← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 128

Sashe 80

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk juyin duniyan nan ya salman da ya salim da mmn sakina sunyi amna na ki yarda nan da nan ya salman ya kira mama a waya ya gaya mata komai sunjima suna magana snn daga bisani ya shigo ya samemu ya kalkeni yace"shikenan rumaisa mu tafi zan maida ke gidan naku kamar yadda kk zaba.

Sanyi naji a raina don haka muka tafi gidan mama a motarsa ya salim kuwa sun tafi da mmn sakina.

Muna isa gidan mama na bude motar na fita ko waiwayensa banyi ba na wuce ciki na tadda mama a babban palo tana kwance mai aikinta lami na danne mata kafa.

Sallamata kawai ta amsa yayinda ta dauki key ta mika min hade da fadin " ga makullin dakinki .

Na karba na wuce ina fadin haka kawai ga gidan ubana a zauna ana wulakantani ai da ba yanzu bane.

Na shiga dakin na tarar an share fess an goge koina sai kamshin room fresh dakin keyi gashi ya dauki sanyin ac .

Ban tsaya wata wata ba na wuce toilet wanka nayi da ruwa mai dumin gaske har naji dadin jikina na fito daure da towel ya salman na gani zaune bakin gadon da alamun ya gaji da jirana.

Yana ganin fitowata ya tashi da sauri ya karaso gabana ya zuban idanunsa masu kwarjini snn yace" baby hukuncinda zaki yanke mana knn ? Ban taba tunanin haka daga gareki ba.amma babu komai idan kin huce zan dawo in dauke ki kinji ki kula da kanki da kyau Allah ya baki lfy.

Daga nan ya juya ya fita nabi bayansa da kallo jikina ya mutu sosai hawaye kuwa kamar jira yake nan da nan ya fara zubowa.

Na zauna bakin gado naci gaba da kukan.

_Fans_ _kuyi_ _manage_ _da_ _wnn_ _page_ _ba_ _yawa_ _saboda_ _rashin_ _chagy_ 🤗🤗🤗🤗🤗🤗

hauly ce🥰👍🏻
[10/9, 10:37 AM] +234 703 558 2498: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡73

**************Su innah ba karamin dadi sukaji ba da na koma gidanmu don haka ta kira salman tace masa" Salman kaifa mijin mace hudune kuma Allah ya baka yadda zakayi dai dai gwargwado.don meye zaka tsaya mace na wainaka ? Wlh bari kaji rumaisa bazata taba abin kirki ba nasha fada maka a baya amma baka yarda ba to yanzu gashinan ka gani.don haka abinda nake so da kai ka nemi wata kawai .

Cike da mamaki yace" haba inna ni me zanyi da wani karin aurene yanzu kwata kwata aurenmu baifa yi shekara ba don Allah kima bar wnn maganar ba dadinta nikeji ba.

Tace " hmm aure kuwa dolene ka kara domin bazaka zauna ba haihuwa ba duk sa,oinka sun fara tara zuria kai kana zaune ko alama babu.don haka bari kaji salman ko kana so ko baka so aure zaka kara domin ni shatu bazan zuba ido ina gani Amina da 'yarta suyita cutar da kai ba!

Ran ya salman yayi mugun baci sosai don haka mikewa yayi ya fita ba tareda yace da ita komai ba.

Nidai zuwa yanzu na warware tass har na fara fita.ya salman kuwa kusan kullum sai yazo ya dubani amma bai min batun komawa ba.haka ma mama ko zancen bata taba bani fuska munyi ba.gashi dama wnn cikin nata gabadaya ya maidata wata silent bata son yin magana gabadaya shiru shiru kawai.

Ni kuwa tuni na gaji da zaman gidan namu duk da ban rasa komai ba amma kewar ya salman nake sosai sau da yawa ko bacci gagarata yakeyi.

Ahmad kuwa tunda mahaifinsa yaga abinda salman ya masa hankalinsa ya tashi matuka yace wlh bazai taba barin salman ba sai dai aka mashi sai da mahaifin salimane ya hanashi hade da yi masa alkawarin zai jawa salman kunne.haka kuwa akayi ya kira ya salman ya tambayeshi meya hadashi da Ahmad ya salman ya fada masa komai .koda mahaifin salima yaji cewa Ahmad ne ya nemi rigima don haka ya baiwa ya salman hkr sosai hade da ce masa zaiyiwa ahmad magana .da haka aka gama wnn case.

Salima kam koda taji wnn zancen kuka tayi sosai hade da yiwa Ahmad adduan neman shiriya.

Yau bayan ya tashi daga wurin aiki gidan mama yazo ya sameni zaune akan dining ina cin abinci .

Kallo daya na mishi na dauke idona don yanda naji a jikina.

A hankali nace" yaya sannu da zuwa .

Bai zauna ba ya karaso guna yana kallona yace" ya akayi?

Nace"babu komai ka zauna in zubo ma abinci.

Ya girgiza kai yace " na koshi.

Na kalleshi cike da damuwa nace" daga wurin aiki fa kk tunda naga kaki ne a jikinka.

Yace " hakane amma tuni da baki nan Aisha ce ta dauki dawainyar kawo min abinci a wurin aiki.

Nan da nan naji wani dam! Duk yadda naso in boye kishina abin ya gagara nan da nan na mike fuska daure nace" tunda Aisha ta baka abinci me kuma ya kawo ka guna?

Yace"nazo in duba lfyr ki ne my dear.

Haushi naji sosai nace" naji sai anjima ka gaida gida.

Cike da mamaki yace what korata zakiyi?

Kai tsaye nace " to tunda bazaka tafi ba ni bari na tafi.

Na wuce fuuu da sauri ya riko hannuna hade da fincikoni na fada kirjinsa ya maida hannunsa duka biyu yarumgumeni sosai kamar zai maidani cikinsa inajin yadda numfashinsa ke fita.nima jikina yayi sanyi sosai na kasa rabuwa da jikinsa lumshe idona nayi.

A hankali ya fara magana yace"baby na don Allah kizo mu tafi gida rashinki a kusa dani babban matsalace wlh nayi kewarki don Allah kiji tausayina baby ko kin manta wani irin mutum ne ni?bazan iya jure rashinki a tare dani ba pls ki daure ki manta da komai kizo mu koma gidanmu.

Tunda ya fara maganar sai shashshafani yake tayi ganin ya rikice gabadaya ya manta inda muke har tura hannunsa yayi cikin rigana .......

Da sauri nayi karfin halin tureshi nace" don Allah yaya ka bari in kuma mama tazo ta ganmu fa?

Ya sake janyoni jikinsa yace"aiko ta gani ba matsala tunda ke matatace halaliyata ko dai ?

Ya fada hade da kashe min ido daya

Kauda kaina nayi nace" ni dai bana so ka tafi kawai.

Na janye jikina daga nashi na wuce dakina biyoni yayi da sauri harda maida kofa yayi ya rufe da key

Nan ya fara kokarin cire kakinsa.

Zaro ido nayi cike da mamaki nace"yaya don Allah me kk shirin yine wai ka manta ban gidan surukanka ne?

Saida ya gama abinda ya keyi snn ya iso kusa dani yace" and so what don gidan surukaina ne hakkina nazo amsa ko shima laifine?

Sake baki nayi ina kallon yaya salman .

Shikam kamoni yayi ya zuba min manyan idanunsa da suka sauya kala nan da nan saboda jaraba lol!

Yace"baby kina son ki jefani wani haline ? Nifa gabadaya 2 weeks da ba kya nan dinnan saura kiris ki jefani cikin mummunan yanayi don haka naga bazan iya hkr ba kawai nazo...

Sosai naji tausayinsa amma na danne nace"shikenan kuma sai kazo ka matsamin a gidanmu bana so wlh kar kace zaka taba......

Rumgumeni yayi da sauri yayi kan gado dani muka fada fadon da sauri na fara kokarin kwace kaina ina yaya ni wlh bana so ka barni wai dolene wlh zan maka ihu mama tazo......

Hade baki na yayi da nashi sosai ya shiga sarrsfani yadda yaga dama nan da nan ya rabani da kayan jikina yaja bargo ya rufemu daga nan labarin ya sauya tun ina nonnokewa har naji bazan iya ba ba shiri na shiga tayashi duk mun rikice sai sambatu gabadaya mun tafi wata duniyar ta daban duk mun fita daga hayyacinmu tsawon lokaci muka dauka cikin wnn yanayin ba abinda ke tashi a dakin sai fitar numfashina da nashi. A hankali nikam ido ya raina fata na gaji tilis sai neman kwatan kaina nake yaya kam kamar zugashi nake kara yi a karshe sai da na fara mishi kuka tukun ya rabu dani da sauri ya wuce toilet sai kace gidansa kai namiji ba kunya .

Ba jimawa ya fito ya maida kayansa ya matso kusa dani nikam har lokacin ina cikin bargo duk jikina yayi tsami ya sunkuyo yayi kissing bakina hade da shafa kaina yace God bless you dear na gode sosai bari in tafi magriba ta wuce bamu sani ba.

Binsa kawai nayi da kallo a raina nace"a sauka lfy.

Ya fita da sauri ya kuwa ci sa,a mama bata fito ba don haka palon ba kowa da sauri ya fita.

Tunda ya koma gida ya kasa nitsuwa don haka gidansu ya wuce wurin mmn sakina tunda ta ganshi tasan akwai matsala don haka ta tattara hankalinsa gurinshi tace"ya akayi salman?

Ya dan sosa kai yace"wlh mama ina cikin damuwa har ysnzu rumaisa taki yarda ta dawo kuma goggo Amina taki cewa komai akai hasalima ko daddyn yola bai san da maganar goggo amina bata sanar dashi ba ni mama bansan me nayiwa goggo amina ba ta sauya min.

Mmn sakina tace"ai kaima Salman da naka tun farko nace ma kazo ka gaya wa abbanka wnn maganar kaki sai ma ce mishi kayi rumaisa ta koma gida do tayi jinya ne.ni nasan bazaka iya daurewa ba da tun lokacin ka bi shawarata ka gayawa abba da tuni rumaisa na nan .kuma goggonka Amina ranta ne ya matukar baci da maganganunsu innah ta ya za,ayi rumaisa na cikin halin rashin lfy suje suyita fadan maganganun marasa dadi akanta kaga ai suma basu kyauta ba .

Shiru yayi ya rasa me zaice don tsabar bakin ciki da bacin rai wai ko yaushe inna zata daina irin wadan nan abubuwane oho.

Ganin yana zaune shiru yasa mmn sakina cewa " yanzu dai ka yi hkr nasanme zanyi zanje in sami abbanku da maganar inshaa Allah rumaisa zata dawo kwantar da hankalinka .

Yayi ajiyar zuciya snn yace" yawwa mama na gode sosai.

Da haka ya fita ya tafi dakin innah.
Chapter 80 · 0% Book details