Sashe 15
Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zuciyata ta shiga bugawa na rasa dalili sai naji raina ya mugun baci tashi nayi a fusace ganin sun bini da kallon mamaki yasa nayi saurin wayancewa nace kuna zaune dare ya tsala so kuke mu makara alhalin nace muku ina son zuwa kasuwa gobe kuma ma zan yi bako daga Kaduna.
Ganin har lokacin bina suke da ido yasa na rasa me zan yi kawai na dauki maganin sauro na spray na wuce daki da sauri tuni faiza ta mike ta biyoni tana rumaisa ki tsaya zan fesa.....
Fuuu na wuce ko kulata banyi na shiga daki na kama fesawa ba kakkautawa raina a bace sosai
Da gudu faiza ta shigo ta kwace ranta a bace" rumaisa me yake daminki kin manta kina da asma ?
Taja hannuna da sauri tace " mu je Palo.
Ko kamin mu iso Palo tuni numfashina ya carke anan na zube da kyar nake fizgar numfashina
Gabadaya suka rude sakina ta dubi agogo karfe sha biyu saura tace " innalillahi bari in kira ya salman.
Ta dauki waya faiza kam kuka takeyi don ganin yadda nake numfashi gani take kamar bazan kai labari ba.
Anci sa,a ya dauka cikin bacci sosai yace" sakina lfy ?
Jikinta na rawa tace ' yaya rumaisa ne.... Gata nan ......
Nan da nan ya fahimceta yace " shikenan gani nan yanzun nan.
Aiko minti biyar baiyi ba sai gashi yana buga kofa nikam ji nake kamar bazan tashi ba.
Sakina ta bude da sauri don tafi fa,iza karfin hali.
Ba tare da Neman Karin bayani ba daukana yayi cak kamar wata yar baby kayan baccine a jikina Riga da wando baiko kula ba yayi waje dani yanacewa sakina zo muje faiza ki biyomu ki rufe gidan.
Abu kamar da wasa har ya kaimu ga saida aka sa min oxygen
Ya salman ma ya tsorata sosai ko zama ya kasa yi yana hango doctor zai tareshi ya kama tambaya.
Sai kusan asuba aka barsu suka shigo banma Sani ba nikam.
Ya kalli sakina yace " sakina ya akayi hakan ta faru ?
Tace " kawai yaya muna hira a Palo ta dauko maganin sauro zata je ta fesa a daki shine faiza ta bita ta kwace amma har ta rigada ta feffesa ma shine faa ta fadi numfashinta ya kama daukewa.kuma mun nemo inhaler dinta bamu gani ba.
Yace" tasha maganinta ?
Tace" aa bata sha ba tace taji sauki
Shiru yy ya zuban ido sannan daga bisani ya kalli agogo ya tashi yace " bari in je masallaci.
Ana idar da sallar asuba saiga mutanen gida sunzo tare da faiza Wanda ko bacci ya gagareta yanzun ma da tazo taga halinda nake ciki kuka ta shiga yi tana " sakina har da oxygen aka sawa rumaisa?
Ya salman ne yace" suje waje su zauna dasu sadiya.
Karfe shidda mama tazo don Abba ya fada mata banji dadi ba.itama ta tsorata ganin halinda nake ciki.
Kiran salman ta yi suka koma gefe ta na tambayarsa ya fada mata.
Tace" baka gani ba abinda nake gaya maka rumaisa batada hankali ita take jawo wnn ciwon da karfin tsiya tazo tn wahalar da mutane .
Sunjima suna tsaye
Sadiya kam mamaki ne ya kamata yadda taga ya salman sunyi gefe da mama suna magana zata so ace taji meyene don taje ta gayawa innah.
Sai da nayi sati a asibity sun tabbatar na warware sannan suka sallamoni mama ta dinga ja min kunne fada ta yi min kaman zata dakeni daga nan sukayi sallama da yaya salman ta tafi da driver dinsu ni kuma mu ka dawo a motar ya salman
Mun iso gida ina shirin fita yace " tsaya ke.
Ya fito ya zagayo inda nake ya riko hannuna yace " kibi a hankali jikinki baiyi karfi ba har yanzu.
Gaskia na rame kam sosai
Ya rufe motar yana rike da hannuna har cikin gida mmn sakina ta tashi ta kamoni suna min sannu a palon inna na kwanta .
Ya salman kafin ya fita saida na jishi yana jawa su sadiya kunne akan kar wacce ta yarda yaji wata magana a bakinta don yasansu kamar shaidanu suke kuma karsu hanani bacci.
Inna kam bimmu kawai take da kallo duk ta bi tayi kicin kicin da fuska ko me aka mata ne oho.
_Comment_ _and_ _share_
_Hauly_ _ce_ 👍🏻😍
[05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹
👨🏻🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻🚒
*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚
~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```
➡ page 1⃣4⃣
*********zuwa yanzu na warware tass mun koma iya shegen mu da fa,iza.
A wnn lokacin gabadaya samarina saida suka zo har gida suka dubani Ahmad kadai na hanashi zuwa gudun kar ya salman ya ganshi don ya min gargadi akansa.
Yauma da yamma doctor hakim yazo doctor din asibityn mu na school akwai lokacin da nayi ciwon Mara naje ya dubani shine fa ya daddage wai yana sona zai auren
Kuma gaskia hakim baida matsala kamilin mutum ne mai ilimin. Arabic da boko sannan yana da fara,a gashi kyakkyawan mutum daga gani bafulatani ne.gaskia hakim ya hadu ba kushewa.
Muna cikin hira a cikin motarsa ya kalleni cikin nitsuwa yace " Rumaisa ya kamata zuwa yanzu kam ki gabatar dani gun iyayenki domin ayi komai a wuce wurin.
Na Dan zaro ido nace"kai doctor me kk sauri?
Yace " ina tsoron kar in tsaya garin kallon ruwa kwado ya min kafa .
Mukayi dariya lokaci daya nace" hmm " ba komai zan tuntunbeka idan na shirya.
Ya juyo muna fuskantar juna sosai yace" rumaisa ko dai akwai Wanda kk so ne daban?
Na girgiza kai nace " ba kowa kai kadaine mutumin da maganar aure ya shiga tsakaninmu don haka insha Allah karka damu da kai za,ayi
Murmushi yayi min nima na maida masa yace" thank you so much my love
Na lumshe ido ina murmushi nace " doctor ina matukar........
Karar wayatace ta katseni ina dubawa naga kiran ya salman ne kin dauka nayi. Muka ci gaba da hiranmu cikin nishadi haka yaci gaba da kira har sau uku hakim yace " me yasa bazakiyi picking ba?
Nace yanzu lokacin ka ne doctor bazan amsa kiran kowa ba.
Yayi murmushi yace" nagode sosai my love.
Mukaci gaba da hira tex ya shigo wayata na ya salman ina dubawa naga:
*_Zaki_* *__zo_* *_ko_* *_sai_* *_na_* *_sameki_* *a* *_wurin_*?
Da sauri na dago kaina sai lokacin na ganshi yana tsaye a bakin gate din gidansu
Yanayin fuskar ya tsinkar min da zuciya sosai tsoro ya gama rufeni.
Hakim ma na lura shi yake kallo .
Ya juyo yace" rumaisa wancan kamar....
Nayi saurin fadin " yayana ne shi yake kirana dama.don bayaso mu dinga dogon hira dama
Na fada a kidime.
Ya gyada kai cikin gamsuwa yace" OK ba damuwa yanzu dai kije gida sai kara zuwa insha Allah.
Sama sama mukayi sallama
Nikam na rasa yanda zan yi duk tsoro ya gama rufeni ganin yadda ya salman ya hade fuska ya ke min wani irin kallo mai cike da tuhuma.
Yana ganin na nufi inda yake ya shige cikin gida haka nayi shahada na bishi a baya.
A Palo na same shi ya juyan baya
Hakan ya dan bani kwarin gwiwa fadin" yaya don Allah kayi hkr wayata tana silent shiy......
Juyowa yayi a fusace idonsa tuni ya rine ya zama jazir yace
" waye wancan Dan iskan da kk shiga motarsa kina wage masa baki?
Sunkuyar da kaina nayi a tsorace
Tsawa ya daka min har na gigice tuni hawaye ya ciko idona fall
" zaki fada min ko sai nayi ball dake!
Da kyar na iya bude bakina jikina na karkarwa nace doctor Hakeem ne.
Yace" OK Wanda yazo jiya fa wayeshi?
Ganin yana matsowa yasa na danyi baya nace" Mubarak ne.......
Ya katseni da fadin "Wanda na ganki da shi shekaran jiya fa wayeshi ?
Ya fadi hakan yayinda yake kara kusanto ni a tsorace nayi baya sai jina nayi na jingina da bango .
Runtse ido nayi ina jiran saukan mari sai jin hannayensa bisa kafaduna
Nikam tuni nasha jinin jikina yace" bazaki gaya min ba?
Na girgiza kai ina kuka nace" yaya Abdul majid ne.
Zuba min ido yayi yana huci kamar bakin kumurci.
Ba shiri naji ya kama jijjjiga kafaduna da karfi yana" dama ashe ba karatu kk ba iskanci ya kaiki makaranta kin tara yan iska kina mu,amala dasu ko?
Na girgiza masa kai cikin jin zafin abinda yake min
Yaci gaba da fadin " to bari kiji baki isa ki bamu kunya ba aurar dake zamuyi ba bata lokaci.don haka ki fada min a cikin ' yan iskan samarin naki waye kukayi zancen aure da shi?
A tsorace na girgiza masa kai nace " babu?
Aikuwa ko kan na rufe baki sai ji kk tass! Ya sauke min mari yana shirin sauke min wata.
Na zube durkushe a gabansa ina kuka mai tsanani na rike kafarsa ina" yaya don Allah kayi hakuri bazan sake ba wlh yaya sune suke matsa min amma daga yau na maka alkawarin bazan sake kula kowa ba
Naci gaba da kuka sosai .
Janye kafarsa yayi jikinsa ya mutu sosai ya zuban ido sannan yace,taso
Na tashi har lokacin kuka nake mara sauti.
Hannayena ya rike yace" ki fada min waye kk yi zancen aure da shi a tsakaninsu?
Cikin dauriya nace" doctor Hakeem ne?
What!!!?
Abinda naji ya fada a rikice.nima na kara tsorata .
Ji nayi ya kara rike min hannu yace " rumaisa ina jiye miki tsoron shiga matsala amma bazaki gane ba.kinsan waye hakim?
Na girgiza kai nace,"aa
A sanyaye yace" hakim mijin surayya yayar Ahmad ne.akwai matsala idan kk kuskura kk shiga gidansa familyn su Salima bazasu taba barinki ki zauna lfy ba.kima kanki gata ki rabu da hakim rumaisa ki nemi wani a cikin samarinki.
Mamaki ne da tsoro ya cika ni don ban taba sanin matar hakinm yar uwar Ahmad bace tab lallai na hadawa kaina case babba.
Ganin nayi shiru yasa shi fadin " ko dai kin fi son hakim din?