← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 128

Sashe 126

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saida su daddy suka zo har gida sukayita masa nasiha hade da tunatar dashi darajar mahaifiya snn Allah da kansa ana masa laifi a rokeshi ya yafe bare mu 'yan Adam.

Kalamansu ya sassauto dashi har yayi wa inna magana kuma ya yafe mata hade da bata hkr.hakama sadiya yace ya yafe mata.

Inna ta jima bataji farin ciki irin ranar ba haka ta dinga saka mishi albarka.

Sadiya ma ji tayi tamkar ta sauke wani kaya mai nauyi a kanta don nima tuni ta rokeni da na yafe mata na ce mata komai ya wuce.

Allah sarki inna da sadiya sun rame sosai don ni tausayi suka dinga bani .

( _Hmm_ _Allah_ _ya_ _bamu_ _ikon_ _fin_ _karfin_ _zukatanmu_ )🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

***Na gama duk wani shirina na bacci na fito daga dakina na kulle dakin farida na leka na sameta ciikin bargo sai sheka bacci take hankali kwance ko wutan dakin bata kashe ba ga A.C data kure dakin yayi sanyi tamkar kankara.

Girgiza kai nayi na karasa shiga dakin na rage A.c snn na karasa bakin gadon na tasheta.da kyar ta bude ido hade da fadin"na,am mama

Nace"ki tashi kiyi addua nasan bakiyi ba haka kk zube kika kama bacci.

Tashi tayi ta kalleni tace"mama lfy baki yi bacci ba har yanxu.

Murmushi nayi nace"yanxu ne dare ya fara yi ai hajia inna ke dai dan kinyi bacci da wurine kinga agogo yanxu ne goma saura minti shidda.

Ajiyar zuciya tayi snn tayi addua ta kwanta hade da fadin "mama ina missing din su hanifa meyasa bazakice hajiya Amina ta dawo dasu ba?

Murmushi nayi don nima kaina ina kewar twins dina sosai tunda muke asibity mama ta daukesu suna gurinta yanxu watanninsu takwas har sun fara takawa ko ina cikin ikon Allah gashi basuda laulayi kuma komai suna ci don haka mama tace in barsu kawai inci gaba da kula da ya salman.

Farida tace"mama gobe zanje in daukosu.

Nace"ai mama bazata yarda ba sai dai kije ki gansu ki dawo.

Tace"to inaga zanyi oneweek acan.

Na girgiza kai nace "bazaiyiwu ba domin yanxu dama nake shirin gayawa daddynku tunda kun samu hutu yola zaki tafi aunty samira zata miki wasu shirye shiryen don kinga daddynku yace baison bikinku ya wuce karshen wnn wata kinga knn yanzu sati uku ya rage da kwana biyu bamuda isasshen lokaci sosai.gara kije yolan ki karasa sauran shirye shiryenki acan.

Sunkuyarda kai tayi tana murmushi tace "mama why not kice daddy a bari sai next month don gaskia nanda 3weeks ya min kadan.

Nace"nima kaina zanso ya bari sai next month din saboda shirye shiryena nima amma kinsan daddynku sai a hankali.sai dai zan gwada rokon ya salim.

Tace"yawwa mama in kin gayawa dad kam zai yarda kuma zai shawo kan daddynmu.

Na ce"to shikenan yanxu ki tashi ki rufe kofanki ki kashe wuta kiyi addua ki kwanta se da safe.

Tace "Allah ya tashemu lfy.

Nace amin snn na fita.
Dakin khalil na tafi je shima na samu yayi baccinsa hankali kwance .daga nan na wuce sashin oga.

Ina tura kofa sai duhu ya min maraba cike da mamakin abinda yasa ya kashe wutar dakin nake na karasa shiga ina kunna wuta snn na rufe kofan.

Can na hangeshi kan gado yana kwance a rigingine hannunsa duka biyu ya rumgume kirjinsa yayinda idonsa ke kallon saman daki alamun yayi zurfi cikin tunani don baima san na shigo ba.

Da sauri na karasa gadon na zauna ina fadin"yaya lfy bakayi bacci ba har yanzu kasha magani kuwa?

Tashi yayi a hankali ya zauna snn ya kalleni yace"nasha tun dazu.

Ajiyar zuciya nayi na matsa kusa dashi sosai na dora kaina kan kirjinsa ina lumshe ido nace "yaya har yanxu kamar baka saki ranka ba akan abinda ya faru.domin kana takurawa zuciyarka da tunani kuma doctors sun hana ka.

Shafa kaina ya shiga yi a hankali yace"baby ya zanyi ne ? Tunanin abubuwanda su inna suka muku yaki barin zuciyata nakan rasa dalilinda yasa innata miki wnn abun.Rumaisah tausayinki ya hana ma zuciyata sukuni abinda ya faru dake a shekarun baya su ke dawo min ko wani lokaci.....

Gabana ne ya fadi jin dumin hawaye ya sauka a fuskata ba shiri na daga kai na kalleshi da sauri.

Dan zaro ido nayi hade da dafe kirji nace"what! Hawaye ? Yaya hawaye a idonka?

Kawai nasa mishi kuka na kifa kaina a kirjinsa rumgumeni yayi yace"baza ki gane yadda nakeji a zuciyata bane rumaisah Inna bata kyauta ba kuma gaskia ta zalun.......

Hannu nasa a bakinsa ina girgiza masa kai nace "ka daina maida hannun agogo baya yaya komai ya wuce a gurina tuntuni.dama haka Allah ya kaddara hakan zata faru gareni ban isa in tsallake kaddarata ba.don haka nidai ka bar tuna abinda ya faru a baya ka share komai muci gaba da rayuwarmu cikin farin ciki.

Nasa hannu na ina goge masa hawaye hade da fadin"kasan me?

Zuba min jajayen idanunsa yayi hade da girgiza min kai .

Na danyi shiru snn nace"da ba don abinda ya faru dani a baya ba da yanxu ba kaine mijina ba.ko ka manta yarima Abdallah ya fasa aurenane saboda abubuwanda yaji akaina lokacinda nike jami,a ? Da ba don faruwar hakan ba da aurenmu baiyiwu ba yaya.amma kaga ikon Allah yana cewa ya fasa aurena a daren washe garin aka daura aurena da kai ....

Na lumshe ido ina murmushi hade da hawaye ajiyar zuciya yayi yayinda ya shiga share min hawaye yace"shikenan maganar ya wuce kinsan a rayuwa bana son duk abinda zaisa inganki cikin tashin hankali.
Nace"nima haka yayanah bana son ganinka cikin damuwa ko kadan.

Dada rumgumeni yayi yace "Allah ya miki albarka my dear ina alfaharin kasancewarki mata a gareni.duk duniya babu wanda ya kai salman dace da mata ta gari mai hkr da sanin ya kamata.

Dan dariya nayi nace "Yaya karkasa kaina ya fashe don Allah.yanxu dai mu kwanta bari in maka addua kayi bacci kasan doctor yace ka na samun isashen bacci domin kwakwalwarka ta huta sosai.

Murmushi yayi yace"yau ba bacci nake bukata ba.matata nake bukata don gaskia yau kam hkr na ya gaza .

Ya karasa fada yana kashe min ido daya kunya ne ya dan kamani nace"kai yaya ka bari dan Allah sai ka kara samun lfy....

Yace"what? Ainin na gama samun lfy insha Allah.kwanan nan zan samowa su hanif kani ko kanwa tunda sun girma yanxu.

Ina shirin yin magana kawai ya hade bakinmu wuri daya .
To fa daga nan labari ya sauya lumshe ido nayi ina karbar sakonninsa ba shiri na shiga maida martani.

Aikuwa ya tabbatar min da ya samu lfy don da kyar na kwaci kaina kunsan yaya dama ba sauki a wnn harkar .

Da kyar nayi sallar asuba don saida na gasa jikina sosai.
Yana dawowa masallaci muka sake komawa .....

Mune bamu samu fitowa ba a ranar har sha daya shima yunwane ya tashemu kuma gashi lokacin sha maganinsa har ya wuce.don haka dole muka tashi mu ka sake wanka na taimaka masa ya kintsa cikin kananan kaya shirt and trouser da suka matukar karbarsa ya koma kamar saurayi dan shekara 30

Ina fesa masa turare nace"yaya gaskia kamin wayo da yawa dubi yadda kk kullum kamar wani saurayi in ka jera da munir kamar friends fa.

Dariya ya danyi yayinda yaja hancina snn ya sunkuyo ya manna min kiss a baki yace"kema fa hakan ne baby har yanxu baki tsufa ba keda farida kamar kawaye.babu wanda zai yarda ke da darling(ruma) da fa,iza da sakina da raihana sa,o,ine don duk kinga sun koma iyaye amma ke har yanxu kina a babynki.

Ya lumshe ido hade da fadin hmm gabadaya jinki nake kamar wata budurwa duk kin rikitani jiya baby domin kin sake zama fresh kuma gabadaya kin tuna min da first night dinmu jiya.don Allah meye sirrin ne?

Rufe fuskata nayi da tafin hannuna ina dariya na wuce gaba bina yayi a baya har muka fita palo yace"muje na tayaki shiryawa kema

Riko hannunsa nayi na zaunar dashi nace "na hutar da kai bari na kira munir yazo ya kara duba min kai kaga ma bakasha maganinka ba bamuyi breakfast ba....

Shigowar munir da sallanarsa ne ya katseni.
Na dan saki hannun ya salman snn na kalli munir ina amsa sallamarsa nace"kaga dan halak dama yanxu nake shirin in kiraka baka fita ba knn?

Yace"yanxu dawowata mama nazo in duba daddyne .

Nace"to bari yayi break fast.

Bayan mun gama breakfast na barshi da munir na tafi dakina nima don in shirya.

Sosai na dage naci kwalliya nasaka riga da siket na lace blue mai adon orange nayi kyau sosai domin kuwa na fito tamkar wata budurwa .gaskia ya salman ya fada domin har yanxu jikina babu alamun tsufa don da can ni ba mai kiba bane sabanin su sakina duk sun cika palo sun zama manyan hajiyoyi har gara fa,iza yanayinmu daya.sadiya kam ta zama kamar wata goggonmu lol!

Farida ta shigo dakin da sallama na juyo hade da amsawa ta gaisheni snn tace"mama daddy wai kije in kin gama shiri.

Nace"to gani nan zuwa.
Murmushi tayi tace"mama gaskia kinyi kyau sosai don Allah muyi selfie.

Nace"keni don Allah ki rabu dani da wani selfie dinki.
Murmushi tayi ta maso kusa dani ta rumgumeni ta saita camera ta daukemu ta sake karawa zata kara na tureta nace "ke ya isa haka don Allah.

Na fita ta bini a baya tana dariya tace "hmm ai bari naje yola zamusha selfie da sweetyna .

Nace"waye kenan?

Tace"Alhaji ibrahim lamido ....

Da sauri na juyo nace"kinci gidanku.ga tsohonki a palo kije kuyita selfie amma ba nawa tsohon ba.

Dariya taskeyi har muka isa palon ya salman

A tare suka kallemu da munir da alamu suna tattauna wata muhimmiyar magana muka shigo.

Ya salman ya kallemu yace"ya dai na ganku haka?

Farida ta zauna kusa dashi tana dariya tace"daddy munsha selfie ne da mamana.saura kai don kaima daddy ka koma saurayi yau kuma.

Murmushi yayi yace"Hmm ke dai farida ba,a raba ki da shiririta.

Na zauna ina fadin "kinga ma yanxu lokacin tashin su khalil a islamiyya yayi kije ki duba driver ko ya tafi.
Chapter 126 · 0% Book details