Sashe 110
Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya tafi inda suke da sauri ko ganin gabansa bayayi yana zuwa wurin ya janyo farida da karfi ya sharara mata mari saida duk wurin suka nitsu.
Da sauri ya fizgota sai mota Allah yaso da driver yazo da bazai iya tuki ba tsabar bacin rai .
Farida kam kuka takeyi sosai.har suka isa gida bai saurara mata ya shiga dukanta baji ba gani ruma ta tsorata sosai ta rikeshi tana"kayi wa Allah da manzonsa ka barta haka kar ka ji mata ciwo don Allah kayi hkr.
Ya salim yana huci yace"rumasau kinsan inda naje na samo yarinyan nan?
Ruma ta girgiza kai tana dada rikeshi.
Cikeda takaici yace"bakiga kayan jikinta ba ? A wurin casu naje na samesu da wnn dan iskan yaron....
Nan da nan ruma ta dafe kai ta zauna kujera hade da fadin innalillahi wa inna ilaihir rajiun.
suka kalli farida wacce take kuka kamar ranta zai fita .Salim yace"tashi ki bani wuri .
Tana fita ruma tace"kaga ko shiyasa nace maka gara mu gayawa mahaifinta dukkan halinda ake ciki domin gabadaya musan matakin da zamu dauka akanta.don ni kwanaki na gayawa ihsan abinda ake ciki nasan matsalolinda take ciki na tun bikin nan ne ya hana cewa komai.amma ni gaskia a shawarce inaga gwara kawai su sani domin su tsananta yi mata addua.
Ya salim ya zauna ya dafe kai snn yace"rumasau gaskia ni ina ganin kamar abun kunya ne a wurina in fuskanci salman da wnn maganar kamata yayi mu tashi tsaye kawai akan case din farida don haka ni zanyi shawaran yadda zamu bullo ma lamarinta ba tare da mun sanar da iyayenta ba kuma kema abinda ya faru yanxun nan don Allah karki fadawa rumaisa domin tana cikin wani hali tun na bikin nan kuma kinga bata da lfy ma .
Ruma tace "hakane Allah ya kyauta.don dazun ma ta kirani take ce min jikin amaryar ya warware har ma za,a kawota nan gidan Ya salman na Abuja snn tace min don Allah kar in bari farida tace zata je gidan.gabadaya yanayinda take min maganar kasan tana cikin tashin hankali .
shiru sukayi cike da tunanin yadda zasu bullo ma lamarin farida.ranar ba suyi bacci ba a zaune a palo suke har gari ya waye.
Farida kuwa kwana tayi tana kuka mimi ta dinga bata hkr hade danunan mata abinda takeyi bai dace ba shiyasa ake mata haka ba wai dan an tsaneta ba.
Aikuwa kamar mimi na kara ingizata ne tace"an tsaneni mana in ba haka ba ina kema every weekend in ya fadil yazo daga zaria daukanki yake ku tafi wajajen shakawa har dare kuke dawowa amma ban taba jin dad ko mum sunce komai ba amma ni duk sun bi sun takurani saboda basu suka haifeni ba....
da sauri mimi tasa hannu a bakin farida hade da fadin " haba farida meyasa kike irin wnn maganar wlh ba haka bane...
Ture hannun mimi tayi da karfi tace"ni ki rabu dani goben nan in Allah ya yarda zan bar muku gidanku tunda an fara cin zalina.
Haka ta kwana tana kuka gari na wayewa ta gama kintsa kayanta tsaf mimi tayi maza taje ta sanar da su daddynsu ga farida can tana shirin tfy kano.
Da sauri suka fita suka isketa a harabar gida da kayanta zata fita.Ruma tayi saurin riketa tana cewa "ina zakije farida?
Kai tsaye tace gidanmu zan koma tunda kun tsaneni ba kwa sona.
Ruma ta girgiza kai yayinda hawaye ya ciko idonta tace"aa farida ba tsanar ki mukayi ba kawai muna fada miki gaskiane kiyi hkr kizo mu koma kinji ?ki fada min duk abinda kk so 'yata.
Ta rike hannun farida wacce ta fizge da sauri ta tafi wurin Ya Salim tana kuka yace"daddy don Allah ka maidani gidanmu ina son yin magana da daddyna.
Ya salim idanunsa suka kada sukayi jazir tsabar bakin ciki amma ya daure ya hadiye ya rike hannun farida yace"shikenan farida zan mayar da ke kamar yadda kikace amma kizo muje ciki kisha koda tea ne kan nan in shirya se mu tafi.
Don haka ta amince suka tafi ciki.Ruma kam ta kasa hkr daki ta koma tana kuka ko kadan bata son farida ta bar wajansu don tun batayi shekara uku ba take gabansu.
Haka suka kasance cikin tashin hankali a ranar gabadaya.
*******Ya salman kuwa bayan ya isah Abuja misalin karfe goman dare .ba kowa a gidan don haka ya wuce toilet ya yi wanka ya shirya cikin kayan baccinsa anan ya fara tunanin shin yaje gun nafisa ko ya barta?
Ya jima yana tunani kamin daga bisani ya gama yanke hukunci ya tashi ya dauki wayoyinsa ya fita ya rufe dakin ya tafi dakinda yake tunani can aka kaita.
Can ya sameta kuwa tana kudundune cikin bargo cike da mamaki ya karasa bakin gadon ya yaye bargon da sauri .
Ita kuwa a tsorace ta kurma wani ihu jikinta na rawa don bata taba tunani shi bane a zatonta wasune daban don tunda aka watse aka barta a gidan ita daya da taga dare yayi gabadaya ta tsorata duk da ma ga sojoji masu tsaron gidan.
Da sauri ya rumgumeta jikinsa hade da cewa"ke nine.
Snn ya saketa ya fahimci gaba daya a tsorace take.
Anan ta nitsu a hankali ta sunkuyar da kanta kasa cikin jin kunyarsa.domin tunda aka fara maganar aurensu da duk wani jinya datayi bata taba kebewa dashi ba sai yau don haka gabadaya sai taji kwarjininsa ya mamaye koina dakin.
Shi kuma zuba mata ido yayi Allah kadai yasan me yake tunani a ransa.
Can ya numfasa ya fara magana "Nafisa bazaki iya zama a gidan nan ke kadai ba ni kuma kinga ba mazauni bane don haka maganar gaskia shine ki shirya mu koma kano goben nan .kuma bana son jin wasu kananan maganganu don haka ki tsarkake zuciyarki mu zauna lfy.rumaisa bata da matsala ko kadan kuma tana da hkr zakiji dadin zama da ita fiye da tunaninki don haka ki daina bin maganar su Adda A'i matukar kina son mu shirya kinajina?
Kai kawai ta daga mishi .yayinda yaci gaba da yi mata magana har da nasiha kuma ta gamsu yayinda jikinta yayi sanyi sosai.
Anan ya umurceta da ta tashi tayi alwala suyi nafila ta ma,aurata.
Kanta a sunkuye tace mishi tana period.
Baiyi magana ba ya tashi yayi nafilarsa snn yaje ya dauko musu ledar da ya shigo da ita na drinks da gasassun kaji yazo ya baje su yace ta sauko taci.
A kunyace ta sauko ta zauna kanta a kasa har lokacin yace mata"wai ke ba kya gajia da wnn sunkuyar da kan ne?
Snn yayi murmushi cikin zolaya yace"ko don banzo da abokai na mun siyi bakin amarya bane?
Da sauri nafisa tasa tafin hannunta duka biyu ta rufe fuskarta tana murmushi.
Shima murmushi yayi yace"to shikenan kiyi hkr yanzu ki dago kanki kici naman nan nasan kina jin yunwa ko dai na baki a bakine?
Da sauri nafisa ta girgiza kai snn ta sa hannunta ta dan fara ci.
Shikam bayan ya danci toilet ya tafi ya wanke hannunsa hade da kuskure bakinsa ya dawo ya kwanta ba tare da yace mata komai ba.
Da farko tunanin halinda ya barni yaso ya hanashi bacci don yasan ina cikin damuwa snn gashi ina daukeda juna biyu amma daga baya daya tuna yanda na sakoshi a gaba akan lallai sai yazo Abuja sai yaji haushi ya kamashi ya dan ja tsaki ya gyara kwancciyarsa da bai biyo takan nafisa ba bacci yayi awon gaba dashi .
Washe gari kuwa bayan ya dawo daga masallaci ya isketa har ta gama shirya kayan sawanta a jaka .
Cike da biyayya tace mishi "yaya ina kwana?
Ya karaso gabanta hade da fadin lfy ya tsoro?
Da sauri ta sukuyar da kai tana murmushi snn yace"duk kin gama shirinki koh?
Tace"eh na gama.
Yace"to ina zuwa.
Daga nan suka kulle koina ya taimaka mata tasa kayanta a mota suka kama hanyar Abuja basuyi nitsa sosai ba ya salim ya buga mishi waya yana tambayarsa yana Abuja ne ko kano.
Yace yanxu nake hanyar barin Abuja zan tafi kano a mota amma.
Ya salim yace"to nima gani nan zuwa kanon da farida.
Ya salman yace"da sassafen nan snn lfy zaka zo da faridan?
Ya salim yace"lfy lau sai mun karaso kawai.
Ya katse kiran .nan ya salman jikinsa ya bashi zuwan bana lfy bane.
*****Kasancewar jiya ban yi bacci ba gabadaya saboda tunanin ya salman da amaryarsa.ina idar da sallar Asuba ban San sanda bacci barawo ya saceni ba daga zaune nake bacci sosai.
Buga kaina da nayi a jiki drawer shi ya tashen na dafe kaina da yake mun ciwo dama ga damuwa ga rashin bacci .
Kama kan nayi da karfi ina karanto addua.....
Bansaki kan ba naji kamar horn din motarshi.
Ban San sanda na saki kan na mike da sauri na tafi window kasancewar window din bedroom dina tana facing harabar gidan.
Ina daga labule Rass! Zuciyata ta tsinke.ganin motar ya salman ne.
Naji wani irin bacin rai da bakin ciki kamar na hadiye zuciyata na mutu.
Da sauri na fita daga dakin na nufi harabar gida ko ganin gabana banayi tsabar bacin rai.
Can na hangoshi ya fito gabadaya sojojin gidan sun zo suna kwasan gaisuwa.
Da sauri na nufi can wurinshi a lokacin da ya juyo shi kuma ya bude gaban motan .kawai sai ganin nafisa nayi ta fito
Bansan sanda na tsaya na saki baki ina musu kallon mamaki ba.
Itama ni take kallo daga fitowarta fuskarta daukeda tsoro da fargaba .
Ganin yadda muke kallon kallo yasa shi riko hannunta a hankali suka nufo inda nake ka min su karaso tuni na daga musu hannu.
Na kalleshi cikin tsantsar mamaki nace" me zan gani?Nafisa a gidana?me ya faru?
Fuskarsa ba yabo ba fallasa yace "lfy ta dawone.
Na zaro ido hade da fadin what! Wlh bazai yiwu ba wnn karon bazan dauki iskanci da rainin hankali da aka mini a baya ba bari kaji ni bazan zauna da Nafisa a gidan nan ba.