← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 128

Sashe 73

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta dan waiga snn ta kalleni ta sassauta murya tace " in ba damuwa kema ki tashi mana ki shiga malamai ki fara neman taimsko.....

Da sauri nace " subhanallah ! Ni bazan iya biye biyen malamai ba kuma Mamana da dad dina sunce idan nabi malamai basu yafe min ba duniya da lahira.

Tace " to Rumaisa ya zakiyi da wnn babban alamari ai gara ki tashi ki nemawa kanki mafita.

Nayi murmushi nace " karki damu na mikawa Allah dukkan lamurana kuma na zuba ido kema ki zuba very soon zakuga ta inda Allah zai saka min!

Jikinta a mace tace " hakane.

Da haka ta sallameni ta tafi ko rakata banyi ba nace a raina " dangin munafukai kawai.

Ta zo da kwana biyu kawai ranar sai ga khabirat ina kitchen nema ina shiryawa ya salman lunch don ya dawo ya shiga wanka naji ana knocking na kofa don haka naje na bude kawai na ganta tsaye cikin kananan kaya ruguna da wando taci kwalliya har ta gaji ido a tsassaye gashi ta kara eye lashes snn tana ta faman taunan chewing gum .

Ganin na bude kofa yasa ta kalleni sama da kasa snn tace " gunki nazo .

Banyi magana ba na juya ta biyoni a baya .

Ba tare mun zauna ba na kalleta nace" lfy me ke ......

Da sauri ta katseni da fadin ke don Allah ya isa ba surutun babzanki nazo ji ba nazo inja miki kunne a karo na biyu ki daina zama da wasu kina zagina idan kin isa mace ki yi yadda duk zakiyi ki rabani da mijinki ba wai ki dinga zama kina zagina ba.

Tunda take maganan kallonta nake cike da mamaki .taci gaba da balbali tana zagina .

A hankali nace kinga malama...

Hannu ta daga min tace " ki daina wani ce mun malama khabirat sunana...

Nace " hmm ai bana tuna sunanki ba shiyasa nake ce miki malama ...

Harara ta watso min hade da isa dab dani tace " idan bazaki iya kirana da khabirat ba sai kice mun farkar mijinki!

Muna cikin haka ya salman ya fito ya samemu ya kallemu yace " lfy ?

Kamin na bude baki nayi magana kawai ta fashe da kuka ta isa gabanshi tana cewa " my love matarka ta tsaneni duk inda taje zagina take waini karuwa har take gayawa aunty silfa wai zatayi komai akaina domin taga ta rabamu don Allah suleyman ka roketa kar ta rabamu wlh ina sonka kaima ka Sani I love you so much!

Ta fada yayinda take kokarin shigewa jikinsa bansan lokacin da nayi sauri nasha gabanta wani irin zafi nake ji a zuciyata a fusace na nuna mata kofar fita nace " kinga ki fitan min a gida kije waje ki jira har yaje ya sameki !!

Cikin kissa da kisisina tace " my love kana ganinta .......

A hasale na dauke fuskarta da mari nace " I said get out ! Kinsan Allah idan baki fita ba sai na miki mugun illah domin I zuwa yanzu kin kaini bango kin kureni.

Dafe kunci tayi ta na kalleni cikin mamaki tace " what you slap.....

Na katseta da fadin " yes and am ready to do it again idan har baki fice min a gida ba.idan ke baki San koni wace ce ba ki tambayeshi zai fada miki don na lura kinai mun kallon wawiya bagidajia ko ?

"To wlh idan har kin cika mara kunya ki tsaya ki jirani har na fito kinga yanda zan yi dake jarababbiya dangin munafukai kawai.

Da sauri na wuce kitchen ya salman kam yana tsaye kyam kamar an dasa bishiya ya rasa me zai ce mana.

Tabaryata na dauka na kirban sakwara na fito a guje na nufo inda take sai dai nayi rashin sa,a ina fitowa ta ganni a tsorace ta zaro ido hade da sakin ihu ta kamkameshi .

Yayinda sai a lokacin yayi maza ya rikeni a fysace hade da kwace tabaryar ya kalleni fuska daure yace " yanzu rashin hankalinki har ya kai haka bansani ba ? Kasheta zakiyi koh?

Nima ba tare da Tsoro ba nace" ka fada mata ta fuce min daga gida kawai .

Ajiye tabaryar yayi ya kalleta kamin yayi magana ta sake tfy zata fada jikinta.

Yayinda ni kuma na shirya tsaf don yi mata dukan tsiya in ta tabashi.

Aikuwa da sauri naga yaya ya hankadeta sauran kadan ta fadi bai saurara mata ya dinga daukar fuskarta da mari har sai da ta fadi kasa a gigice tana wayyo Allah idona suleyman idona bana gani

Bakinta ma ya fashe sai jini

Sunkuyowa yayi ya dagota yace " ko ba kya ganina nasan kina jina don haka bari na maki last warning khabirat daga yau bani ba ke na TSANEKI bana son sake ganin ki a RAYUWA ta ki fita anan.

Ya fada cikin tsawa da daga murya.

Kuka ta shiga yi sosai tana sambatu da yaransu ko me take fadi oho.

A fusace ya fizgo hannunta ya jata yayi waje da ita snn ya dawo ya maida kofa ya rufe.

Nikam mamaki ne sosai bayyane a fuska ta.

Ina ganin shigowar sa na juya jikina a mace zan tafi daki

A hankali ya kira sunana RUMAISA!

Tsayawa nayi cak ba tare da na juyo ba.

Har ya karaso gabana yanayinda na ganshi ya tabbatar min ya yi nadaman abinda ya faru.

Da sauri na fada kirjinsa na fashe da kuka mai tsima zuciya.

Rumgumeni yayi sosai yana Shafa bayana alamun rarrashi .don ya kasa cewa komai baisan ta inda zai fara bani hkr ba..............

🤦🏻‍♀ *fans* *kuci* *gaba* *da* *mun* *uzuri* *bamuda* *wuta* *ne* *am* *sorry* 🤗🤗🤗🥰🥰🥰🥰🥰

Hauly ce🙏🏻🤗🥰
[9/25, 6:22 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*KYAUTAR_* *SHAFI* *NA* *MUSAMMAN* *A* *GARKEKU*

*INTELLIGENT* *ASSO* *GROUP* 1

Maman sadeeq🥰
Ummin Khadija
Nafeen nura
Hebbert
Aysha A Umar
Asma'u
Haleemath
Ummu suhaima
Ummansukhaina
Reemat
Ummu khalifha
Aisha
Husnah
Umma salma@
Mum nawwal
Hussaina
Farhat 'yar baba

*INTELLIGENT* *ASSO* *GROUP* 2

Zubaida minna
Rukayyat
Rukayyah Musa
Bintu
Amysher
Mmn mahamud
Aishatu
Maman zahra
Aisha Aliyu🥰
Maman saleem
Murjanatu yahuza
Maman sayyeed
Hussainah
Ismajee
Zeemah Ilelah
Habiba Ahmad
Ameenah uthman
Ummu Ansar

Duk Wanda bata ji sunanta ba tayi hkr ba haka naso ba don Allah .amma dai zuciya ta tana tare da ku masoyana hauly ina yinku over 🥰🤗

_Na gode sosai da irin kaunar da kuke nuna ma wnn littafi RUMAISA SALMAN ina ganin comments kuma ina matukar jin dadi Allah ya saka da alkhairi Allah ya bar kauna da zumunci mai dorewa🙏🏻🥰🥰🥰🥰🥰🥰_ *Wnn shafin nakune kuyi duk yanda kuka dama dashi👌🏻*🤗

*PAGE*➡ 67

**********Rabuwar ya Salman da khabirat yasa hanakalina ya kwanta sosai domin yaya ya dawo da soyayya da kulawa da yake min.

Khabirat kuwa ansha case da ita sosai akan marinda yaya ya mata wai wlh bazata yarda ba sai taje gaban manya an bi mata hakkinta.da kyar case din ya mutu don yayanta hassan yaki ya bata goyan baya a karshe ma korarta yayi harda matarsa silfa ma da ya fahimci itace take zuga ta ranar taci dan banzan duka a wajansa ya ce sai dai kome ma a masa daga karshe duk ya korasu dama ba suda yara don haka shi kadai ya rage a gidan.

Na kira mama da aunty samira na sanar dasu mama kam a lokacin suke shirin fita Dubai da daddy wai daga can ma zasu wuce umrah a can zasuyi azumi.

Murmushi nayi a zuciyata nace " hmm mama da daddy masoyan asali.

Shigowar ya Salman yasani juyowa da sauri na tafi na fada jikinshi ina murmushi .

Rumgumeni ni yy sosai yace " baby sai sallama nike tayi tun a kofar Palo.

Na dago kaina hade da fadin wlh yaya banjika ba sannu da dawowa yayana.

Murmushi yayi snn ya sumbaci bakina yace " thank you babyna.

A hankali na fara balle masa ma ballin rigarsa .

Saida na gama cire masa komai snn na kawo towel na bashi nace "asha wanka lfy bari in shirya mana dining.

Har zan wuce ya jawoni hade da fadin baby na gaji fa sosai bazan iya yin komai ba kuma kin Riga kin saba min .

Nace " hmm naki wayon sai dai in ka min alkawarin baza ka jikani ba.

Yace " bazan jikaki ba baby gudun kar ciwon ki ya tashi gashi kwanan nan sanyi ake sosai .

Nace " to muje.

Bayan yayi wanka ya fito na sake taimaka mishi ya shirya snn muka tafi Palo muka ci abinci .

Anan muka shiga hira ina kwance kan cinyarsa.

Nace" yaya mun kusa fara service fa.

Yace "aina zakiyi a kano ko nan?

Nace " gaskia ni yaya bazan iya yi anan ba bansan kan Lagos ba.

Yace " ai ke dama 'yar kauye......

Da sauri na zumbura baki hade da tashi daga jikinsa nace " yaya ni fa banaso

Dan dariya yayi yace "sorry sorry bazan kuma ba.yanzu zo muje ciki na baki labari mai dadin gaske .

Nace " fara bani anan.

Yace to shikenan.

Daga rigata ya Shafa cikina snn yace " yau so nake mu samo baby insha Allah.

Murmushi nayi nace "Allah yasa yayanah yanda kk son haihuwan nan Allah ya bamu yara na gari masu albarka.

Ya Shafa kaina hade da sakin murmushi yace " ameen my dear.

Mama da daddy kam ana Dubai ana shan love.don tunda suka maida aurensu bai samu yanda yake so a gurinta sosai ba don taki tarewa a yola shikuma yana dan jin nauyinsu Abba gashi bazai iya jira a gama gininsu na kano ba don haka kawai yayi shawarar dauketa daga kasar ma gabadaya.

Aikuwa tun mama na dan jin kunya dole ta saba basu fi sati biyu a Dubai ba suka shiga gwadawa juna tsantsar soyayya.

Aunty samira kuwa tana nan sai kewar daddy take dan bata son yayi nitsa da ita.

Watansu daya a Dubai suka tafi umarah.hmm rayuwa knn.
Chapter 73 · 0% Book details