← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 128

Sashe 75

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunda daga ranar muka sami salama da daddare mu samu muyi bacci zuwa karfe biyun dare tfy tahajjud mukeyi da yaya mu barta a gida.da kyar take bude mana kofa in mu dawo.

Sosai na lura takejin haushina bare ma ta taga irin kayayyakin da ya salman ya siya mun masu tsadan gaske na adon sallah duk hsnkslinta ya tashi ranar wuni tayi a daki tana ta waya da 'yan uwanta tana fada musu.

Gaba ta karu don yanzu indai gani gata sai dai in kauce in bata hanya in ba haka ba sai dai tasa kafada ta tureni da karfi taja tsaki ta wuce tana zagina abin yana min ciwo don haka daya isheni rannan da naxo shiga kitchen ita kuma tazo fita tana jiran na kauce mata kawai taga na tsaya a bakin kofa.

Cikin tsiwa tace " dan Allah ki ban hanya in wuce kona tureki.

Takaraso da sauri ta ture kafadata zata wuce .

Da sauri na jawota na dawoda ita muna fuskantar juna na kalli fuskarta cikin tsanani fushi na sharara mata mari mai rai da lfy har ta sunkuya idonta nan da nan ya cicciko da hawaye !

Cikin zafin nama ta daga hannunta zata rama na rike hannunta snn nace " ko kinsan duk abinda kk yi ina tara miki ne to yau kam dubunki ya cika wlh idan kk kuskura ki kace tak anan sai nai miki shegen duka in yaso in kun isa kusa Salman din ya sakeni.

Sake baki tayi tana kallona cike da mamaki ta kasa fadan komai tuni na wuce na barta a wurin !!!

Fans na gode da kulawar da kk nuna min sosai Allah ya bar zumunci🙏🏻

Hauly ce👍🏻🥰
[10/9, 10:36 AM] +234 703 558 2498: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

*WANNAN* *SHAFI* *KYAUTACE* *A* *GAREKU* *MASOYAN* *KWARAI* 👍🏻🤗

*AL*- *FAHARI* *NOVELS* *ONLY*

Hauwa Ado 😄
D yuguda
Sadiya sulayman
Mum Abulkhair
Maman ummee
HAUWA.U M
Shauwa
Mamar Ramadan
Maman Amir
Aji Abubakar
Safiyya Atiku
Maman zee
Maryam Dango
Ummah bala B
Aisha Abdullahi
Maman Nabil.
Ummu hybat🥰

*RASHIN* *NAZARI* *FANS*

Mmn amcy
Maman baraka
Ummu aslam
Phertyma
Useexer
Basmah
Aisha Ardo
Aisha lafene
Mom ruky
Khadija
Maman al'amin
Maman Abba
Maam khyry
Ummu shahid
Laweezat imam
Halima
Harira Isa 38
Zynab

Duk wayanda basu ji sunansu ba su min uzuri ba hakan naso ba ayi hkr ngd🤗🤗🤗🤗🤗🤗🤗👏🏻

_🥰🥰🥰🥰Ina yinku sosai fans kamar yadda kk kaunar *RUMAISA* *SALMAN* nima ina matukar kaunarku Allah ya bar _zumunci_ _da_ _kauna_ _mai_ _dorewa_ _tnx_ _so_ _much_ 🥰🥰🥰🥰🥰🥰

_Hauly_ _ina_ _tare_ _da_ _ku_ a _kowani_ _lokaci_ 👍🏻👍🏻👍🏻😄😄😄😄

*PAGE* ➡69

*************A ranar ta tattara kayanta don tsabar munafurci zata tafi ni kuwa ko a jikina cewa nayi umma ta gaida assha in yaso taje ta fadawa adda A' i tazo ta sameni.

Tana fita ta hadu da hassan ya fito daga motarsa zai shiga gidansa don haka da sauri ya fara tambayarta me ya faru yaga tana kuka? Dake ya santa wasu lokuta ita take kai mishi abinci.

Kawai sai ce masa tayi wai na kamata na mata shegen duka alhalin batada lfy don haka zata koma gidansu.

Anan ya shiga rarrashinta akan kar ta tafi da kyar ya shawo kanta ta amince shine harda dauko mata jakar kaya suka dawo kawai naji ana buga kofa ina budewa na ganshi tsaye tare da ita sai harara data watso min.

Nan na fara gaisheda hassan ya amsa hade da fadin " haba madam me ya hadaki da kanwarmu har kk mata duka?

Cikeda mamaki na kalli madiha murguda min baki tayi na kalli hassan hade da fadin " ni ban daketa ba kawai.......

Ya katseni da fadin" its ok shikenan kawai ta koma don Allah ku zauna lfy pls madam i beg you

Nace " ba komai ni dama ban koreta ba.

Yace ok thank you.

Ya kalli madiha kauda kai tayi tace " nifa bazan shiga taje ta kasheni ba kawai zan zauna anan ka kira ya salman.

Murmushi yayi yace " come on kiyi hkr mana babu komai.

Nidai shigewa ciki nayi na barsu.

Shiru shiru banji shigowarta ba har na kuma lekowa don na bar kofata a bude amma abin mamaki sai ban ganta ba .

Don haka na maida kofata na rufe.

Na wuce daki naci gaba da harkokina har ya salman ya dawo bayan ya dan watsa ruwa a jikinsa ina kitchen ya sameni yace" sannu da aiki baby.

Murmushi nayi nace"yawwa ya aiki?

Yace" Alhamdulillah yau ina madiha ne banji motsinta ba tunda na shigo.

Na danyi shiru snn daga baya na kwashe duk yadda akayi na fada masa duk na tsorata kar ya min fada amma sai naji yace" kinyi abinda ya dace kuskurenki daya ne da baki kirani a waya kin fada min hassan ya dauketa ba .

Nace" ni ma bansan sun fita ba .

Dan tsaki yayi ya fita da sauri wayarsa ya dauka ya kira hassan ya tambayeshi ina madiha wai gata nan suna tare sun fita ya kaita ta sha iska ne.

Hankalin ya salman na lura ya tashi sosai don ko zama ya gagareshi sai kai komo yake a palo mamakine ya kamani nace " yaya lfy naga ka daga hankalinka ? Tunda yace suna tare ai shikenan zasu dawo ka kwanta ka huta.

Ya girgiza kai yace" rumaisa bazaki gane bane hassan fa ba mutumin arziki bane so yake ya bata mata rayuwarta........

Da sauri nace" haba yaya kasan me kk fada kuwa ? Ko ka manta a watan ramadan muke?

Murmushin gefen baki yayi yace" shiyasa nace miki bazaki gane ba din kawai kije kici gaba da ayyukanki.

Jikina a mace na koma kitchen.

Shiru shiru sune basu dawo ba har nine .ya salman duk ya gama cika

Tana shigowa naga ya tashi a fusace ya fita nasan gun abokin nasa zaije.

Ni dai ina ganin iko Allah ranar yana dawowa ya wuce dakinda madiha take banyi mamakin jin ihunta ba don a yadda naga rainshi a bace nasan komai ma zai aikata.

Da sauri na shiga na sameshi hannunsa rikeda belt dinsu na sojoji duk ya faffasa mata jiki da kyar na rikeshi ina ya salman kaiwa Allah ka rabu da ita karka mata lahani kaga fa duk ka faffasa mata jiki ? Pls ka barta yaya dan Allah mu tafi.......

Juyawa yayi ya fita ba tare da yace komai ba.

Na kalli madiha wacce take dunkule wuri daya tana kuka nace" hmm kinga abinda rashin kunyanki ya jawo miki ko don haka in kina da hankali yanzu sai ki san me kk yi.

Na fita kayana.

Washe gari da sassafe yace ta fita maza ya maidata gida.

Ba yanda banyi dashi akan ya kaita asibity ba amma muguntan su na sojoji ya hana shi ganin halinda ya jefata ciki haka suka tafi ko ya zasu kare da adda A'i ne oho.

Daga nan dai na samu zaman lfy a gidana ana saura kwana biyu sallah muka dawo kano.

Anan muka fara hidimar sallah cikin kwanciyar hankali ba takurar inna fa,iza ma sunzo kuma a kanon suka sauka .itama ciki yayi nauyi da kyar tashi ga ruma ma haka sakina ma ko yau ko gobe.bansan yanda zasuyi service dinnan ba.gaskia nima na fara sha,awar cikin nan Allah Allah nake inga na tsallaka wata amma sai wata yayi nitsa in mun fara expecting ni da ya salman sai period na yazo duk sai na shiga damuwa ya koma yana rarrashina .

Bayan sallah da sati uku mama ta dawo don dama ta yola ta sauka wai karkuso kuga yadda mama tayi wani irin kyau da haske gashi tayi jiki a bakin maman sakina naji wai mama tana da ciki ni duk kunya ne ya rufeni gani nake kamar ta tsufa da haihuwa in na fadi hakan ya salman ya kama yi mun dariya yace " ba wani ke dai kk ganin haka don kinga ta haifi kamarki .

A lokacin aka gama ginin gidan mama na kano.wai karkuso kuga kudinda aka kashewa gidan nan abin sai wanda ya gani ga sabuwar mota dalleliya da ya sake sai mata ya komai na more rayuwar duniya daddy yazubewa mama a gidan nan nima kaina inada dakina a gidan masha Allah sai dai fatan alkhairi.

Gagarumar walima muka shirya a wnn gidan na tarewar mama .faiza cewa tayi ba don cikin nan da ya mana cikas ba Allah na tuba da casu zamusha.

Dariya mukayi hade da tafawa nace" karki damu sisi sai ta haihu kamin nan kuma kun sauke sai mu hada casun?

Zaro ido tayi tacs" sis karkice mun goggo Amina nada ciki ?

Hannu nasa na toshe mata baki nace " ke karki daga murya ta jiyo mu tazo ta sauke min . ....

Shigowar ruma ya katseni tace " ihsan oganki yazo ku tafi .

Bata fuska nayi nace " haba ya salman shi kuma bayan munyi dashi kwana zamuyi dukanmu anan shine zaizo .

Sakina tace" kema kinsan zaiyi wuya ya salman ya iya barinki tunda sanin kanki ne tun kan kuyi aure ma in yazo daga lagos bai sameki a gida ba sai yaje ya daukoki ko a makaranta ko a gidan Alh Aminu...

Harararta nayi nace " wai waya sako bakinki ne ke kuma kiji da nauyin jikinki don Allah ba wanda ya tambayeki tarihi.

Sukayi dariya ruma tace " ki dai tashi ku tafi in kuma kin tsaya bata lokaci yanzu ya shigo ya samemu anan ya sauke mana kwandon balai.

Faiza tace" hmm to wai shi yaya don ya hkr na yau kadai mene ne?

Sakina tace " bazai hkr ba mutum da matarsa ke yanzu ra'is in ya ce kizo ku tafi wlh nasan da gudu zaki debi jiki ki bishi duk da nauyin cikin nan naki .

Faiza tace" tsab ma kuwa ksmar kin sani.

Muna cikin haka mama ta leko tace" wai rumaisa ba,a gaya miki salman yazo kun ajiyeshi sai faman jira yake gashi dare nayi.

Shagwabe fuska nayi nace" mama don Allah ki rokeshi na kwana.....
Chapter 75 · 0% Book details