← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 128

Sashe 48

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin fuskata ta sauya yasa shi fadin " no kar ki damu abinda Na gaya miki gaskia ne har cikin raina.

Murmushi na sakar masa nace " yaya Na gode tabbas ka cika masoyi na gaske .ni kuma duk randa ka aureni zan baka babban *SURPRISE*

Na karasa fada ina murmushi shima fuska sake yace " Allah ya nuna mana rai da lfy *IHISAN* 'yar gatan daddy

Dariya nayi nace " kai yaya .to muje kaci abinci ka samu ka huta.

Yace " ai ba gajia tunda jirgine Abuja to yola ba nitsa.

Muka isa dining na gyara mishi wurin zama ya zauna hade da fadin " thank you.

Ruwa mai sanyi na dauko a fridge na zuba masa a cup snn na mika masa ya karba .

Nace " to yanzu me za,a zubo maka tuwon semo miyar kuka ko jallof da peppe chicken ko dai pepe soup na rago zan zubo maka akwai kuma snacks.

Tunda na fara magana ya zuban ido har na gama baice komai ba sai kallona kawai yakeyi.

Da sauri nace "au afwan yayana nasan kafi son tuwo musamman semo da miyar kuka ko kubewa.

Ya saki fuska yace " ai na dauka ko kin manta abubuwanda nafi so ne?

Na ce " tab na isa ?

Na fada ina murmushi na dauko plet na masa serving tuwon semo miyar kuka da yasha naman rago ga daddawa da man shanu .gaskia mutanen yola sun cira tuta wajan dafa miyar kuka .

Ya salman yaci sosai don ya yaba miyar sosai har yace min " gaskia girkin nan yayi ki koya sosai ina so.

Nayi murmushi nace to.

A yayinda yake wanke hannunsa na mika masa tissue nace " amma yaya bakaci da yawa ba fa in kara maka mana.

Yace" what! A gidan surukai fa nake kuma ma am OK nagode sosai.

Nace " to muje ka huta ya samir Na jiranka in yaso da yamma Sai muje gidan galadima.

Muka fita Na kaishi gun ya samir don ya samu ya huta.

Ni. Kuma na dawo dakina Na fada gado zuciyata cike da farinciki nan na fara tunanin me zanyiwa ya salman in Dada burgeshi domin ina matukar ji da *SOJAN* nan nawa.

Aunty samira ce ta shigo ta sameni.

Bayan ta zauna kusa dani ta kalleni tana murmushi tace" ihisan yau dai naga ya salman dinnan da kk damunmu da sunanshi motsi kadan yayana yayana yayana!!!

Dariya mukayi lokaci guda nace " aunty to ya kk ga yayan nawa.

Tace " eh na ganshi kyakkyawa ga cikar kamala ga kuma kwarjini ga natsuwa amma fa yayan baki yanada matsala daya.

Fuskata tuni ta sauya nace" meye matsalar aunty gimbiya?

Tace" yayan naki baya dariya Sam kuma baya magana sosai me yasa?

Dariya nayi nace " aunty yayana haka halittarsa yake amma fa a hankali in ya saba da mutum to zakuyi hira kuma zaiyi miki fara,a kuma kinga sojane a bariki ba,a San wani dariya ba...

Dariya mukayi lokaci guda kamar kawaye .

Aunty rukayya ma ta shigo tana cewa" daryar mi akeyi?

Aunty samira tace " tadin surukina muke.

Aunty rukayya tace " gaskia surukin mu ya hadu sai dai rashin magana ko dai kunya ne.

Nace " eh aunty.

Ta yi murmushi tace " to ba wnn ya kawo ni ba nazo ne in tambayeki me surukin nawa yafi so a dafa masa.

Nace uhmm to surukin naku Dan gargajiyane tunda yaci tuwo da rana to da daddare kunu zaisha sai kuma in yazo kwanciya yakan sha fruits shikenan.

Aunty rukayya tace " OK to da safe fa ina son komai ya zama ready ne kar a sami matsala kinsan daddy zai yi fushi .

Nayi murmushi nace " breakfast dinnan na lura bai cika zabe ba amma na lura yana son tea da bread da pepe soup ko wane iri.

Aunty rukayya tace " O Ihsan kinaji da yayan nan naki.

Sunkuyar da kai nayi nace "aunty .....

Tace " banson sunan nan na aunty kuce mun Momy kamar yadda yayyunki ke ce mun ga nan auntynku.

Ta nuna aunty samira .

Mukayi dariya .aunty samira tace " kai Momy kema fa kamar auntynce don baki tsufa ba.

Aunty rukayya dai fita ta yi ta barmu.

Na kalli aunty samira nace " yawwa aunty dama ina son nono mai kyau ko fresh milk yayana yana so.naga rannan an kawo wa daddy.

Tace " eh ai sati sati ake kawo masa madarar mu muke maidashi ( kindirmo) gashi na wnn satin ya kare wlh.dama daga garken sa ake tatsowa...

Nace " kash amma banji dadi ba yanzu aina zan sa mu?

Tace " kwantar da hankalinki yanzu ma ba don yamma yayi ba da sai muce a kawo amma gobe in Allah ya yarda zan sa a kawo miki fresh milk sabon tatsa ma kuwa.

Nace " to aunty Allah ya kai mu.

Tace " amma na lura kin damu sosai me zai hana in aiki driver akwai SARE KOSAM can kusa da Jippu jam sai a siyo mishi.

Nace " yawwa aunty bari ma naje da kaina ina son in dana motata dama ko zaki fadawa daddy?

Tace ba komai kije amma kar ki Dade Allah ya tsare ba dai kin tabbatar kin iya driving ba?

Nace " eh.

Tace " to sai kin dawo.

Tashi nayi da sauri na dauki gyalena na yafa snn na dau jakata da key din motata.

Na fita harabar gida nan nace mai gadi ya buden get.

Ba jimawa naja motata na fita bansha wahalar gane kwatancen ba ina isa naga an rubuta *SARE* *KOSAM*

Bayan na gama parking na sauka na rufe motata na shiga gaskia wurin ya burgeni na tarar da mutane da yawa wasu suna shan fura da nono wasu madara wasu kuma youghut .

Gaskia naja hsnkalin mutane sosai domin ba maza kadai ba harda mata bina suke da ido .

Wasu har daga min gaisuwa suke da fillanci bansan me suke fadi ba amma dai komai akace min nakance musu ' *JAM* '(lfy)

Bayan na sayi fresh milk da kindirmo na fita da sauri wani har bina yayi yana ce min da fulatanci " hajjajo noi chomri( hajiya ya gajia.?)

Nace " bana jin fulatanci yi hkr kuma sauri nake .....

Karar wayata ta katseni na Ciro ta a jakata ina dubawa naga sunan daddy da sauri nayi receiving kamin nayi magana yace " ihisan kina ina ne?

Nace " yanzu ina wajen jippu jam ..

Ya katseni da fadin to ki dawo karki tsaya koina garin nan namu cike yake da kidnappers ga kuma wayan nan matasan masu kwacen wayoyi ki kula sosai Allah ya dawo dake lfy.

Aikuwa a tsorace nace amin daddy .

Tab ai ban biyo ta kan wnn mutumin ba na fada mota ina waigawa inga su waye a bayana ganin ba kowa yasa na fizgi motar da gudu sai gida .

Ina fita daga motar ya salman da ya samir suka karaso guna ya samir yace " ke ihisan yaushe kk gama gane kan garin ne da zaki fita ki rufa mana asiri don Allah.

Na kalli ya salman snn na kalli ya samir a shagwabe nace " naga duk hankalinku ya tashi aunty samira ma sai kirana take ina tuki .ban fa yi nitsa ba naje na siya ma yayana ne fura da nono sai fresh milk don nasan yana so ko yaya?

Na fada ina kallon ya salman yace " hakane amma da baki fita ba sai ki aika kinga ke bakuwa ce a garin kuma macece don Allah kar ki kuma fita ke kadai kanwata.

Na bata fuska kamar zan yi kuka nace " to .

Daga nan na wuce ciki.

Gun daddy naje tukun kamin na koma dakina na sake wanka na sake shiryawa cikin material dogon Riga na zauna gaban madubi na sake zuba make up .

Bayan na gama na je na sami su yaya samir muka tafi gidan galadima.

Su ummah da mama sai Jan salman suke da wasa suna ya rabu dani ga su nan sun fini kyau .

Gaskia ya salman yaji dadin zuwansa yola domin an karramashi sosai .

Kwanansa biyu duka daddy ya hana shi kwana hotel a gida yake kwana da ya samir sun saba sosai .

Gaba daya naji ba dadi da yazo tfy duk da nasan nima na kusa tfy tunda mkranta za,a bude.

Daddy yayiwa ya salman Godiya sosai da irin kulawar da ya bani don na bashi labarin.

Ni da ya samir muka rakashi airport duk naji ba dadi wlh banki muyita soyaiyar mu a yola don ba sa,idon su inna .

Hauly ce🥰👍🏻
[9/25, 6:21 PM] Mum Sadiq: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰

*Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤*

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```

Page➡45

************Bansan sanda ya tafi ba ni dai bayan na gama kukana toilet na wuce na wanke fuskata .

Da yake tuni mukayi sallama da daddy kawai na salami su aunty rukayya fatan alkhairi suka min yayinda sukace in gaida Mamana.

Ya samir ne ya kaini gidan galadima na ma su Haj rumaisa sallama daga nan muka kama hanyan airport.

Sam ban gayawa kowa ina hanya ba.don gudun kar ya salman ya nemeni ma rufe wayoyin nayi.

Ya samir ya lura ina cikin damuwa sosai jikinsa a mace yace" ihisan duk naji ba dadi da wnn hadin da za,a yi na aurenki da yarima tun kan kizo daddy ya kiramu ya sanar damu amma wlh dagani har awwal da Hafiz bamu ji dadi ba kuma mun cewa daddy ya fadawa mama( Haj Zubaida) halinda ake ciki ta fadawa mai martaba cewa kina da Wanda zaki aura kuna son juna amma daddy yace maimartaba umarni ya bashi kawai kai tsaye...,

A hankali na katse ya samir da fadin " babu komai yaya zan yi biyayya sosai ga iyayena kuma zan auri yarima da zuciya daya in masa ladabi da biyayya.
Sai dai matsalata dayace a rayuwa ta yaya zan fuskanci ya salman da wnn maganar?
Chapter 48 · 0% Book details