin yanzu ana zama hakan nan ne ?

Nace " mama wlh tunda na dawo banma sami natsuwa bane.......

Ta katseni da fadin " bana son dogon surutu idan har kina son ganin haske a lamuranki to fa dolene sai kin koma kan turbar da na doraki .

Nace " to mama zanyi .

Tace " don haka sai da safe!!!!!

Kamin nace wani abu har ta kashe don haka da sauri na tashi Na wuce toilet na dauro alwala na fito.........

Hauly ce👍🏻🥰
[9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡65

************Kwana nayi ina sallah hade da gayawa Allah bukatuna har gari ya waye ba tare da gajiyawa ba.

Karfe shidda na shiga kitchen na shirya breakfast dina dan kadan don nasan ba lallai ne yaci ba tunda har yanzu bai dawo ba.

Na gama komai na aikin gida har na snn nayi wanka na kintsa jikina tsaf cikin English wear Riga da siket don sune kayana anan garin turare kadai ban fesa ba.

Daga nan na dauki Qur'an na bude na fara karatu sai dai kuma ko aya biyar ban karanta ba bacci ya fara dibana.

A fili nace" Auzubillahi minash shaidanir rajim ai yau banga abinda zai hanani karatun nan ba.

Don haka na tashi na dawo Palo na zauna kan kujera .

Karfe takwas ya Salman ya shigo da Sallama .

Na dago na kalleshi snn na amsa hade da fadin "yaya ina kwana ?

Fuskarsa ba yabo ba fallasa yace" lfy lau .

Rufe Qur'ani na nayi na tashi snn nace bari a hado ma ruwan wanka.

Na fada yayinda na wuce bedroom bayan na hada ruwa na fito daga toilet kawai na sameshi ya shirya cikin kakinsa yana daura igiyar takalmi .

Jikina a mace nace " yaya har na hada ma ruwan wanka.

Kai tsaye yace" nayi wanka a inda na kwana.

Nace " to ga breakfast a kan dining muje kaci.

Nan ma yace min " na koshi.

Daga nan ya tattara wayoyinsa zai fita nace " Allah ya bada sa,a .

Har yace amin zai fita bansan me ya tuna a ransa ba ya juyo ya kalleni yace " kina bukatar wani abu ne?

Nace " eh ina son dama inje saloon ne .

Ba tare da yace komai ba yasa hannu a aljihunsa ya Ciro wallet ya bude ya dauki 5k ya ajiye kan dress mirror ya fita.

Na bishi da kallo hade da fadin Allah ya kyauta .

Ba jimawa na shirya na tafi saloon da ke cikin barrack din .

Ana cikin gyara min gashi khabirat ta shigo ta madubi ba ganta da sauri na cire idona .

Ta kalli matar tace " mansura nazo wash and set kuma sauri nake suleyman na jirana a office

Matar tace" to ki zauna bari na gama yiwa wnn parking.
Chapter 71 · 0% Book details