← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 128

Sashe 17

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Inna tace" ooo wato so kk ki bata ta da muguwar dabia irin taki dana uwarki .ina kk taba jin an saki mace sannan ta koma da kanta ba tare da anyi bikonta ba ? To bari kiji mu nan miji ke bin mace ba mace ke bin miji ba wnn abin kunyane .kuma abinda kike zuga raihana ta yi mu bamu sanshi ba wnn halin gogaggun mata karuwai ne .dama na fada in har kk tafi jamia ba abinda zaki tsinana to gashinan kinje kin koyi karuwanci zaki zuga min ' ya to wlh a hir dinki ki fita idona in rufe hawainiyarki ya kiyaye ramata .Uwarki ma duk karuwancinta ta buga dani ta barni bare ke karan Kad'a miya.

Tuni hawaye ya cicciko idona nace, " inna kiyi hkr in Allah ya yarda bazan kuma yi muku shishshigi ba.

Sadiya tace" hmm da yafi miki .

Raihana tace " wlh tunda abin ya zama haka gara in fito muku fili ni komawa zan yi kuma ba wanda ya isa ya hanani.kuma Ku daina zagin rumaisa don ba ruwanta Ku zageni ni.

Ta mike ta fita tana gunguni .

Suka bita da kallon mamaki sadiya tace" Inna bakin gani muna zaman zamanmu yaya yaje ya dauko wnn shegiyar yarinyar ya kawota dama ya barta can gidan uwartata.kinga daga zuwanta har ta zuga raihana ta na son ta bijire miki ba.

Cike da takaici inna tace" tama bijire ai bakiji maganganun da ta gaggaya mana ba .

Sadiya ta harareni hade da fadin " sai ki zuba ruwa a kasa kisha munafuka kawai.

Inna tace" sai anyi magana ki tashi kinawa mutane kukan munafurci.kamata yayi kije ki tambayi uwarki waye UBANKI kuma aina yake ba wai ki zauna kina shirya munafurci ba .don haka ki tashi ki bace min da gani.

Mikewa nayi ko ganin gabana mai kyau banayi na fita tsabar bakin ciki naji wani abu ya taso ya tokare min kirji ban tashi Sanin ina nake ba sai bude ido nayi na ganni a gadon asibity.

Anan na fara tuna komai daya faru .

Na kalli mama dake zaune kan kujera da kyar na iya bude bakina nace,mama.

Riko hannuna ta yi tace" rumaisa ya jikin me kk ji? Bari in kira doctor.

Ta fita da sauri sai ga doctor ya shigo da ya salim ya salim duk ya shiga damuwa.bayan ya sake duddubani yace" ba matsala yanzu kam amma ta kiyaye sosai domin ciwonta har bacin rai ma yana iya tayarwa don haka a kula don Allah. Kuma ayi kokari tasha magungunan da zamu rubuta mata yadda ya kamata

Daga nan ya fita ya salim ya bishi baya.

Karfe 9 na dare muka isa gidan mama ina ji tun a mota ta kira abba tace mishi an sallameni kuma zata koma dani gidanta saboda ina sakaci gun shan maganina.

Nasan dai ta fadane amma daga jin yanda take magana nasan ranta a bace yake.

Anan mukayi wa ya salim sai da safe muka shigo gida bayan mun idar da sallah mukaci abinci nasha magani na.har na kwanta mama ta shigo tana tambayata abinda ya faru.

Nan na kwashe duk na fada mata.

Ranta ya mugun baci tace " lallama shatu har yanzu tana neman magana dani amma very soon zan maida mata da martani.

Nikam zuwa yanzu nafi jin haushin mama da kowa ta boye min labarina koma ta hana in tambayeta wnn wace irin rayuwace ? Ni yaushe zansan mahaifina ko zan huta da gori😭

Hauly ce👍🏻😍
[05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```

➡ page16

***********Gabadaya na rage walwala tunda abin nan ya faru mama ta kasa gane kaina.

Kwana na biyar a gidanta rannan ina bacci da rana sai ga kiran ya salman da kyar na iya lalubo wayar nayi receiving ba tare da nasan ko waye bane.

Muryar ya salman naji ya kira sunana" rumaisa.

Ai da sauri na bude idona na mike na zauna hade da fadin" na,am yaya ina wuni?

Yace " lfy ya jikinki? salim yace bayan tfyna kin kuma rashin lfy.

Nace" eh amma na warke.

Ya danyi shiru snn yace" ya akayi hakan ta faru?

Nace" haka kawai.......

Ya tari numfashina snn yace " nasan bazaki fadamin gaskia ba dama.kuma na hanaki karya.

Nace" kayi hkr.

Yace" shikenan amma dama na gargadeki akan karki saka kanki a cikin matsalar su sadiya ko?

Nace" eh ka gargadeni.

Yace" kinki jin maganata shiyasa hakan ya sameki.don haka ki kula nan gaba kome zai faru da su ki zuba ido kawai.

Nace" insha Allah yaya zan kula.

Yace" ya maganarmu? Kin samo min?

Shiru nayi na rasa me zance.

Yace" kinyi shiru.

Na kama Sosa kai nace " am yaya dama ni duk na dudduba ban samo irin wacca kk so ba.kayi hkr .....in yaso...sai ince su...faiza su duba maka...a ABU....

Ya katseni da fadin" wnn maganar sirri ne tsakanina da ke.karki yarda na jita a koina.

Nace" to yaya zan kiyaye.

Ya danyi shiru snn yace tunda kin kasa samomin shikenan duk wacca na samo karki kushe.

Ban San lokacin da nayi murmushi nace " na isa in kushe abinda kk so yaya?

Yace" shikenan.kuma ki shirya duk sanda nazo kano zan zo miki da mijinda na zaba miki.

Nan da nan gabana ya fadi na daure nace"to yaya Allah ya kaimu.

Yace" ameen .yaushe zakuyi resuming school?

Nace" next week inshaa Allah.

Yace" OK Allah ya bada sa,a ki gaida goggo Amina.

Nace" to yaya zataji na gode.

Daganan ya kashe sauke wayar nayi ina murmushi nace hmm lallai ni nafi kowa sa,a yaya yana hira dani har sirri muke yi dashi😜

Ina shirin Shiga wanka sai ga faiza da sakina sun dawo dama tunda na dawo gidan mama muke tare dasu yanzu ma kasuwa sukaje don yi mana shopping din komawa makatanta.

Sakina tace " a rumaisa sauki ya samu naga yau kam kina fara,a.

Faiza ta harareni hade da fadin to sarauniya sai kije ki duba abubuwanda kk ce a siyo miki din ai.
Hannu na daga mata " hey don't talk to me like this.ki bari sai sanda nayi ra,ayi naje na gani.

Zaro ido tayi hade da fadin " what!

Sakina tasa dariya hade da fadin ni kunga wanka zan shiga .

Faiza ta ce,wlh rumaisa kinci sa,a don bakida lfy amma kin dau bashi.

Ta fita nima binta nayi a dakin mama muka zauna nan na baje kayan ina dubawa.

Faiza tace,goggo kinga uban wahalar da mukasha amma muka dawo rumaisa ko sannu batayi mn ba saima rufeni tayi da balai.don nace tazo ta duba kayanta.

Mama tace" ai Ku rabu da ita bakin halinta ne ya motsa.

Nace" mama fa karya take.....

Faiza tace" ke ban fada miki ba raihana fa ta koma.

Da dan zaro ido nace "don Allah kunje gidane?

Tace" munje shine mama tace mn ta koma wai ba yanda su inna basuyi ba amma taki fir.

Dariya muka sa lokaci guda hade da tafawa.nace" sadiya zata mutu da bakin ciki.mama kinsan sadiya bakinciki takewa raihana don taga ta sami miji kamili ba kamar jafar ba.har admission yace min ya samowa raihana zata fara zuwa BUK amma part tym .

Mama tace" hmm in kuma ta biye wa sadiya zata yi asara don sadiya kam sai dai shiriyan Allah.

Faiza tace " goggo wlh idan zan gaya miki yadda na tsani sadiya sai kinji mamaki.

Mama tace" aa faiza ki bari ba kyau 'yar uwarki ne adduan shiriya kawai zamuyi musu.yanzu tashi ki shaga wanka kar wani ya sameki da towel haka.

Tace" goggo sakina ta Shiga wanka tun dazu ita nake jira.

Mama tace" aa tashi ki shiga toilet dina kiyi wankanki sai muje muci abinci tun tuni ku nake jira

Faiza ta tashi ta shige toilet .

Mama tace " to ke kuma hjy rumaisa tashi zakiyi ki tattara kayaiyakin nan ki kai dakinku.

Nace" yawwa wnn karon bana son komawa makaranta da soyayyen kaza.mama nafi son a soya min nama da yawa kuma ayi min stew ne.ni zan dinga siyan abinci ne bana son wani tarkacen kayan abinci da yawa

Mama tace" kudine dake haka bansani ba?

Nayi dariya nace" mama duk kudaden da kk turamin fa ban wani kashe sosai ba kuma gashi ya salman da ya salim suna turo min ga daddy ma yana turowa .kawu ma yana turowa wasu lokutan.

Tace" lallai Ku ' yan gata ne .yanzu kudin naki zai kai million daya ko fin haka?

Na danyi shiru snn nace " zasu danfi.

Tace " to me zai hana ki fara juyasu ne akan kashe kashen banzan nan.

Nace"mama business knn?

Tace" eh mn

Na dan turo baki nace" mama ni da nake ' yar mkrnta me ya hadani da wani business?

Tace " ke tafi can banson rashin wayo .waye gaya miki makaranta na hana kasuwanci?. Kina dai gani da kasuwancin nan na rufa mana asiri da bamu kai wnn matsayin ba a yanzu.

Nace " to mama sai dai na baki kudin sai ke ki juya mun.

Tace " to yaushe zaki koyi kasuwanci knn?

Shiru nayi tace" hmm ki yi tunani duk abinda kk yanke ki fada min.

Nace "to

Sannan na tattara kayaiyakin na kai daki nan na sami sakina har ta fito wanka nima na shiga.

****a kwana a tashi ba wuya gun Allah gashi har mun koma mkrnta karatu ya fara nitsa.

Ahmad kuwa sosai muka kara shakuwa gaskia ina samun kyaututtuka na ban mamaki a gurinsa ga kayayyakin sawa masu tsada na kece raini da yake siyo min ya kasance duk inda nabi sai bina ake da kallo
Kadan ne wayanda basu sanni da Ahmad ba a yanzu kuma yawanci yanzu kowa ta koma kirana da suna QUEEN OF BEUTY.ina jin dadin wnn sunan sosai.
Matasan yan makaranta da yawa in suna Neman taimako gurina suke zuwa don indai nayiwa Ahmed magana shikenan kawai .
Gaskia na sauya sosai fatana har wani sheki take sosai na zama yar hutu gabadaya ' yan hostel ma girmamani suke saboda 'yan canji

Doctor Hakeem kam tuni na ture batunsa a gefe.bama shi kadai ba harda sauran samarin.
Chapter 17 · 0% Book details