← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 128

Sashe 109

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan nafisa ta warware tass anan suka fara shawarar dawo da ita amma tace sam ita bazata zauna gida daya dani ba sai dai a canza mata gidanta anan innah tace wa ya salman ya nemawa nafisa gida yace shi baida kudi lol! Sai dai ta zauna a tsohon gidanmu wanda ke kusa da su innah anan adda A'i tace Allah ya sawwaka nafisa tafi karfin wancan tsohon gida sai dai a kaita gidansa na Abuja.

Haka suka dauki kayayyakinta suka mayar Abuja ba tare sun tsaya jin ra,ayinsa ba don haka shiru ya masu ya xuba musu na mujiya ranar da zasu maida nafisa Abuja inna ta kirani tana ja min kunne akan in ta kuma jin kiris wlh sai ta saka ya salman ya sakeni don ya isheta zamana a gidan danta.

Da yamma ya salman ya dawo ko abinci ban barshi yaci ba nace ya shirya ya tafi Abuja an kai masa amaryarsa can kar ya zauna ana kuma ya ja min matsala suce ni na hanashi zuwa gun matarsa.

Wani irin kallo ya min snn yace "ke yanzu tunaninki ya baki zan bar abinda nakeyi in tafi Abuja saboda wata?
Ya girgiza kai snn yace bazai yiwu ba wlh tunda sukayi abinsu ba shawara su suka sani ni ba inda zan je kuma kema karki matsa min.

Ba shiri na soma hada shi da Allah ina don Allah yaya salman kayi hkr ka tafi Abujan nan ka rufa min asiri kar su innah su zargeni akan nice na hanaka tfy gun amaryarka .

Yace"ke ni fa ba inda zanje karma ki bata bakinki.

Tashi nayi na fita da sauri raina a bace na koma part dina waya nayi wa mama na gaya mata abunda ya faru.don haka ba bata lokaci ta kirashi itama tayi mishi magana.ba dan ransa naso ba ya shirya ko sallamata baiyi ba ya fita yana ta fushinsa ko ya sami jirgi ya tafi ko da mota ya tafi nidai ban sani ba........

Hauly ce👍🏻🥰
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡94

*********Farida tun ranar da aka kawo nafisa sukayi sa,ainsa da su goggonanta dama washe garin suka koma Abuja.tunda ta koma hankalinta na nan kano ita a son ranta tafi so ta dawo nan mu zauna.

Kuma dama ruma ta fada min duk halinda faridan ke ciki sanda tazo biki.amma tashin hankalin da na shiga na bikin nan ya hana inyiwa farida maganar har suka koma Abuja.

Bayan komawarsu suka ci gaba da soyayyarsu da farouq har ya kaita gun iyayensa ta gaishesu anan Ahmad ke tambayan farouq din farida yar gidan wayene?

Salima dake zaune tayi murmushi tace"ka dubeta da kyau dawa tayi maka kama?

Ahmad ya kalli farida wacce kanta ke sunkuye a dole ga mai surukai
Yace"gaskia dai fuskar tayi mun kama da tsohuwar fuska dana sani a baya.

Salima tayi dariya tace"hakane faridace wnn 'yar gidan Salman da Rumaisah .

Cike da mamaki Ahmad yake kallon farida yace"ikon Allah yanxu wnn yar queen ne ta girma haka?masha Allah taso taso yata ai nan gidanku ne ki saki jikinki sosai karki kuma yin bakunta a gidan nan kinji?

farida ta daga mishi kai tana murmushi yace"tashi ki zauna kan kujera.

Kusa da salima farida ta zauna salima tace "kaga ni kuma tafi min kama da ya salman akan rumaisa.

Ahmad yace"ai ke dama bakisan kama ba.ai wnn kina ganinta kinga rumaisah bata wani kama da salman.

Farouq yayi dariya yace"ai mum karkuja maganar da nitsa ma.da mum dinta da dad dinta suna kama sosai da juna shiyasa kuka rasa da wa take kama a cikinsu.duk kamanninsu daya ni da na gansu a hoto har ina mamakin kamanninsu sai da ta gaya min cewa ai yanuwane auren dangi sukayi.

Ahmad yace"hakane yan uwane.
Salima tace"son ya kamata idan kaje kano kaje ka gaishesu tunda yanxu maganarku tayi karfi .
Farouq yace "in Allah ya yarda mum zanje.

Haka suka dinga hira da dariya farida kam ba karamin dadi taji ba yanda iyayen farouq suka karbeta da mutunci har tayi kawance da kanwar faruk mai suna Rumaisa amma suna ce mata Islam Ahmad ya gayawa farida cewa Islam takwaran mamanta ne.anan farida ta fara tunanin shin meye alakar mamanta da Ahmad ? Lokacinda faruk ya dawoda ita gida ta tambayeshi ko ya sani.

Murmushi yayi yace"Aisha sarkin tambaya.zan fada miki amma sai lokaci yayi yanxu dai ki shiga gida kinga magriba ta kawo kai.amma gobe zanzo da yamma in daukeki tunda kika dawo daga kano bamu samu mun fita ba kuma goben ma akwai dinner din wani abokina da nake so muje.

tace"hmm ai baka sani ba dadyne baya son yawan fitan nan yau ma basu sani ba na fita nasan zasuyita nemana ban ma san wani karya zan musu ba wlh.

dan tsaki farouq yayi yace"gaskia uncle dinki nan ya cika sa miki ido da yawa yanxu fa zamaninmu ne be kamata a matsa miki ba haba don Allah su lokacinda sukaci zamaninsu waya sa musu ido?

Farida tace kai dai bari kawai dear gabadaya ni yanxu na gaji da zama gidan nafi son in koma gidanmu domin daddyna baya sa min ido duk abinda naga dama nakeyi.

farouq yace"ai daga gani dad dinki wayayyen mutum ne kinsan zaman bariki ai dama.

suka danyi dariya daga nan farida tace"kaga bari in shiga gida nasan dad zai fito domin tfy masallaci.

Rike hannunta farouq yayi sannan ya matso da fuskarshi dab da nata yana mata wani irin kallo yayinda yayi kasa da muryarsa yace"Aisha bana son rabuwa dake ko na second daya saboda irin son da nake miki.
Murmushi farida tayi hade lumshe .

farouq ya sauke ajiyar zuciya snn yace"ki yi yadda zakiyi duka mu fita goben nan kar ki ce kin fasa.

Cikin kwantar da murya tace"Insha Allah.

Suna cikin haka kuwa Salim ya fito tare da su Salman junior zasu shiga masallaci gabadaya sun ganta amma ba wanda yayi magana suka wuce masallaci.

Farida ta tsorata sosai don haka sukayi sallama da farouq ta shige cikin gida.ba kowa palo tasan mum dinsu ta shiga daki yin sallane dan haka ta wuce dakinsu da sauri inda ta sami mimi ma na sallah bandaki ta shiga dan yin alwala.

Bayan sallar isha Salim ya kirata yana tambayarta ina taje kuma ita da wayene ya gansu a mota?

Bata da zabi dole ta fada mishi gaskia tunda ya gansu.
Kanta a sunkuye tace"dama daddy munje gidansu farouq ne na gaisheda iyayenshi shine ya dawo dani gida bayan nan ba inda naje.

Salim yace"amma ba hanaki kula wnn shashashan yaron ba?

shiru farida tayi kanta a kasa yace"farida wnn yaron ba dan arziki bane in kika biye mishi zai bata miki rayuwa ne kawai.don Allah ki rabu da shi ki daina biye masa yana zuwa ya na daukanki kuna fita kinji?

ta daga mishi kai hade da fadin"to daddy.

Yace"kinga ma har naje na samo muku admission keda mimi zaku fara zuwa makaranta kwanan nan don haka ki daina biyewa wnn yaron don Allah .

Shiru farida tayi don bataji a jikinta kamar zata iya rabuwa da farouq .

Salim yace"shikenan tashi kije ki kira yan uwanki kuzo gabadaya muyi dinner.

Tashi tayi hade da fadin to.
Tana fita ya kalli rumasau yace"Ruma gaskia lamarin farida ya fara bani tsoro kinga fa yarinyan nan ta canxa gabadaya kuma duk abinda muke gaya mata bata ji.don haka dolene se mun tashi tsaye akan tarbiyan farida don kar muzo muji kunya.

Ruma tace"gaskiane kaga wlh ni dazun bansan yaushe farida tasa kafa ta fice ba ina bacci.

Salim ya ce"don haka dolene ki bar baccin rana ki kula da shiga da ficenta.domin hanata fitan shine mafita a garemu don muddin in tana fita suna haduwa da wnn yaron to watarana zata bijire mana.

Ruma tace insha Allah zan maida hankali sosai a kanta .

Suna cikin hakan yaran suka shigo gabadaya amma banda farida don haka dadynsu ke tambayansu ina take?

Mimi tace"tana daki wai ita ta koshi bazataci komai.
Shiru salim yayi ya rasa me zaice.rumace ta tashi ta tafi gun farida.

Gaba daya farida rashin jinta se gaba gaba yakeyi .farouq se kara zugata yakeyi don hska ta daina jin maganar kowa sai nashi.munir kam ta ma daina zancansa gabadaya don yanxu ko ya kira ta layin mumynsu in yace a bata kin karba takeyi .gashi ta tsiri bakin hali bata kula kowa a gidan kuma bata sakewa tunda dad dinsu ya saka mata doka akan kar ta kuma fita shine ta shiga gaba da kowa.yayinda farouq ke kara zuginta akan ta bijire musu yana nunan mata sam basa sonta a gidan.

Watarana yace mata zasuje club da daddare tayi duk yanda zatayi ta fita su hadu don haka ta shiga lallaba mom dinsu akan ta barsu suje gidan kankansu Alh Kasim su wuni da kyar ruma ta yarda suka shirya gabadaya driver ya kwashesu ya kaisu.

Momy zuwaira ta cika da murnar ganin jikokinta dama ga yaran hakim ma sunzo harda mamansu wato ruky.
Nan aka shiga hiran duniya cikin nishadi a inda farida tayiwa farouq text din inda take yazo ya dauketa.

Ba jimawa kuwa yazo lokacin yamma yayi sosai don haka ta fita suka tafi ba tare da sanin kowa ba.
Sai da akazo tfy gida suka nemeta suka rasa duk gidan bata nan.mai gadine ya tabbatar musu da wani mai mota yazo ya dauketa sun tafi

Anan ruky ta kira ruma tana tambayanta ko farida ta dawo tace bata dawo ba.

Shiru shiru ba labarin farida har bayan isha.Salim ya dawo ya sami labarin don haka bai zauna ba ya fita domin nemota .

Har kusan shabiyun dare Salim ya binciko ya gano inda suke.yana zuwa ya sami farida acikin yanayinda ya matukar tsoratashi koda wasa bai taba tunanin farida zata zo club ba bare tasaka irin wadan nan damanmun kaya dake nuna siraicinta a waje.gata rumgume jikin farouq anata casu.

Kansa ne yayi wani irin mugun sarawa ba shiri ya dafe kan hade da fadin"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun.
Chapter 109 · 0% Book details