← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 128

Sashe 112

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta katse ni.da fadin don Allah rufe min baki da zancen wofi .Wai kawai ganinsu kk yi makarciyar banza to bari kiji na gaya miki idan kk kuskura ko ciwon kai Nafisa tayi sai kin gane kurenki wlh .don haka ki kiyaye don hakane na kira ki.Sannan abu na biyu ga 'yarku nan taxo ta fada min komi.wato bazaku mata aure ba sai ta yi karatu.to me karatun zai tsinana mata? Ke kanki lokacin da uwarki ta nace sai kinyi jamia ina karshenta a karuwanci da shaye shaye kk kare ko an gaya miki na manta ne.to wlh bari kiji ahir dinki daga ke har Salman Ku kiyayi fushina.

Ka min nayi magana tuni ta kashe wayar!!!!!

Jefar da wayar nayi na fashe da kuka mai tsanani na rasa me yake min dadi a rayuwata ni rumaisa!

*Hmm* *masu* *karatu* *ina* *fatan* *kuna* *biye* *dani* ?
Wnn shine Asalin labarin rayuwar rumaisa.ku biyoni a pages na gaba don jin ci gaban labarin.

Shin ya zata kasance tsakanin farida da iyayenta ?

Ya Amarya nafisa zata kasance a gidan salman?

Ya kamata Innah adda A'i da sadiya asirin su ya tonu .ta ya ya?

A karshe rumaisah ce.......

🤪🤪🤪🤪Don jin karashin wnn labarin sai ku biyoni a ragowar pages masu zuwa nan gaba.nagode fans din rumaisan salman Allah ya bar kauna.❤❤❤

*WNN* *SHAFIN* *KYAUTACE* 👌🏻 *TA* *MUSAMMAN* *A* *GAREKI* *AUNTY* *MARYAM* (Shugabar kungiyar mu ta intelligent writer's asso. *Boss*😎👍🏻) *ALLAH* *YA* *KARA* *MIKI* *LFY* *YA* *TSARE* *KI* *DA* *DUKKAN* *SHARRIN* *MAKIYA.YA* *KARA* *JEFA* *SOYAYYARKI* *A* *ZUCIYAN* *OGA* *YA* *RAYA* *AFRAH* *DA* *MUHAMMAD* 🥰🙏🏻🙏🏻

Hauly ce🥰👍🏻
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡95

******Ji nayi zuciyata kamar zata huda kirjina ta fito tsabar azaba .

Dafe kirjin nayi sosai ba shiri na fara fadin Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!
Na fara kokarin lalubo wayar da nayi jifa da ita amma ina ya gagara sai ma wani tari dana kama yi wanda yake kara min radadi da ciwon kirjin......

Sosai na fita hankalina ina dafe da kirji ga tari kuma matsananci.

Cikin sa,a Allah ya kawo ya salman dakin domin haka kawai xuciyarshi ta bashi ba lfy nake ba.

Haka kuwa yana shigowa ya ganni cikin halinda ya matukar tsoratashi.da sauri ya isa wurina ya kamoni yana"Rumaisah menene?

Ina dafe da kirji nace"yaya mutuwa zanyi ka yafe min duk abinda na maka ka rokan min mama da daddy su yafe min ........farida da khalilullah duk na yafe m.....musu .....ka kula min da fareeda ......don ...Allah nasan mutuwa......

jikake dif numfashi ya dauke.idonsa ya kada yayi jazir saboda tashin hankali don bai taba ganina a cikin wnn yanayi na yau ba.

Rumgumeni yayi sosai a jikinsa zuciyarsa ta karaya sosai da kyar ya iya fadin"Rumaisa bazaki tafi ki barni ba in Allah ya yarda .

Da sauri yayi na maza yayi cak dani da matukar hanzari ya fita dani sai mota nan da nan drivernsa ya shiga yaja sai asibity .

Muna isa suka amsheni emergency ya salman na biye da su hankalinsa tashe .
Nan da nan likitoci uku suka hadu akaina sai shiga da fita sukeyi suma hankalinsu ya tashi sosai oxygen aka samin kamin su samo numfashina ya dauki lokaci sosai har sun fara cire ran zan sake numfashi a duniya .

ya salman yau kam fa babu batun jarumta duk yadda yaso ya daure abin ya gagara shi kadai ya dinga magana kamar zautacce har ya ba likitocin tausayi ce musu yakeyi "idan rumaisa ta mutu doctor bazan yafewa kaina ba domin a dalilina take ta shiga matsaloli kala kala.pls doctor kuyi iya kokarinku ku dawo min da lfyr matata.

Doctor ya girgiza masa kai hade da fadin"Salman Insha Allah zamuyi iya kokarinmu dan ganin rumaisa ta tashi amma fa sauki na wurin Allah shi zaka roka ya tashi kafadunta in kuma rabon shan ruwanta ya kare a duniya.......

Tab! Ai bai karasa ba saboda wani irin mugun kallo da ya Salman ya jefeshi da shi har ya tsorata ya danja baya snn yace"am sorry Allah ya bata lfy.

Daga nan ya tafi.

Hankalinsa bai kwanta ba saida numfashina ya dawo ya daidaita nan ya fara hamdala hade da godewa Allah.

Doctor ya kirashi office nan yace masa gaskia na kamu da ciwon zuciya sakamakon damuwa da ya min yawa ga kuma jinina da ya hau sosai don haka ina bukatar kulawa sosai da kuma addua domin lamarin ya tsananta matukar ba,a maida hankali wurin kula dani da kiyaye bacin raina ba to fa akwai matsala babba.....

Ya salman ya fahimci inda maganar doctorn ya dosa hankalinsa ya kara tashi sosai har ya rasa me zaice .

Doctorn yace"karfa ka damu shi cuta ba mutuwa bace insha Allah zata warware tass kuma zamu dorata akan magunguna a dinga barinta tana samun bacci sosai ta dinga hutawa kuma ku guji duk wani abu da kk san zai bata mata rai.in dai kun kiyaye wnn insha Allah zata warke.

Ya salman da kai ya iya amsawa doctor.

Doctor yace"kuma kaga munci sa,a sosai duk halin nan data shiga ba abinda ya sami cikin jikinta.sai ka godewa Allah.

Ya salman sai lokacin yace "Alhamdulillah sai dai ni a yanxu samun lfyr rumaisa ta fiye min komai a duniya.

Doctor yace"insha Allah zata samu lfy.

Haka Doctorn yaci gaba da kwantar masa da hankali.

******Nafisa kuwa bayan fitan ya salman ta kira adda A'i ....

Tun basu gaisa ba adda A'i ta shiga balbaleta da masifa"ke kuma shashasha mara hankali ashe kin yarda salman ya miki dadin baki kika biyoshi kano? Muna raba ki da wahala da zama da kishiya ke kuma ....

Nafisa tatari numfashin adda A'i da fadin"adda don Allah ki tsaya kiji mana nifa wnn ya salman din tsoro yake bani wlh ni inaga kamar bazan iya zama da shi ba shiyasa ma na kiraki dama fa kinsan niba shine zabina ba ke kika dinga zuga baba akan sai an hadani aure dashi ....

Adda A'i tace"kan uban can.Nafisa wnn wane irin magana kikeyi ? A ina ma kk tukunna?

Nafisa ta turo baki tace"a dakina nake kuma ni kadaice ya salman baya nan ya kai mummyn farida asibity.

Tsaki adda A'i taja snn tace"wnn matsalarsu ce in yaso ta mutu ma ni ina ruwana?yanxu dai kina jina?

Nafisa tace"inajinki mana.
Adda A'i tace "to don ubanki ki saurareni da kyau.dama nice rufin asirin familynmu gabadaya kuma yanxu kinsan cewa abubuwan duk ba kamar da bane komai na ya kare nayi iya kokarina wurin ganin na farfado da arzikina kamar da amma abin yaci tura kamar abin asiri gashi yanxu Alhaji baya taimaka min kamar da don shima kansa arxikin nasa yayi kasa.snn duk burin da naci akan yarana mata ya tashi a banza domin duk babu wacce ta auri wani mai maiko sosai bare nayi tunanin zasu min wani abun .ba yanda banyi da mahaifinsu ba akan ya bari su samu ma hannu da shuni amma yaki ya bi zabin ransu gashi nan yanzu babu wacce take tsinana mana komai.snn shi kuma mujahid shine kadai namiji kuma karami a cikinsu har yanzu bai wani karfi da zai iya rikemu ba.abubuwa duk suna neman kwabewa.......

Nafisa tace"ni adda wlh zaki cinye min kati kawai ki yi min maganar da ta shafeni .

Adda A'i tace"ke har yanxu bakida hankali ashe ? To bari in fito miki fili kinaji koh zagewa zakiyi da kissa da kisisina kija rabonki a jikin salman don kinsan kudi kam yana dashi domin kullum kwanan duniya arzikinsa karuwa yake.snn gashi baisan taimako ba kanshi kawai ya sani se kuma iyayenshi da yanuwansa na jiki snn ita kuma goggo (inna) ba ruwanta bata nunan masa ya taimaka mana ki duba halinda iyayenmu ke ciki har yanzu ba wani ci gaba da aka samu tunda dama ni dince mai yin komai ni nake kokarin sanya ku makaranta in kawo ku birni ku waye domin ku sami mazaje masu kudi mu hada kai mu kula da iyayenmu mu fitar dasu daga kauye.amma kinga abubuwa sunki nikam gabadaya jikina yana bani karayar arzikice tazo mana ga nabila can suna fama dama ita haka nan Allah yayita bata da kashin arziki daga aurensu mijinta komai ya koma baya.snn na dora buri akan madiha itama gashi babu abin kirki data ke tsinanawa.sa,adatu kuma kinsan ta muguwa ce ga tarin arzikin amma bata taimakawa kowa kuma bata da niyyar taimako duk da arzikin da mijinta ke dashi bama iya shi ba har ita kanta haihuwar ta na uku kasancewar ya mace ta haifa ba abinda dangin mijinta basu mata ba daga kan kyautan gida mota da gwalagwalai ga filaye batun kudi ba,a magana. amma kinganta ko a jikinta bata yi wani yunkurin taimakonmu ba.
Don haka nafisa yanxu duk wani burinmu akanki ne .kuma zan tashi tsaye wurin ganin kin mallaki zuciyar salman ta kowani hali domin ki sami naki kason babba a cikin tarin arzikin da Allah ya bashi wanda baya amfanar mana da komai a ciki tsabar mugunta.Don haka ki ajiye duk wata kiyayya da kk masa ki fara cusa ma zuciyarki sonsa ki dage da ladabi da biyayya haka nan kissa da kisisina na jan hankali gaki kyakkyawa duk cikinmu ba mai kyanki snn gaki yarinya mai kananan shekaru mazan yanxu sunfi son irinki.don haka kiyi amfani da wnn baiwar da Allah ya maki .ki ja mana kaso mai tsoka ta kowani hali kanwata kinji koh?

Nafisa ta danyi murmushi snn tace"na fahimceki adda amma ni gaskia yayan ne yake min kwarjini da yawa.

Adda A'i tace "kar ki damu kiris ya rage ya dawo a tafin hannunki sai yanda kika juya shi tunda aka daura aure kika tare anyi mai wuyan abinda ya rage shi yafi komai sauki kwantar da hankalinki.hmm baki ma fada min ba wani kyauta ya baki tunda nasan jiya ba karamin rikitashi kikayi ba nasan irin gyaran nan da kk sha dole yayi miki kyauta ta musamman.

Tabe baki nafisa tayi tace"hmm ni adda ce masa nayi ina period.....
Chapter 112 · 0% Book details