← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 128

Sashe 79

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban rufe baki yaya ya daukeni da wata mari har saida na yanke numfashina tsabar azaba idona tuni ya kawo duhu na dafe gun .

Cikin tsananin bacin rai yace"karya zaki min .saboda kinga bana gari ! Meye wnn?

Ya fada yayinda ya bude jakar ya fitar da wasu kanan pills na family planning ya zube su akan gado snn ya fitar da hotunanmu nida ahmad kuwa birjik tun na da can abin mamaki harda na ranar da ya tareni ya rike hannuna ina kokarin fizgewa .ga kuma pant da breziya duk a cikin jakar .

Dora hannuna nayi akai nace"na shiga uku wlh Ahmad sharri yake min don naki sauraransa yaya ka yardada.........

Girgiza kai yayi yace" Rumaisa ashe ni kadai nake haukana dama abinda kike aikatawa knn wato baki rabu da wnn dan iskan bako ?

Cikin tsananin kuka na durkusa gabansa nace" yaya wlh wlh wlh ......

Ya katseni ta hanyar daga min hannu cikin tsawa yace" karki kuskura kice wani abu kawai ki saurari hukuncinda zan miki!

Da sauri na mike a tsorace kar dai yaya sakina zaiyi da kuwa na shiga uku!

Jinayi kirjina ya fara toshewa numfashina ya fara daukewa yayinda marata ta fara wani irin azababben ciwo .

Nan da nan na sake durkushewa ba shiri na shiga janyo numfashina da kyar !

Duk da tsananin bacin rai da yake ciki bai hanashi bai hanashi kulani ba don da sauri ya dagani ya zaunar dani bakin gado ya dauko inhaler na ya mika min hannuna na rawa na karba.

Daga nan bai kuma ce mun komai ba har sai da yaga numfashina ya daidaita snn ya jawo stool ya zauna muna fuskantar juna yace" are you ok?

Kai kawai na iya daga masa.

Yace " ina son ki gaya min gaskia idan kika kuskura kk min karya wlh sai nasa bindiga na harbeki ki mutu nd no one will ask me why .

Zaro ido nayi yayinda ya ce min " yes! Ina son ki fadamin yaushe kk fara haduwa da Ahmad ? Snn me ya hadaki da family planning pills ?

Ajiyar zuciya nayi snn na fara mishi bayanin komai daga ranarda muka fara haduwa da Ahmad har kawo sanda a fizge jakata.

Ido ya zuba min tunda na fara magana har na gama ya jima yana nazarin maganata snn daga bisani ya mike a fusace ya fita koina ya tafi oho.

Nidai a inda nake zaune jina nayi na jike da sauri na tashi don ganin me yeke faruwa dani .

Jini ne na gani gabadaya ya bata bedsheet din .ga wani irin ciwo da marana keyi jini kuwa ina daga tsaye yake bin kafana .

Durkusawa nayi a wurin na kama kuka ina rikeda mara .bansan tsawon lokacinda na dauka ba har jinai jiri yana dibana sannu a hankali na sulale na fadi kasa a sume!!!!!

Hauly ce🤗🥰👍🏻
[10/9, 10:37 AM] +234 703 558 2498: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡72

****************Ba yanda ya salim baiyi ba don ya hana ya salman zuwa gun Ahmad amma abun ya gagara ce mishi yayi "salim don Allah don Annabi ka rabu dani ko ba a gabanka bane dan iskan nan ya turo da jaka a bani ka manta ne?

Salim ya girgiza kai yace"ban manta ba salman amma kasan ba kyau yanke hukunci ciki fushi yana haifar da dana sani kayi hkr kazo kaji abinda........

A zuciye ya salman yace" kaga salim ni banson ranka ya baci kwata kwata don haka ka rabu dani babu ruwanka cikin wnn maganar kaje ciki ka kula da rumaisa.

Yana gama fadin haka ya wuce motarsa da gudu ya fizgi motar kowa sai gudu yake yana matsawa kar a bugesu.

Ya salim kam girgiza kai yayi cike da damuwa yace" Allah ya tsareka salman.

Ya shigo cikin gida side dinmu tun a palo yayita sallama shiru ya zauna zaman jiran ko zan fito yaji shiru don haka kai tsaye ya shigo dakina ganin halinda nske ciki yasa da sauri ya fita ya je gida ya kira mmn sakina yace tazo a tafi asibity.

Nidai bansan a wace duniya nike ba.

Ya salman kuwa yayi sa,an samun Ahmad a guess house dinsa yana zaune da abokansa a harabar gidan sunata hiran duniya .

Ai baiyi wata wata ba ya iske shi a wurin ba tare da tunanin komai ba ya hau kansa da duka da naushi yana fadin " me ye hadinka da matata!

Abokan Ahmad da kyar suka kwace shi a hannun ya salman duk ya mishi jina jina abun babu kyan gani!

Anan ya mishi warning sosai snn ya kama hanyarsa ya tafi ya barsu.

Dole aka tattara Ahmad aka kaishi asibity don yaji masa ciwo sosai.

Ni dai koda na dawo hayyacina na ganni kwance a gadon asibity banyi mamaki ba .don gashi har ma da karin jini aka min.

Hawayene ya cicciko idona nan da nan dana tuno cikin jikina nasan babu shi a yanzu cikinda ko shi ya salman baisan da zamanshi ina ta son in mishi albishir din yau sai gashi ya janyo sanadin mun rasa cikin .

Ya salim ne da mama sai sannu suke min ina amsa musu da kai.

Muna nan innah suka shigo da sadiya sai da naji gabana ya fadi wlh.

Bayan an gaggaisa suka jajantawa mama kamar abin arziki inna ta kalleni tace" Rumaisa ya jikin?

Nace da sauki innah.

Tace" kinga abinda nake fada muku ko keda salman kunki yarda matsalar haihuwar nan daga wajanki ne sau uku knn kina bari ba tare da wani kwakkwaran dalili ba don haka gaskia ni a shawarce ina ganin gara ku kyale salman ya kara aure domin yaga kwansa a duniya.duk sa,o,insa sai haihuwa suke don haka a duba dai a masa adalci duk da cewa nasan maganata zata muku zafi amma dai gaskia dayace kuma dole a fadeta a duk lokacinda bukatan hakan ta taso.

Shiru mukayi dagani har mama ba wanda ya tanka ya salim ma haka .

Sadiya kuwa cewa tayi " a duba dai ayima ya salman adalci.......

Ya salim ya katseta da fadin " ke yi mana shiru dan Allah waya sako bakinki?

Turo baki tayi inna tace" ai gaskia ne sadiya take fadi salim .

Ya salim yace" amma inna ai naga haihuwar nan nufin Allah ne kuma rumaisa ba ita ta dorawa kanta lalurar ba......

Mama ta katseshi da fadin" salim don Allah ka bar wnn maganar kira min rabi ni tfy gida zanyi.

Ya salim ya fita nikam da tunda inna ta fara magana nake zubar da hawaye sai yanzu nace" mama dan Allah karki tafi ki barni.

Tace" ga rabi zata kula dake rumaisa nima bana jin dadine kiyi hkr sai gobe zanzo Allah ya baki lfy.

Daga nan fita tayi inna ta tabe baki tace" hmm ummah ta gaida assha .

Snn ta kalleni tace kekuma bari kiji na gaya miki ko zaki mutu salman aure zai kara don bazaici gaba da zama dake da wnn lalura taki ba sadiya tashi mu tafi.

Sadiya ta kalleni hade da fadin "sai anyi magana ki zauna kina ma mutane kukan munafurci yaya aure zaiyi ba fashi ehe!

Ni dai ban musu magana ba suka kama hanyarsu suka tafi dama ba zuwan Allah da annabi sukayi ba.

Bayan sallar isha ya salman ya shigo tunda na ganshi na juyar da kaina saboda wani irin haushinshi danake ji yau na daban ne.

Bayan sun gaisa da maman sakina fita tayi ta bamu waje.don haka ya samu damar zama kan gadon kusa da kaina yace"Rumaisa ya sannu ya jikin?

Kamar badani yake ba shiru na masa kuma ban juyo ba.

Shima shirun yayi tsawon wasu mintuna snn yace " kiyi hkr rumaisa don Allah raina ne ya baci dazun ba wai zarginki nake ba .

Yana ffadin haka ya juyo da kaina a hankali yana kallon fuskata nikam rufe idona nayi don ko ganinsa banson yi.

A hankali yace" pls say something baby

Shiru na masa still.ya sauke numfashi yace " baby bana son kiyi fushi dani kiyi hkr kinji don Allah ki bude idonki ki min magana pls ba don halina ba.

Sai lokacin na bude idona ba tare da na kalleshi ba nace" ni ka rabu dani kawai inji da abinda yake damuna yaya tunda nayi aure zuciyata bai huta ba kullum a cikin matsala nike yaushe ni zan sami farin ciki a rayuwata ? A tunani na koda duk duniya zasu zargeni kai bazaka zargeni ba yaya amma sai gashi lokaci guda ka juya kamar baka sanni ba yanzu dubi halinda ka jefani a ciki ? Snn ga gorin su innah da wanne kuke so naji? Ina kuke son na saka raina?

Na fada cikin matsanancin kuka. sassauta murya yayi yayi yace " kiyi hkr rumaisa tabbas nasan kina cikin wani hali amma ki min afuwa ......

Girgiza kai nayi nace" ya isheni haka ni gabadaya yanzu bazan iya wani hkr ba kawai ka rabu dani kaje kayi wani auren ko mahaifiyarka zata sami farin ciki......

What! Ya fada cike da mamaki yace " rumaisa kece kk irin wnn maganganun.....

Zuciyata kamar zata fashe nace " nima fa zuciyane a kirjina kamar kowa yaya don haka kawai ni ka rabu dani zama da kai ya isheni gabadaya daga nan asibity gidan mu zan wuce ko zuciyata zata huta.

Na karashe maganar da kuka sosai.shiru yayi hankalinsa a tashe ko kadan bazai iya juran kukana ba

Rumgumeni yayi a jikinsa yace "haba baby ki daina kukan nan don Allah wlh yana matukar daga min hankali bazaki gane bane .

Haka yaci gaba da bani hkr yana rarrashina nidai ban kuma ce masa komai ba ganin nayi shiru ya sashi tunanin na huce don haka ya min sallama ya tafi.

Washe gari da aka sallameni nace ni bazan koma gidan ya salman ba gidanmu zan tafi tunda ga gidan ubana na nan a garin nan!
Chapter 79 · 0% Book details