← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 128

Sashe 120

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni ban me suke ciki ba kawai da daddare ya kirani wai inkawo masa twins dinsa.bace aina?

"Dakina mana.
Na kalli agogo snn nace"haba yaya me zai kawo ni wurinka yanxu ina nafisa taxo ta daukan maka su.....

Ya katseni da fadin"nafisa bazata kwana anan yau ba don haka ki kawo min twins dina su tayani kwana ina jiranki yanzu.

Ko kan nayi magana ya kashe wayarsa.don haka dole na tashi zuciyata cike da tunani kala kala na dauki yaran duk bacci suke na tafi na kai masa su tuni yayi shirin bacci yana rumgume da fillow

Ya nuna min gefensa alamun na kwantar dasu.
Ina kwantar dasu na juya zan tafi da sauri naji caraf ya riko hannuna a hankali yace "ina zakije?

Nace"dakina mana?
"saboda me ?ya jefo min tambayar yayinda yake kallona sosai.

Nace"haba yaya kasan fa bana girki har yanxu.idan na kwana anan ya nafisa zataji?kuma kaga duk abinda ta fada tana da gaskiarta don haka ni bana son rashin hankali.

Fincikoni yayi na fada kirjinsa yace "ni ina son tashin hankali.

Ya fada yana kallona ido cikin ido da sauri na janye idona daga kallonsa ba shiri naji ya hade bakina da nashi wuri daya ya shiga sarrafani son ransa gabadaya ya rikice se sakin numfashi yake .ganin yana kokarin wuce gona da iri yasani fadin"wayyo yaya ka bari ko ka manta banda lfy.

Dakatawa yayi da abinda yakeyi a hankali ya sakeni yana sauke numfashi idonsa a lumshe.

Nikam da kyar na lallaba na fita na barshi da yaran na koma daki da yake suna shan madara na tanadi komai na ajiye musu na dawo nayi kwanciyata.
Washe gari da asuba ya shigo dakina ya tasheni hade da fadin zan tafi masallaci kije ki kula da yaran karsu tashi suyi kuka.

Daga nan ya fita.nima ba bata lokaci na tashi na tafi sashin nasa har lokacin bacci suke.

Nima ba jimawa baccin ya kuma dibana koda ya shigo bai tasheni ba shima baccin ya koma.

Sai karfe goma muka tashi saboda yunwa da kuma kukan su hanif don tuni suka rigamu tashi .

Part dina na koma a sace kar nafisa ta ganni .larai tayiwa yara wanka nima nayi snn na basu nono duk bacci sukayi ni kuma nan na samu daman fara tawa kwalliyar.

Ya salman ta kira wayata wai nazo na daukan masa ajiyarsa zai fita.yana fada ya katse kiran don kar na kawo excuse

A gurgujuje na karasa abinda nakeyi na tafi sashin nasa ina duba wurin ajiyan kudin sukace daukemu inda kk aje.

Da sauri na kalleshi nace"au ka canzawa jakar wurin zamane?

Kai kawai ya girgiza min yana daura agogonsa.

Nan da nan naji kaina ya sara .

Wasa gaske muka nemi jakar kudi kaf dakin muka rasa tirkashi!!!

Zamewa nayi na zauna kasa na dafe kai hawaye ya wanke min fuska nan da nan............

Fans kuyi hkr da rashin jina kwana biyu ban cika jin dadi bane🥰.need your prayers my sisters🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻

Hauly ce🥰🙏🏻
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡100

*********Karasowa yayi gabana ya tsugunna ya zuba min ido fuskarsa cike da damuwa.

Hannu ya mika ya dangwali hawayena dake sauka bisa kumatuna.

Ajiyar zuciya yayi a sanyaye yace"Rumaisa me kike tunani?kina ganin zan zargeki ne akan batan wnn kudaden?

sai lokacin na dago kaina na kalleshi nace"ba haka bane amma na shiga damuwa ta yaya za ayi jiya jiyan nan na ajiye kudin nan kuma ba wanda ya shiga dakin nan daga ni sai kai snn a rasa wnn jakar.bayan gidan nan........

Hannu ya daga min snn ya tashi tsaye nima mikewa nayi ina kallonshi hannunsa ya zuba cikin aljihu ya na tsaye shiru tsawon wasu lokuta snn ya gyada kai ya fice abinsa.

Nikam hankali na ya tashi kwarai na dada birkita dakin ina neman jakar kudi amma ina bangani ba.

Yinin ranar gabadaya mun yishi ba dadi a gidan dagani har yaran nan.
Farida kasa hkr tayi tace"mama kinsan me kudin nan ko shakka banayi aunty nafisa ce ta dauka....

Harara na watso mata nace"rufe min baki kin ganine? Ba fa nason abinda kikeyi.ai jiya kwata kwata nafisa bata ma kwana a dakinsa ba .

Munir yace"Mama amma maganar Aisha da kwai ksmshin gaskia domin fa kinsan gidan nan kaf kewaye take da securities kai bama gidan nan kadai ba anguwan gabadaya saboda barayi shakkan anguwan nan sukeji saboda sunsan gidan daddy na nan.don haka ba yanda za,ayi har a shigo a dauki kudin nan a fita dashi ba wanda ya sani kai impossilble wnn satan a cikin gidan nan ne kuma kudin nan yana nan cikin gidan.

Farida ta gyada kai tace"oo hmm

Ta matso kusa dani tace"mama wlh na gaya miki ko nafisace don nasan wlh ba don Allah ta auri dad ba dama tana son kudinsa ne kawai.

Jikina ya mutu sosai kaina ya kulle gaskia banason in zargi nafisa don sanda aka kawo kudin nan bata nan kuma bata kwana a dakinsa ba bare tasan dasu.

Farida tace"mama ki barni inje in sameta wlh wlh wlh sai ta fitar da kudin nan ko bata so don ita ta dauka ko shakka banayi.

Kafin nayi magana munir yace"no bazakiyi haka ba Aisha ki barta a hankali ake bin komai.

Farida ta dan bata fuska .
Nikam tashi nayi don naji kaina na min ciwo na koma daki nayi kwanciyata don su hanif ma se baccinsu suke.

ina tashi munir ya taso yazo kusa da farida ya zauna ya dan zuba mata ido snn yace"me nene na bacin rai kuma?

Tace"inajin haushin yadda kuke min ne kai da mama.wlh da zaku ban dama abubuwa da yawa da basu faruba a gidan nan.

Ba shiri munir ya dan saki kasaitaccen murmushi yana kallon yanda farida ke cika tana batsewa.

yace "to shikenan na baki dama kije ki same ta ......

Ai bai rufe baki ba farida ta tashi da sauri zata wuce part din nafisa.

munir yayi masa ya kamo hannunta ya jawo ta baya yayinda ya juyo da ita suna fuskantar juna yace"baki fada min me zaki gaya mata ba in kinje ?

kai tsaye farida tace"cewa zanyi kudin daddy da ta dauka ta dawo dashi ko kuma jikinta yayi laushi.

Dariya munir yayi sosai yayinda farida ke binsa da kallon haushi .

Janta yayi suka zauna snn ya dan nitsu ya kalleta har lokacin hannunsa na cikin nata yace"my dear farida meyasa kika cika saurin fushi da yanke hukunci ba shawara ne?

shiru farida tayi munir yaci gaba da fadin "ki bar wnn maganar kudin nan insha Allah ko sisi bazai yi ciwon kai ba kudin daddyne fa hmm.

ya fada yana kashe mata ido daya snn ya danja hancinta wanda har zufa yakeyi tsabar masifa.

Sun danyi shiru tsawon mintuna biyar snn ta zame hannunta daga cikin nashi ta kalleshi shima ita yake kallo tun dazun gabadaya ya kasa dauke idonsa ga barin kallonta.

A hankali tace"lfy?

kai ya gyada mata snn yace"ya maganar mu .....

Da sauri ta sunkuyar da kai ta rasa me zata ce masa ita gabadaya abubuwanda ta masa yasanya takejin kunyarsa da nauyinsa a yanxu.amma tabbas zuciyarta tana sonshi ta rasa dallilinda yasa tayi soyyayya da farouq domin gaskia munir yafishi komai ......

katse mata tunanin yayi lokacinda ya matso da fuskarsa dab da nata saukar numfashinsa taji akan fiskarta

A hankali yace"Aisha ki daina boye boye ki fada min gaskia abinda ke ranki na baki nan da one week kije kiyi tunani .

daga nan tashi yayi ya fita tabi bayansa da kallo har ya bace snn tayi murmushi tace"ya munir ina sonka kuma insha Allah kaine......

duk da ita kadai ne saita tsinci kanta da jin kunya don haka tashi tayi ta tafi dakinta.

Haka Oga ya dawo gidan bai samu kowa ba part din nafisa ya wuce kai tsaye ya sameta a bedroom tana kwance hankalinta na kan latse latsen waya ganin ya salman ya sata tashi bakinta har rawa yake tace"yaya sannu da dawowa.

Bai amsa kawai kai tsaye ya fara magana"Jiya na shigo da kudina gidan nan amma se na nemesu yau na rasa.....

Zaro ido nafisa tayi tace"Subhanallah anya kuwa yaya ka duba da kyau? Ni kaga ma bansani ba don koda na dawo ma rufeni kayi da fada harda mari na kayi ka ce na tafi na bar maka part dinka.....

Daga mata hannu yayi yace"enough bana son dogon surutu abinda nakeso dake kawai ki tattara kayanki ki bar gidan nan har sai na nemeki.

Ta zaro ido hade da fadin what! Yaya me nayi?

Kai tsaye yace"sau nawa nasha warning dinki akan in bana gari ki daina fita ?don haka ya isheni rainin hankalinki.karki yadda na dawo dakin nan na sameki.

Yana fadin haka ya juya ya fita.

Tabe baki nafisa tayi snn ta saki murmushi tace"gaba ta kaini gobarar titi a jos Allah sa ma ka bini da takardata.

Ni kuma tunda naga dawowarsa ta window din dakina don haka na tafi dakinsa amma ban sameshi ba kuma alamu ya nuna baya toilet ma.don haka na zauna jiransa .

Har na gaji zan tashi sai gashinan ya shigo dakin kallona yayi yace"ya akayi my dear

sauke ajiyar zuciya nayi nace "sannu da dawowa yaya

Da kai ya amsa na karasa gabansa nace"ya maganar kudin nan ne?

Yace"no karki sa kanki a matsala kudina suna nan bazasu bata kuma zasu dawo insha Allah.

Binsa nayi da kallo na rasa me zance to.

Nafisa kuwa tuni driver ya sauketa gidansu inna kawai sai ganinta inna tayi da lodin kaya gaban inna yayi mummuna faduwa tace"lfy nafisa na ganki da jakar kaya......

Nafisa ta fashe da kuka tace "goggo yayana ne yace in bar masa gidansa.

Tashin hankali innah ta dafe kirji tace"na shiga uku ni shatu to me kk masa ?

Nafisa tace"bai gaya min ba nima.

Inna ta dan runtse ido tace lallai salman baida mutunci zai zo ya sameni ne kuma wlh bai isa ba.

nafisa kuwa kuka ta shiga yi sosai .

inna kuwa nemanshi tayi a waya tace yazo .
Chapter 120 · 0% Book details