← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 128

Sashe 20

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama kam dariya abin yaso ya bata.

Abba ya kallerta yace,shatu kukan fa na meye?

Cikin muryan kuka tace" ba dole inyi kuka ba in ba kuka nayi ba me zan yi ? Kun hada kai kun dauki shegiya wacce ba,a San asalinta ba,a San waye ubanta kun likawa dana dan kun tsaneshi.me ye salman ya muku a rayuwa kk mishi irin wannan abubuwan da farko kun daukeshi kun turashi makarantan mugaye yanzu kuma kun rasa wacce zaku bashi duk dangi a matsayin matarsa sai RUMAISA?

Ta kara tsananta kuka .

Abba yace,kinga shatu duk abinda kk fada ba haka bane salman da kansa yace zaije makaranta soja sannan shi ya zabi rumaisa a matsayin wacce zai aura sanin kanki ne bama takura ma yaran mu abinda suke so shi muke musu in dai basu kaucewa fadin Allah da manzansa ba.

Innatace "wlh salman ba son rumaisa yake ba kawai dai makircine.

Abba ya fusata " kaji zancen banza to su waye suka hada makircin.......

Daddy ne ya katseshi da fadin " yaya karka bata rai bari in kira salman yazo

Nan da nan daddy ya kira salman aiko minti biyar mai kyau ba,aiba sai gashi ya shigo hankalinsa ya tashi ganin inna na kuka .

Aikuwa tana ganinsa ta mike tun kan ya zauna ta fuskance shi cikin tashin hankali tace" Salman fada min wai Kaine da kanka kace kana son rumaisa ?

Shiru yayi ya rasa me zai ce mata ya riko hannunta yace " inna zauna bana son inga kuka.

A fusace ta wanke shi da mari cikin tsawa tace " zaka amsa min tambayata ko kuwa.

Ya dafe kuncinsa yayinda ya sauke kansa a kasa yace " eh inna ni nace ina sonta kuma nake son aurent.....

Bata bari ya karasa ba ta sake dauke fuskar sa da mari tana shirin karawa Abba ya ce" kar ki kuskura ki sake marinsa ya isa haka.

Riko wuyar rigar salman tayi tana kuka tana cewa" duk duniya ka rasa wacce kk so sai RUMAISA? Kasan wace ce ita ? Kasan ta wace hanya aka sameta?
Salman ina so ka Sani ban amince ka auri rumaisa ba kuma wlh idan ka aureta sai ka biyani NONO na da kasha!!!!!

Ta fice tana kuka mai tsanani.

To fa!!!!!!!!

Hauly ce👍🏻🤝🏻😍
[05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*Wannan* *page* *_naku* *ne* :
*CHUBADO *MOH'D*
( *Uwar* *dakinmu* ) *&*

*UMMI* *ABDULLAH*
*na* *gode* *da* *kulawarku* *sosai* .

```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM```

Page➡17

*********Ganin yanayinda na shiga yasa ya salim riko hannuna ya na kallona yace" rumaisa ko dai ban miki ba? Naga kamar bakiyi farin ciki da zumuncinda muka kulla ba.

Kai na sunkuyar jikina a mace sosai na kakaro murmushi na dole Wanda yafi kuka ciwo duk da ni kaina bansan dalilinda yasa naji banson ya salim ba.

Murmushi yayi yace " kinga shiga mota bari inje in siyo drinks ina zuwa.

Ya bude min gaban motar ya salman na kame ko a jikinsa don tsabar duniyanci waya ma yakeyi hankali kwance.

Ya salim ya kalleshi yace" Oga sir gata nan ka mata karin bayani ina zuwa naga ka dage sai soyewa kk a waya .in ka gama kayita daurewa mutane fuska tsabar mu ka raina.

Ni dai na shiga na kuma zauna ya salim ya rufe kofar ya tafi.

Mamakin yanda ya salman ke waya cikin nitsuwa da nishadi har da 'yar fara,a nake.na dai San sun rabu da Salima ko dai ya samo wata ne?

Maganarshi ta karshe naji wani rass!
"Ki kula da kanki sweet heart komai zai daidaita insha Allah tnx u bye.

Ya sauke wayar a hankali ba tare da ya kalleni ba ya kunna na,urar sanyaya mota hade da daga glass sannan yace" gaskia kano ana zafi.

Sai lokacin ya kalleni kamar bai son yin maganar yace " Salim din ya gama yi maki bayani ai?

A sanyaye nace"eh yaya.

Yace" Good, to me kk ce?

Na danyi shiru snn na daure gudun kar na cuci kaina a banza nace" amma yaya kamar ka ce min ya salim ya sami wata a Abuja har maganar su tayi karfi?

Shiru yayi har na tsawon minti biyar har na cire ran zaiyi magana sai naga ya juyo sosai ya fuskanceni cikin sanyi murya yace" ba salim ne na zaba miki ba.

Da sauri na dago na kalleshi cike da mamaki sannan na juya na duba bayan mu ba kowa na sake kallonshi a karo na biyu shima ni yake kallo da sauri na sunkuyar da kai nace" to wayene?

Ba zato ba sammani naji yace"SALMAN ne ma,ana nine.

Tsabar mamaki bansan sanda na zaro ido na saki baki ina kallonsa ba shima ni yake kallo .

Bansan tsawon lokacinda muka dauka a haka ba kowa da abinda ke ransa.

Hannuna da ya riko shi ya dawo dani duniyar tunani dana tafi da sauri na sadda kai kasa.

A hankali naji yace" RUMAISA kaina na zabawa ke a matsayin abokiyar rayuwata.amma fa sai kin Amince don ko da wasa bazan so kaina in kuntata miki ba.

Ya dan numfasa sannan yace"Rumaisa INA SONKI zuciyata ta dade da fara sonki.

Nikam zuwa yanzu tsoro ma na koma yi bayan mamaki.

Ban ankara ba naji ya matso da fuskarshi dab da tawa har muna exchanging numfashi a hankali ya furta" kin amince?

Wani masifaffen kunya ne ya ziyarceni har na kwaci hannuna ba shiri na rufe fuskata.a can cikin zuciyata kuwa farin ciki nake sosai don ina matukar son yayana.

Sautin murmushinsa na jiyo sannan yace" kunya ko? Bari kiji yanda na zo da kaina na Isar da sako ba tare da na aiki kowa ba kema haka nake son ki ban amsata kawai.

Kai kawai na iya daga masa don har lokacin fuskata rufe.

Ji nayi ya riko hannayena duka ya sauko da su sann yace" to oya gaya min kin Amince?

Ya fada yana kallon fuskata .

Duk na rasa yanda zanyi saboda kunya.
Da kyar nace" eh!

Wayyo ji nayi kamar na nitse gashi ya tsura min ido kallon ma na daban ne yau.

Murmushi yayi sosai yayinda ya jawoni jikinsa rumgumeni yayi sosai a cikin kunnena yace min" masha Allah kanwata na gode sosai gaskia bazan iya manta wnn rana a tarihin rayuwata ba .Kanwata ina sonki sosai ke din dabance a cikin mata.Allah ya miki albarka.

Nikam dada kwantar da kai nayi a kirjinsa ina jiyo bugun zuciyarshi ido na lumshe ina shakar kamshin turarensa mai dadin gaske yayinda sanyin Ac ke ratsani.wani dadi da farin ciki nakeji mara misaltuwa.

Ya dago kaina a hankali sannan ya riko hannuna ya zuba ma yatsuna ido sai naga ya Ciro wata container mai kyau a aljihunsa sai daukan ido yake ya bude wata zobe ya cire tsiriri mai kyan gaske na gold yana ta daukan ido ya kamo yatsata na hannun dama ya saka min .

Murmushi yayi yace" wnn tukuicin kyautar da kk min ne kanwata na gode sosai Allah ya miki albarka Allah ya nuna mana aurenmu rai da lfy.

Kaina a sunkuye nima ina murmushi nace " na gode yaya Allah ya saka da alkahairi.

Yace" yanzu kije ki shirya kizo mu tafi gida .

Nace " to

Daga nan na bude motar na fita hade rufo masa kofar .

Har na isa hostel bakina ya kasa rufuwa don farin ciki wayyo Allah ba dadi zai kasheni anya akwai macenda ta kaini sa,a kuwa? Lol

Da sauri na dauko jakata da wayoyina Wanda na saka a silent.

Ina zuwa ashe ya salim ma ya dawo don haka na shiga baya mun fara tfy ya salim ya dinga zolayata nikam duk kunyansu nakeji ya salman kam baice komi ba

Sai da ya gama zolayarmu snn yace" to yanzu kuma saura na maku nasiha a kan zamantakewar rayuwa.

Ya danyi gyaran murya sannan yace" rumaisa ga dan uwana amana ki rike shi da kyau ki nuna masa so da kulawa ki masa biyaiya sannan kiyi hakuri da halinsa kinji .

To. Na fada a hankali

Sannan yace " kai kuma ga ' yaruwata maganar daure fuska tsawa fada da makamantansu duk ka aje su a barikinku sosai zaka zage ka nuna mata so da kulawa ka jawota jikinka kaji matsalolinta Ku zauna Ku fahimci juna a tattauna kowa yasan me Dan uwansa yafi so me kuma ya tsana don a kiyaye sannan duk wuya duk rintsi a rike gaskia wnn shi zaisa soyyayya ta dore har ta kai ga aure fatan ka fahimceni?

Shiru ya masa kamar ba da shi yake maganar ba.

Can muna cikin tfy ya salim yace" wai ni baka fada min yadda kuka kare da mutumiyar ba.

Sai lokacin yace" ta yi serious kan maganar nan fa kawai ka hkr ka nemi fili a abujan.in dai don ni kk son zaman kano na yafe don nima ba mazaunin nan bane.....

Tsaki ya salim yayi yace" wayace maka saboda kai ne? Ni ra,ayina nafison in zauna cikin dangina don haka ba wacce ta isa ta juyani.wlh salman zan iya rabuwa da rumasa'u akan wnn..

Ya salman yace" kar ka fara don rumasau tana sonka ka Sani kawai dai tafi son zama Abuja kusa da iyayenta ne ga kuma makarantarta don haka a wnn tfyr dai kaine baka da gaskia.in zaka bi shawarata Ku zauna Abuja tunda kaima acan kk aikinka in yaso in kun samu hutu sai kuzo kano a hankali a hankali watarana sai kaga kun dawo kanon gabadaya ko ya ka gani?

Ya salim yace" hmm na tuna wnn amma kasan me ya bata min rai? Irin yadda naga take ta fishi akan nace a kano zamu zauna.anya kana ganin wannan yarunyar zata so min ' yan uwa da dangina? Ni faa nafi son matar da zata so min yanuwana ta zauna cikinsu a hada kai a zama daya.

Salman yace " na fahimce ka kuma insha Allah sweet heart ma tana daga cikin jerin matan da kakeso karka damu.

Ya gyada kai yace" to Allah yasa.

Har muka isa gida suna hirar wnn yarinyar da naji sunace mata Rumasa'u
Chapter 20 · 0% Book details