← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 128

Sashe 5

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadiya tace wlh kuwa don mukam 'yunwa mukeji

Raihana ta karba tace bare ma anyi ruwa kam dama sai yunwa.

Na mike idona tuni har yayija na fita sai ruwa ake tayi kamin na isa kitchen har na jike charkaf Ashe itacen ma sun bari a waje ruwa ya gama jikawa.

Haka na kai kitchen na hada murhu na hura huta na nemi wuri na zauna naci gaba da kuka sosai ina bakin cikin kasancewata a raye dama mutuwa nayi.

Na kai awa daya ina kokarin hura wuta amma ina yaki kamawa ga hayaki ya turnuke kitchen ko gani banayi da sauri nayi waje a gigice idona duk yayi ja sai kwallah.

Sadiya ta fito zata ban daki har zata wuce ta leka kitchen taga hayaki.

Ta shiga tafa hannu tn salati tace yanzu tun fitowarki baki dora ba muguwa so kike ki kashe mu da yunwane?

Shiru na mata tace ina miki magana kina tsaye ko?to wlh kamin na fito ban daki ki fifita wutan nan ya kama.bayan yunwa har horo zaki mn da hayaki ki cika mn ciki muguwa kawai anyi gadon mugunta.

Ta wuce bandaki zuciyata kamar zata fashe hawaye kuwa yaki yankema idona.

Ta fito daga bandaki ta sameni zaune a wurin

Tace kan ubancan lallai ma yarinyan nan taurin kai zaki min ko? Zan nuna miki na fiki danyan kai.

Ta rufe leman hannunta ta wuce randa fuuu!ta debo ruwa cikin botiki ta nufi kitchen da isarta tajuye ruwan cikin murhu.

Zaro ido nayi ina kallonta na tuna irin wahalar da nasha akan hura wutan nan.

Murmushin mugunta ta yi tace "duk sanda kika gama hutawa kyaje ki hura wani don bazaki kashemu da hayaki ba.

Ta shige daki.na bita da kallo sannan na fashe da kuka. Durkusawa nayi a bakin kitchen ina ta rusar kuka.

Sai kawai ga ya salman Ashe tuni ya dawo ruwa ya hanashi shigowa shine yanzu da ruwan ya Dan dauke ya shigo.

Yana ganina cikin wnn yanayin yace" subhanallah! Ke me kikeyi a ruwan nan?

Ban kulashi ba kukana kawai nakeyi.

Ya karaso bakin kitchen ya riko hannuna yana "taso taso.

Ya kalleni yace me ya faru dubi yanda kk jike don Allah tafi ciki ki cire wayan nan kaya.

Inna ce ta fito daga daki tace " ba wani canza kaya da zatayi don Allah sabar munafurci ba wuta nace ki hura ba? Shine kk barmu da yunwa kk zauna cikin ruwa kika jike don munafurci ko?

Na girgiza kai nace Inna har na hura wutan sadiya taxo ta Debi ruwa ta zuba a murhun kuma dama itacen sun jike.

Tace madalla ina tun lokacinda hadari ya hadu nace Ki shigar kitchen kikayi banza da maganata don ba uwarki bace ni ko?

Nace aa inna raihanace kk ce ta shigar......

Ta katseni da fadin zaki wuce kije ki hura wutan ko zaki tsaya kina min musun raini shegiyar yarinya.

Sai lokacin yayi magana yace "aa inna gaskia bazata iya hura hutan nan ba saboda murhun ya jike.kawai suje da raihana su sayi gawayi don gaskia ina jin yunwa.

Inna batayi magana ba ta wuce ciki .

Ya kalleni yace jeki cire kayan kice sadiya da raihana su zo yanzu ina jiransu an an.

Na wuce ciki ya bini da kallo duk kunya ya kamani saboda yanda rigan ya kama jikina da ya jike.

Bayan na kirasu sai hararata suke na wuce ciki.

Ko da suka fita yacewa sadiya maza ta wuce kitchen ya bata minti. Talatin ta hura wuta in ba haka ba zata ci duka.

Ya bawa raihana kudi yace ta wuce taje ta sayi gawayi.

Sannan ya. Shigo palon innah.

Nikam bayan na canza kayana Sai naji bugun zuciya ta ya canza kirjina ya to she numfashina ya fara fita sama sama har wani barazanar daukewa yakeyi.

Bansan sanda na fara kiran inna ina zan mutu wayyo Allah na ina dafe da kirji.

Ta gudu suka shigo suka sameni cikin wnn yanayi inna kam Sai salati ya salman bai tsaya wata wata ba ya fita waje da sauri kamin ya dawo tuni numfashin ya dauke .cak! Yayi dani ya tafi ya Sani a mota Sai asibity emergency aka karben nidai bansan inda kaina yake ba.

Lokacin da na dawo hayyacina Sai kalle nake doctor ne ya shigo da ya salman

Ya sake duddubani sannan yace "yanzu kam ba wata matsala ko?

Shiru na masa.

Yayi murmushi yace me kk ji a Jikinki yanzu?

Nace " babu komai jikinane ba kwari.

Yace ba wata matsala a hankali zaki warware .

Sannan ya juya wurin salman yace "don Allah a kulada ita sosai ciwon asma nada hadari.

Da kai ya amsa masa docton yaci gaba da fadin kuma akwai ulcer ma don haka a sayi magunguna da aka rubuta mata duka Allah ya bada lfy kuna ita tfy.

Anan suka fita da ya salman.ba jimawa ya shigo ya kalleni yace zaki iya tashi?

Na daga mishi kai alhalin naji jikina ba kwari .

Ganin yadda nake ta kokarin tashi na gagara yasa shi isa bakin gadon ya dagoni Dan kwalina ne ya zame ya fadi gabadaya gashi na ya baje har fuska dama ya tsawo ga cika ga kuma yauki gashi ban iya parking ba na saba da kitso.

Kallon gashin yakeyi har ya shagala da sauri na fara lalubo Dan kwalina.

Sai naga ya kai hannu ya tattara gabadaya ya ce ina rivom?

A kunyace nace bandashi .

Ba zato ba sammani naji yace dama an taba yin budurwa ba rivon ne? Ke dai 'yar kauyece.

Na girgiza kai nace mama tana saya min amma sun bata ne wasu kuma sun sake.

Baice komi ya tattara min gashin sannan ya kawo hijabi ya sakamin ya riko hannuna yace mu tafi .

Yana rike da hannuna har muka isa bakin mota.

Muna isa gida muka tarar inna har ta shirya da mmn sakina zasuje asibityn.

Suna ganinmu cike da mamaki Maman sakina tace har an sallamota ?ikon Allah.

Inna ta karba tace "har mun tsorata yarinya kamar baza ta tashi ba ?

Salman ya kalli sakina yace " sakina zo ki rike hannunta kuje ciki.

Sakina ta riko hannuna duk sai sannu suke min mun shiga palon inna na kwanta sakina ta kawo min pillow.

Nan naji ya salman yana cewa "inna rumaisa asma take dashi likitan yace a kula da ita sosai don ciwonta bai son sanyi baison hayaki ko kura da makamantansu don Allah a kiyaye.

Sannan ya kalli sadiya tace " ke kuma wlh wlh ki kiyayeni don idan kk kuskura kk shiga hannuna sai ki yabawa aya zakinta muguwa kawai.

Ya kalli raihana yace ke kuma idan kk ce zaki dinga biyewa sadiya zaki ji jiki wlh nonsense kawai.

Ya juya ya fita innah ta bishi da kallo sannan tace " jeka masifaffe mutum ne baza a taba maganar arziki da kai ba kullum cin magani.naga matar da zata aureka da wnn bakar zuciya taka.

Maman sakina tayi dariya tace " wlh kuwa matarsa na nan gau a leda.

Raihana ta karba tace don ma bakiga yanda 'yan mata ke binsa yana gwalesu bane.

Inna tace " a hakan?mtswww

Maman sakina tace ai ina mamakin yanda ya nace akan Salima alhalin ba bashi aurenta zasuyi ba.

Inna tace "saboda sun ganshi Dan talaka ne ai bai da komi sai uban zuciya da miskilanci.

Sadiya tace aa so suke suyi mata auren dangi ne.yaya kuma sai dagewa yake yi akanta.......

Shigowarsa ne ya katseta gabadaya shiru sukayi suna binsa da kallo.

Ya ji su sarai sai dai baiyi magana ba ya wuce dakin innah ya sameni ina kwance yace "kinci abinci?

Nace"aa.

Dan tsaki yayi sannan ya fito ba jimawa ya shigo da plet guda biyu da cokula .

Ya dauko kular abincinshi yayi mn serving jalof ne da wake da manja.

Ya taura min gabana yace tashi kici bari in gama inje in sayi maganinki.

Na mike a hankali na jingina da kujera na fara ci kadan kadan ina ware wake gefe guda.

Yace " ba kya son wakene?

Nace,"eh

Yace" ke dai 'yar kauyece.

Bance komi ba har ya karasa cin abincinshi zai tashi inna ta shigo tace "yawwa salman zauna inada magana.

Ya koma ya zauna ba tare da yace komi ba.

Inna tace ,su sadiya sun kawo min korafi akan in suna tsaye da samarinsu kn zuwa ka musu wulakanci ka koresu hakane?

Kai tsaye yace" eh

Inna ta matukar kulewa tace"to meyasa jika su zamuyi musha ne?

Yace " karatu zasuyi.

Inna ta harzuko ta kama bala,i makarantar banza mkrantar wofi baza suyi ba wlh.mkrnt indai irin wacce goggonku Amina tayi ne Allah wadarai wlh.domin ni tun kan goggonku amina naga illar nitsa a karatu don haka ni yarana suna gama wnn secondary aure zasuyi shine rufin asirinmu baki daya.don haka kar in kuma jin ka sake Koran musu samari ba ruwanka kai da kk zuwa naka zancen Wa ya tanka?to ka kiyayeni wlh.

Baiyi magana ba mikewa yayi ya fita.

Nikam na kasa cin abinci saboda maganganun inna na Dade ina juya maganar a raina.

Tunda na gama shan magunguna na na warware tass .

Naje gaida kawu a daki na tarar kawuna na Abuja ma yazo .na gaishesu cike da fara,a suka amsa

Abbansu salman ne yace " Rumaisa mamarki ta yi aure daurin auren mukayi dazu a kofar gidan nan.

Kaina a sunkuye nace "Allah ya bada zaman lfy.

Suce amin suna dariya sannan daddynsu salim yace " sai in ta tare za,a kaiki kinji?

Nace to.

Daga nan na mike na musu sai anjima.

Ina fita muka tafi shago da sakina.

Muna dawowa a kofar gida na hango ya salman zaune kan kujerar roba da wata tsugunne gefensa kanta sunkuye abin mamaki fuskarsa daukeda murmushi.

Naja hannun sakina da sauri mukayi baya tace lfy?

Nace"aa ya salman na gani da wata ko itace saliman naga har murmushi yake tayi dama yana dariya?

Sakina ta yi dariya tace nima tun tashina ban taba ganin yana fara,a ba sai da Salima.yaya yana son Salima sosai amma iyayenta basaso sunfi so su hadata auren dangi da danuwanta kuma ma gidansu sai sunyi jamia tuku......

Na katseta da fadin dama bata gama secondary ba?
Chapter 5 · 0% Book details