← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 128

Sashe 102

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Momy tace"one week in ne se kaje da rumaisa to me zata maka tunda naji kace aiki ne ze kaika ?

shiru yayi ya rasa me zaice don haka tace kayi tfyrka Allah ya kaika lfy ya dawoda kai lfy.in yaso zan duba zuwa nan one week din se ka dauki matarka amma yanxu ba inda zata.

Ba don ransa yaso ba yace "to momy Allah ya kaimu.

Yayinda ya kalleni muka hada ido gwalo na masa na sunkuyar da kai ina dariya kasa kasa.

Gyada kai yayi snn yace"momy don Allah to ko rakiya ne ta min a get zanyi magana da ita.

momy tace "naji kuma minti biyar na baka ka gama magana da ita ka kama hanyarka ka tafi.in ya wuce minti biyar zan fito in sameku kuma kasan sauran zancen.

Yace"to momy.

Yana fita momy ta kalleni tace"ya fara shiga hankalinshi yanzu kam.

Murmushi nayi bance komai ba .

momy tace"tashi kije kuyi sallama.

Na tashi na fita na sameshi yana tsaye rataye da jakansa muna hada ido nayi saurin janye idona na juya masa baya nace"gani.

Shiru yayi kamar bazaiyi magana ba snn yace"hmm baby ina jiye miki tsoron randa zaki shiga hannuna don wlh bazan saurara miki ba saboda kin azabtar dani dayawa.

Murmushi nayi don nasan baya kallon fuskata nace "haka kace to wlh se na gayawa momy abinda kace.

Na fada yayinda nayi gaba da sauri ya bini ya rikeni yace"wasa fa nake miki karki gaya mata don Allah.

kokarin kwace kaina a jikinsa nake saboda yanda ya rikeni sosai ko kunyar driver da mai gadi bayaji.

Muna cikin haka sai ga momy ta fito aikuwa tana ganinmu tace"ok wnn shine maganar da zaka mata din?

Da sauri ya salman ya sakeni ya bude mota ya shiga ya kulle dama driver na jiranshi don haka mai gadi na bude get suka fita .

momy tace"mara kunya ai da ka saya har inzo in sameka.

Muka koma ciki a ranar ya salim yazo ya dauki farida duk da kayanta yace zai kaita gun mimi su dinga wasa bibbiyu.

Nikam ya salman na tfy da kwana biyu na kama rashin lfy ciwon kai daga baya marata da bayana a rana ta hudu kuwa sai amai duk abinda naci sai amai kawai.hankalin momy ya tashi sosai don haka ta kira doctornsu har gida yazo ya dubani bayan ya tambayeni yadda nakeji na fada masa kawai ya jefomin tambaya"yaushene last kikayi menstruation dinki?

Na dan saci kallon momy naga ta kafeni da ido kawai nace"na manta.

dariya doctorn yayi yace "bakiyi ba last month?

Shiru nayi don haka yace zai min gwajin ciki aikuwa yanayi ya kalli momy yace "Hajia cikine!

Dam!naji kirjina ya buga ban iya na dago na kalli momy ba .snn can zuciyata kuma farinciki na shiga yi abin nema ya samu.

Bayan momy ta sallami doctor ta dawo ta kalleni tace"Rumaisa ya akayi hakan ya faru don nasan cikin nan anan abuja kika samu saboda lokacinda kika zo nan kinyi period dinki.gaya min yaushe kuka hadu da salman.

Sosai kunya ya kamani kamar zan nitse momy tace"wato hauka kuka manna min ke da salman kuna ta shagalinku koh ?to meye amfanin zamanki anan ai dana san kun daidaita kanku da tuni na barki kika bishi

Kaina a tsunkuye nace"wlh momy ba abinda kike tunani bane wayo ya min suka hada baki da ya salim yazo ya daukeni ya kaini gidansa shi kuma yaje ya sameni.kuma wlh momy sau dayan ne kawai......

Ta katseni da fadin ya isa .ai zaizo ya sameni daga shi har salim din.

Ta tashi har zata fita ta kuma dawowa tace" to yanxu dai kinji abinda duk doctor ya fada don haka ki kula da kanki sosai don ba ke kadai bane yanzu.Allah ya raba lfy.

Shiru nayi har lokacin kaina a sunkuye murmushi momy tayi tace"meye kuma najin kunya ai ba haramci kika aikata ba rumaisa.yanxu dai gaya min me kike son ci a dafa miki ?

Na danyi shiru snn nace"momy kawai zansha kunu in wanda akayiwa daddy ya rage.

Tace"aikuwa ya kare amma zanje nayi mishi sabo yanxu jirani mintuna kadan .gara na dage wurin kula da ke watakila maigida zaki haifo min.

Ta fita tana dariya nima murmushi nakeyi zuciyats wasai jina nake kamar wacca akayiwa albishir da gidan aljanna.ya salman in yaji wnn labarin ba karamin dadi zaiji ba nasani.

Satinsa daya da tfy ya sake dawowa bamu san zaizo ba kawai muka ganshi bazata ya samemu a palo da momy ina shan kunu don shine kawai abinda raina keso.

Momy tace"salman irin wnn zuwan bazata ko ka buga ka sanar damu.

Yace"wlh momy wani mafarki nayi mai dadi dama ba yau nayi niyyan zuwa ba se gobe.

Momy tace to wani mafarki knn?

Yace"momy mafarki nayi rumaisa na da ciki .

Momy ta harareshi tace "da yake kasan abinda ka aikata kamin ka tafi ba .

Sunkuyar da kai yayi yana sosa keya momy tace"hmm to ai shikenan .mafarkinda kayi gaskiane cikin ne da ita
Da sauri ya dago ya kalleni nikam daure fuskata nayi na danne dariyata naci gaba da shan kunu na.

Dariya yayi yace"Alhamdulillah Allah mun gode maka.

Ya kalli momy yace"momy dolene in baki tukuicin wnn albishir da kika min domin naji dadi sosai wlh.

Momy tace"to maza hanzarta ka bani.

Tashi nayi na wuce daki abuna na barsu a palo hira suka dinga yi da momy kamar ba itace ke ta faman fushi dashi ba.

Har daddy ya dawo ya samesu yace"zuwaira gaskia yanzu kam a bar soja ya tafi da matarsa.

Momy tayi dariya tace"ai dolena in barsu yanxu kam .amma fa kaja mishi kunne kar ya sake aikata wani kuskuren

Daddy yaja kunnen ya salman hade da fadin"kaji ai naja kunnenka da baya jin maganan nan wlh ka kukura ka kuma batawa rumaisa rai sai mun saka tsallen kwado.

Dariya momy tayi yayinda shikuma yace"inshaa Allah dady bazan kuma ba.

Da daddare ya shigo ya sameni har nayi shirin bacci don yanxu da wuri nake jin bacci.

Hawa gadon yayi ya yaye bargon da na rufa ya tura hannunsa cikin jikina yana shafa marana yana murmushi snn ya kalli fuskata nima murmushin nakeyi a hankali ya dagoni ya rumgumeni a jikinsa yace"Alhamdulillah my dear Allah mun gode maka karkiso kiji irin farin cikin da nayi wlh.nan bada jimawa zan sake samun baby.

Ya shiga shafa kaina snn ya dago fuskata yayi kissing din bakina yace"babyna Allah ya miki albarka Allah ya barmu tare.

Nidai bance masa komai ba yace"mene ne kodai har yanzu fushin ne ?pls ki manta da komai rumaisa mu maida rayuwar soyayyarmu kamar nada .

Turo baki nayi nace"yaya ni na daina yarda da maganarka .zaka sa in saki jiki da kai nan gaba kace zaka kara aure......

Da sauri yace"waya ce miki zan kuma yin aure?ni bazan sake yin wani aure ba in Allah ya yarda ke kadai kin isheni dear.

Tabe baki nayi nace"hmmm .

Yace "means baki yarda ba shikenan zaki gani.yanxu abinda nakeso dake kiyi parking din kayanki gobe jirgin safe zamubi na rigada na gyara mana gida yanda zamu sake sabon rayuwa don har nasa an mana saukan Qur,an a gidan Allah ya kade mana dukkan masifu dake ciki don haka yanxu ba ruwana da wani karin aure ke kadai kin isheni babyna. *KI* *YARDA* *DANI*.

Murmushi nayi nace"na yarda da kai yaya hundred % amma don Allah ....

Ya katseni da fadin "magana ya kare dear.

Ya sake kissing din bakina snn ya shafa marata yace"Allah ya raba lfy.

Nace"ameen yayahna.

Daga nan ya sallameni ya fita.

Washe gari kuwa karfe shadaya muka bar Abuja bayan momy da daddy sun zaunar damu sun mana magana sosai.farida mun barta gidan ya salim don sun saba da mimi sosai basa son rabuwa(wnn shine sanadin zaman farida a gaidan ya salim)

Gidan mama muka fara sauka mun sami daddyna ma yazo bayan mun gaisa bamu zauna ba muka tafi gidansu innah to ba laifi ta tarbemu da mutunci amma sam na lura bata wani fara,a duk ta sake sauyawa kuma.sadiya kam bata nan tana cameroo don rashin auren ta ya fara damun innah don haka ta turata kamaru a sama mata maganin matsalarta na rashin samun tsayayyan bazawari.

Madiha kam tana nan don haka tana ganinmu ta hada kayanta wai zata biyo mu yaya salman yace mata ba yanzu ba ta bari tukun sai daga baya haka ta koma daki tana ta tura baki.

Inna kuwa bata ce mana komai ba har muka tafi.

Hmm rayuwa knn gidanmu mu kadai yanzu se munir da hakim da masu aiki.mun shimfida rayuwar soyayya kamar zamu cinye junanmu sosai yaya ya shiga nuna min so da kulawa gashi munci sa,a cikina ba laulayi sosai.

Daga baya madiha ta dawo inda ya salman ya mata jan kunne sosai akan idan ta sake ta min rashin kunya zata bar masa gida kuma ta fitar da miji tayi aure zamanta hakan nan ya isheshi.don haka yanxu rashin kunya ta rage sai dai munafurci kusan kullum tana gidan innah ta kwashi karya da gaskia a kaina ta fadawa innah.sadiya ma ta dora da nata da yake tuni ta dawo daga camaroon.
Kuma taci sa,a tana dawowa ta sami wani Alhaji nasir babban dan kasuwa yana da mata uku da yara goma sha biyar.hmm wayaga sadiya da kishiyoyi Allah dai ya sa ta iya zama da wnn banzan halin nata.tuni maganar tayi karfi don har an daura aure sauran tarewa tace sai ta shirya don haka ta shiga neme neme kullum ana gidan malamai don ance mata gida da kishiyoyi sai ta shirya sosai kamin ta shiga.kuma ita a son ranta Alh nasir ya sota sosai ya kashe mata kudi.

Cikina na wata shidda sadiya ta tare bayan mun gama shan biki tarewan ne sa,adatu ta haihu an sami da namiji mai sunan daddy .ruma ma ta haifo babynta namiji ya salim ya sanya masa sunan ya SALMAN wayyo karkuso kuga farin ciki gun yaya salman na samun takwara.
Chapter 102 · 0% Book details