← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 128

Sashe 3

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba tare da na dami da abinda ya fada ba don ba shine a gabana ba.na tsallaka gefe naci gaba da tfyna

Fizge motar yayi da karfe ya bade ni da kura ya wuce sai lokacin na lura Ashe su biyu ne.

Nayi gaba kadan sai naga motar sun paka shi sun fito suna zaune a kai tabe baki nayi nace duk uban saurin nan naka dama nan zaku tsaya.

Har zan wucesu dayan yace minmalama don Allah muna da tanbaya.

Tsayawa nayi nace "to Allah sa na sani

Fuskarsa dauke da fara,a yace "ke kuwa 'yar kauyen nan ne?

Nace " eh.ka tambayi abinda zaka tambaya don sauri nake in isa gida.

Murmushi yayi ya kalli Dan,uwansa da ya kame ko kallonmu bayayi yana latsa wayarsa.

Yace kaji ai 'yar kauyen ne.

Ba tare da ya dago ba yace to ka tambayeta kawai mn.

Mai fara,an ya juya gareni yace"ya sunanki?

Cike da mamaki nace "tambayar taku knn?

Yace " aa ba shikenan ba akwai wata mata da mukaxo nema a kauyen nan.

Nace "wace mata knn me sunanta?

Yace " sunanta Amina kuma tana da 'ya Rumaisa ko Rumasa,u na Dan manta.

Bansan lokacinda nayi murmushi ba don tuni jikina ya bani 'yan,uwana ne.

Shi ma murmushi ya min nace " gidan na can gaba muje nima can zani.

Yace OK in ba damuwa zo muje a mota.

Na girgiza kai nace aa ni bana shiga motan da bansan masushi ba.

Dariya yayi yace gaskiarki kar a sace ki .to muje a kafa.

Ya juya ya kalli danuwansa yace"to oga munyi gaba ka biyo mu a mota.

Ko dagowa baiyi ba bare a sa ran amsa.

Muka jera dashi sai tadi yake min gashi da abun dariya.

Nace wai wancan me motar Dan,uwanka ne kuwa?

Yayi dariya yace Dan uwana ne ba kya ganin kamanni?

Nace hakane naga shi baya fara,a ko an bata mishi rai ne?

Yace "ke rabu dashi miskilancine zalla ba wani abu ba.

Na juya baya har lokacin yana zaune kan motar

Mun isa kofar gida Nace bari na shiga me zance da ita?

Yace kice mata baki daga birni.

Nace to.

Na shiga ciki da sallama can daki mama ta amsa min na sameta a dakin Nace mama kinyi baki sunce daga birni suke.

Tace baki daga birni kuma ?to ina suke?

Nace maza ne su biyu inaga ma kamar 'yan biyu ne sunzo da mota.

Ta danyi shiru daga bisani tace to sa musu tabarma kije kice su iso.

Nace to .

Bayan na shimfida tabarma na je na samesu Ashe har miskilin ya karaso na kalli dayan Nace ta ce bismillah Ku iso ciki.

Na wuce gaba suna biye dani a baya har ciki na nuna musu tabarma suka zauna .

Mama ta fito duk ta bisu da kallon rashin Sani suma kallonta suke.

Ta yi musu sannu da zuwa ta zauna a kujera suka gaisa.

Shiru ya biyo baya mama ne ta yanke shirun da fadin " sai dai ban ganeku ba kuyi hakuri don Allah.

Mai fara,an yayi murmushi yace "eh bazaki gane mu gaskia amma mu mun ganeki mu yaran....

Mama ta katse su da fadin tsaya in canka.

Murmushi ta yi ta mike ta karaso inda suke ta kallesu cike da fara,a tace" SALMAN da SALIM ne

Ta nuna miskilin tace Kaine salman.

Sannan day an kuma tace kai kuma salim.

Murmushi salim din yayi yace "hakane goggo Amina mune.

Mama cike da farin ciki ta zauna tana fadin Allahu Akbar kune kk zama samari haka?

Ta kalli salman tace" Salman ina innarku?ina yaya na ?

Yace duk suna lfy goggo amina da saninsu muka zo nan mun Dade muna nemanki.

Ta danyi dim sannan tace ayyah

Sannan ta kalli salim tace salim ya aunty Zuwaira da yaya kasim kannenka nawa?

Ya na murmushi yace su biyu ne fa,iza ne sai hakim.

Tace Allah sarki salman kaifa?

Yace su hudu ne mata sadiya da raihana.sai sakina da zainab yaran mama.

Mama cike da fara,a tace masha Allah gida ya cika.

Sun danyi shiru snn Salman yace Goggo ina yarinyarki ta girma sosai ko?

Mama tayi dariya tace " ta girma sai a fara shirin bikinku dama kai nace zan bawa.

Ta karasa maganar da dariya.shi ma ya Dan murmusa ya sunkuyar da kai.

Salim yayi dariya yace goggo kin ganshi wai bayaso to ki bani kawai goggo in ta girma muyi aure.

Mama tasa dariya tace wane girma kuma ta kusa gama secondary

Cike da mamaki suka dago suna kallonta tace ai itace ta muku jagora Rumaisa ba.

Salim yayi saurin fadin wow masha Allah goggo kin haifo mn indiya masha Allah salman kawai kayi serious ka ji in kuma bakayi ni dai ayi dani goggo.

Harararsa salman yayi bai ce komi ba.

Mama ta yi dariya
Sannan ta kwala min kira tana "rumaisa ki fito ki ba yayyunki ruwa mn.

Bata San duk abinda suke ina tsaye a window gabadaya murna kamar ya kasheni ba da sauri na saka hijabina na fita duk ido suka sa min kunya kamar na nitse.

Na wuce na dauko jug din roba na sa musu ruwa a randa na kawo musu da cup sannan na saka musu.

Mama ta kalleni tace rumaisa wnn yayyunki ne salman da salim yaran yayyuna biyu Wanda muke cike daya.

Murmushi nayi na kalli salim sannan na kalli salman abin mamaki sai naga yana kallona muna hada ido ya Dan saki fuska yace " kanwata kiyi hkr da abinda ya faru dazu.

Nace "babu komi laifina ne.

Mama tace ta yi muku rashin kunya ko?

Yace aa goggo nine na mata laifi.

Anan suka dinga min tambayoyi akan mkranta ina amsawa mama kam bata sa mn baki ba ta tafi ta hura wuta ta dora tuwo don tuni nayi miya.

Magriba yayi na kawo musu ruwa a buta sukayi alwala na fita na nuna masallaci suka tafi.

Bayan sun idar da sallar magriba suka dawo na kawo musu abinci sunci kuwa sosai.bayan sun gama mama tace in tattara kwanuka bayan na kai tace in tafi daki in dau torch light in yi karatu.

Anan na barsu suna hira har karfe takwas sukayi sallama.mama ta kira ni tace inje muyi sallama.

Tuni har sun fita salim ya shiga mota salman ne ke tsaye .

Na Dan russuna nace yaya Ku gaida gida mun gode da ziyara.

Na juya zan tafi naji yace"zo Rumaisa.

Na juya cike da mamaki na tafi gunsa.

Ya numfasa yace "zamu dawo nan da one week me kk bukata inzo miki dashi?

Na girgiza kai ina jin kunya nace" babu komi yaya na gode da kulawarka.

Bai ce komi ba yasa hannu a aljihunsa ya ciro kudi bansan ko nawa ba ya mika min

Na girgiza kai nace "aaa yaya na gode

Yace ki karba in baki son bacin raina .

Dole na karba nayi Godiya ya salim ma ya fito mukayi sallama sannan suka tafi.

Bayan nayi sallar isha ne na fadawa mama abinda su Kulu da zainab suka min.

Sosai ran mama ya baci tace babu komi zan kai karasu gun mai anguwa don a sawatar nasan uwarsu ce ke zuginsu.

Duk yadda naso mama ta ban labarin 'yan,uwanta sai kauce min take har na hakura .

Amma abin na damun raina duk da ma yau naga 'yanuwana .
[05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: _🌹RUMAISA SALMAN_🌹

👨🏻‍🚒 ```MATAR``` ~```SOJA```~ 👨🏻‍🚒

(_Labarine da ya kunshi soyayya,tausayi, fadakarwa,Ilmantarwa da kuma Nishadantarwa_)

Story and written
By
Maman khausar✍🏻

( *INTELLIGENT WRITErs ASSOCIATION*
*[onward together]*
*{we give the reader's of ours the best out of the bests,, our inks are melodious and dropping a kinda lights to reader's}*
```THE PEN OF LOVE😘 HEAT TORCHING❤ TEAR OF SORROWS😭 CURDLES😊 GIGGLES😁 AND MARRIEGE THINK💑```
*```JUST GIVE US FOLLOW..**
[ ```~BISMILLAHIRRAHMANI RAHEEM!~```

➡page 3

Bayan sati daya sai gasu sun dawo har da yayun mama.

Sun Dade suna tattauna Wa don ni mama tace in tafi islamiya tun bayan ba gaishesu.

Har na fita ya salman ya biyo ni

"Rumaisah!

Na juyo hadi da fadin na,am

Ya karaso gabana sanye yake da kananan kaya sun matukar amsarsa yana sanye da bakaken glass Wanda ya kara masa kwarjini.

Yace " muje na kaiki islamiyar a mota tunda akwai nisa.

Nace na gode yaya amma islamiyar mu in sunga an saukeni a mota.........

Ya katseni da fadin " ce musu zakiyi yayanki ne ai zo muje.

Ya bude min gaban motar banda zabi haka na shiga muka tafi har muka isa bamucewa juna sannu ba.

Ya sauko ya zagayo ya bude min ina fita sai ga Kulu da zainab sake baki sukayi suna kallommu har da tsayuwa.

Yace "nasan kamin ki dawo mun tafi.saboda haka ki kula da kanki kinji.

Kai na daga masa .

Aljihunsa ya lalubo ya ciro five hundred yace " gashi kiyi kudin break...

Na girgiza kai nace "aa na gode.

Yace" zamu bata fa waya gaya miki ana maida hannun kyauta baya?

Na karba hadi da Godiya baice komi ba ya shiga motar yaja ya tafi.

Su Kulu suka karaso wurina kallonsu nayi na dauke kaina na wuce.

Da sauri suka sha gabana zaunab tace " ke waye wancan mai motar?

Na harareta nace "ina ruwanku?

Kulu tace" kar ki yadda ki fada mana bakar magana yanzu anan muyi miki shegen duka.

Nace "hmmm bismillah mana.

Zainab ta harareni tace zaki fada in muka tare ki a lungu yasin

Taja hannun Kulu tace Kulu mu tafi

Kulu ta harareni tace karuwa kawai uwarki karuwa kema karuwa Allah wadaran zuriarku wlh.

Binsu nayi da kallo har hawaye ya taru a idona.

Bayan an taso islamiyya canza hanya nayi don in kuma haduwa da su zainab.

Bayan na idar da sallar isha nayi shirin kwanciya mama ta kirani naje tace " zauna.

Na zauna tace "rumaisa yayuna sun yanke shawarar daukeki a kauyen nan ki koma birni gidansu salman.

Na dago da sauri nace " alhamdulillh mama dama garin nan ya isheni kwanan nan su Kulu sun sakoni gaba.

Jikinta a mace tace "hmmm rumaisa ba don kar suce na kara bijire musu ba da nace su barki kawai.domin gidansu salman zamanki a wurin akwai matsala Innar su salman bata da kirki ko kadan.
Chapter 3 · 0% Book details