← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 128

Sashe 41

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rannan kam ranshi a bace yace " amina bansan da wani yare zan miki magana ba wai me yasa kk damuna ne? Kinga in bazaki iya zama dani haka ki kama gabanki ke kinga na ma sawwake miki kawai ki dauki 'yarki Ku bar min gida.

Cike da mamaki da tsoro amina tace " what Ibrahim me kk nufi?

Kai tsaye yace " amina na sakeki saki daya.

Yana fadin haka yayi ficewarsa amina kam jiri ne taji ya fara dibanta a hakali ta fara fadin innalillahi wa inna ilairrajiun !!!

Da kyar ta dawo hayyacinta ta fashe da kuka mai tsanani ta rumgume rumaisa.

Sai da tayi mai isatta snn ta shirya kayanta ta tafi gidan galadima anan ta sanar ummah komai.

Hankalin Haj rumaisa ya tashi matuka don haka ba bata lokaci ta nemi Ib tayi masa tatass kuma tace dole ya maida Amina.

Haka ya hkr amina ta koma yayinda Haj rumaisa ta cewa Amina ta dage da addua domin sakacinta ne ya jawo mata hakan

Ita kanta Amina tsan da hakan domin yanzu ta saki jiki ta shagala ba kamar da ba don haka dole ta mike tsaye.

Wnn karon wulakancin Ib ya ninka na da sau dubu don ko girki amina batayi bare kuma zuwa turaka.

Jamila da yaranta kawai ke cin karansu babu babbaka a gidan.

Wasa gaske amina ya kasance sai tayi sati bata ga ib ba.

Abinci ma sai Jamila taso amina keci a gidan don a yanzu ko 'yan aiki sun fita daraja.

Ranar aka wayi gari rumaisa ba lfy nimonia dinta ya tashi kirjinta na toshewa.

Amina tayi sa,a ta sami ib a dakinsa yana karatun jarida

Durkusawa tayi tace " lamido don Allah don annabi ka tausaya rayuwata data ihisan gata nan ba lfy ko bacci ba muyi ba jiya don Allah ka taimaka ba don halina ba ka kaita asibity.

Ba tare da ya ko kalleta ba yace " ki kaita mana kawai meye sai kinzo kin matsa min

Amina cikin matsanancin kuka tace" don Allah Ibrahim ka gaya min abinda na maka kake min irin wnn horon ? Ko ka manta banda kowa sai kai din ka tuna fa na bar garinmu yayyuna na bijire musu saboda kai yanzu ina kk so nasa rayuwata?

Murmushi yayi yace " na godewa Allah da kika gane kuskurenki na rashin biyayya ga yayyunki.

Ya numfasa yace karki damu lokaci bai kure miki ba kina iya zuwa ki nemi gafarar su indai nine matsalarki amina kije daga yau na yanke igiyoyin aurena dake kanki ma,ana na sakeki saki biyu in kin hada da waccan ya zama uku!

Amina ta mike da sauri ta kalli Ib cikin bacin rai tace " Ibrahim kana cikin hayyacinka kuwa ko kasan me kk fadi?

Yace na sani sarai amina zama dake ya isheni bana son ganinki daga ke har 'yarki Ku fita Ku bani wuri kuma na baki yau da gobe ki tattara Ku bar min gida na har abada ke da ' yarki kar Wanda ya kuma dawowa gareni bana bukatarku.

Ya karasa fada cikin tsananin fushi .

Tashin hankali ranar amina taga matsifar rayuwa haka ta sanyawa zuciyarta hkr ta dauki ' yarta ta kaita hospital bata fadawa kowa ba don yanzu kam tsakaninta da ib ya kare tunda babu sauran igiyar aure don haka babu amfanin taje ta fadawa Hajia rumaisa .

Bayan sun dawo ta tattara kaysnta da gwalagwalanta duka kudadenta kam ta adanasu a bank.

Kafin ta bar Adamawa sai da ta tabbatarwa ib bazata kuma dawowa ba daga ita har 'yarta sai ya nemesu da kansa.

A wulakance yace "alhamdulillah haka nake son ji .don ki Sani nima bazan nemeku ba kuma har abada matsiyata kawai!!!

Da wnn bakin ciki amina ta bar Adamawa ba tare da sanin su Haj rumaisa ba .

Gaskia amina ta yanke wa kanta hukunci cikin fushi don saida ta isa Kd ta fara tunanin da wani ido zata ga yayyunta kuma me zatace musu.????

Hauly ce🥰👍🏻
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰

*Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤*

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```

Page➡36

***********Amina ta isa gidansu zuciyarta sai tsinkewa yake haka ta daure ta shiga sai dai sam ba su tasamu ba wasu ne daban anan ta shiga yi musu bayani amma basu gane ba.

Abin mamaki makwaftansu ma data ke shiga sun kaura dake gidan hayane.

Amina a karshe dai gidansu Zuwaira taje gaskia taga kallon banza babu Wanda ya kulata sai maigadine yake fada mata su Zuwaira sun koma kano da zama shekaru kusan shidda yanzu.

Don haka amina bata tsaya ba ta sake samun motar kano ta tafi har cikin dare ta isa .dake tasan gidansu na gado don nan ne yayyunta sukayi gini.

Duk da haka sai da tasha wahala snn ta gane .ta shiga gidan da sallama yayinda take bin gidan da kallo sungyareshi yayi kyau ginin zamani lallai arziki yaci uban Nada.

Wata matace ta fito rikeda yarinya.
Anan fa amina ta fara tunanin ko ba gidanneba.

Suka gaisa da matar cike da fara,a

Amina tace " don Allah nan ne gidansu Mohd da kassim?

Matar tace " eh nan ne.

Amina tayi ajiyar zuciya tace " Zuwaira na nan ?

Matar tace ' eh yanzu kuwa ta tafi sashinta bari na fada mata tayi bakuwa.

Anan matar ta tafi amina ta bita da kallo a ranta tana fadin wnn din kuma wacece?

Tana cikn wnn tunanin suka fito amina tuni ta gane Zuwaira amma ita sai da ta matso ta karewa amina kallo ta dafe kirji tace"Amina!!!

Hawayene ya ciko idon Amina suka rumgume juna da Zuwaira suna kuka Wanda yaja hankalin yaran gidan kanana .

Sai kuma shatu data fito wanka ganin amina yasa ta saki salati tace amina! Kece? Dama kina raye? Tab bari nayiwa yayyunki albishir .

Da sauri ta wuce Palo inda su kasim da Mohd suke hira sai su salman da salim Wanda a lokacin suna da shekara 13 a duniya .

Anan shatu ta sanar dasu dawowar Amina.

Gabadaya suka fito tsakar gidan ganin da gaske amina ce.yasa Mohd yin murmushin takaici yace " Amina dama nasan dole ne ki dawo watarana don bakuda wayanda ya fimu.
Ya kalli shatu yace " shatu kuje da ita Ku kwanta dare yayi koma meye a bari sai gobe.duk kuje Ku kwanta.....

Kasim da yaketa cika da maganar Mohd yace " haba yaya ina zata je wlh ta bar mana gidanmu mu muka San daga ina ta fito?

Shatu ta karba" kuma gata da goyo ko ina ta sami yarinya kuma oho.

Sai lokacin duk suka lura da goyon

Kasim ya kalli Mohd yace " kagani ko ? Amina sai da tagama yawonta taje ta debo mana abin kunya snn ta dawo wlh Sam zaman Amina a gidan nan bazaiyiwu ba.

Shatu tace " wnn gaskiane kasim .

Ta kalli amina dake kuka tace " sai yanzu da kika gama yawon karuwancinki zaki dawo mana da goyo? Amma amina kinji kunya wlh .....

Ta karasa fada hade da fashewa da kukan munafurci tana fadin yanzu fisabilillah abinda zaki mana knn dama tunda kk tafi yanuwanku sai nuna mu suke wai mun kasa baki tarbiyya mun barki kin tafi karuwanci alhalin sauran sati daya da bikinki.yanzu shine kk dawo da yarinya don ki tabbatar musu karuwancin kk je?

Maganar shatu tayi tasiri a zuciyan Mohd da kassim .

A fusace kassim ya kalli amina yace " ki fita daga gidan nan tun kamin na miki illah in yaso kije kici gaba da karuwancinki .

Matar can ne da ta fara ganin amina tace " haba kassim Ku saurareta mana.....

Mohd ya tari numfashinta da fadin " kar ki shiga maganar nan rabi domin baki San komi ba.

Zuwaira ta goge hawayenta tace " amma yaya ya kamata ace Ku saurari amina watakila abinda kuke tunani ba haka bane.don Allah Ku barta haka sai da safe......

Kassim yace " ke Zuwaira bari kiji amina bazata kwana a gidan nan ba don haka ta fice daga gidan nan kawai ta koma gun wayanda ta zabesu fiye damu......

Zuwaira tace " yanzu a cikin Daren nan a naka tunanin ina zata je?

Kai tsaye yace " ta koma inda ta fito.

Zuwaira tace " wlh bazaiyiwu ba babu inda amina zataje don itama nan din gidan mahaifinta ne kuma tana da gadonta ko karyane? Don haka ba inda zata je don naga ka dage da yawa.baka San kuskure bane ko bakasan kaddara ba?

Kasim ya harzuko yana shirin yiwa Zuwaira magana Mohd yace " ka rabu da ita kawai barsu aminan ta kwana in yaso gobe sai tasan inda dare ya mata.

Kasim ya kalli Zuwaira cike da jin haushi yace " wlh da ba don yaya ba kema da sai kin bar gidan nan cikin daren nan.

Zuwaira tayi mishi wani irin kallo sannan ta watsar ta kalli su salman tace " kai salim kuzo Ku dauki kayan goggonku Ku kai dakina .

Lokaci guda sukace " to Momy
Zuwaira ta kama hannun amina tace "zo muje ciki amina yi hkr.

Shatu tace " lallaima Zuwaira har wani hkr kk bata ? Anan kiri kiri babu tsoron Allah tace bata son danuwanki.

Zuwaira tace " sai me don tace bata son danuwana ana son dole ne?

Mohd da kassim shiru kawai sukayi .

Yayinda rabi ta wuce dakinta shatu kam har lokacin magana takeyi tana kara ingiza su Mohd .

Zuwaira kuwa ranar taki zuwa turaka anan suka zauna da amina sukaci kukansu har suka gaji .

Tace " amina ina kk shiga kk barmu cikin tashin hankali ni da yayyunki?

Amina tace " aunty Zuwaira labarin mai tsawone sai gobe in Allah ya kaimu zan fada miki .

Zuwaira tace "to Allah ya kaimu.kin dawo kinga gida ya cika da yara ko?
Chapter 41 · 0% Book details