Sashe 16
Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Na girgiza kai sannan nace,ko kadan dana San matarsa yar uwarsu Salima ce da ban amince da shi ba amma yanzu bai baci ba don ban amsa masa akan maganar aure don haka daga yau na rabu da shi kayi hkr yaya ni ba wanda zan kuma amincewa da shi .na bar maka zabi ka zaba min mijin da kaga yafi dacewa da rayuwata.
Hawayene ya zubo min
Jikinsa ya mutu sosai yace" ki daina kuka maganar ya wuce.
Hannunsa ya saka yana gogemin hawaye abinka da farin fata tuni fuskata tayi ja musamman gefen da ya mareni.
Nadama yayi sosai gabadaya tausayina ya gama mamayeshi ba shiri ya jawoni jikinsa cikin sanyi n murya yace " kiyi hakuri ba,a son raina na miki haka ba rainane ya baci dazun
Nikam tuni na dada kwanciya jikinsa dama son jikine dani😜
Rumgumeni yayi yace " kanwata insha Allah zan zaba miki miji Wanda zai rikeki da amana ya kyautata miki ya sanyaki farin ciki kinji?
Kai na daga masa idona lumshe ina jin yadda kirjinsa ke bugawa.
Ya rasa dalilin da yasa yaji baison dagani daga jinkinsa .
Mun dauki tsawon lokaci a haka.kowa da abinda yake ransa.
Gyaran murya muka jiyo da sauri na dago daga jikinsa shima ya sakeni jikinsa a mace sosai.
Ya salim ne ya shigo ganin mu a haka ba karamin mamaki ya bashi ba.
Don binmu yayi da kallon tuhuma gabadaya.
Kunyane ta kamani kamar na nitse a kasa.
Yayinda ya salman ya daure yace " yaushe ka karaso?
Tsaki yayi ya wuce dakinsa ba tare da ya ce komi ba.
Ya salman ya bishi da kallo sannan daga baya ya juyo da kallonsa gareni a cikin wata kasalalliyar murya yace" ki tafi gida kuma kisha maganinki kar ki manta.
Nace " to
A sanyaye na juya na fita.
Ya kalli agogo hade da fadin subhanallah what har magriba ya wuce ko kiran sallah banjiba.
Ya salim da ya fito daga daki ya amsa masa da fadin" ta ya zaka ji kiran sallah da ba don nazo ba asuba ma zaiyi kuma baza kaji kiran sallah ba.
Ya kalli ya salim fuska daure baice komi ba ya wuce toilet alwala ya dauro ya fito .
Zai wuce daki sai ya lura ya salim yana ta binsa da kallon tuhuma.
Yace" salim bana son irin kallon nan da kk min faa
Salim ya ce" hmm guiltiness! Gani nayi alwala kawai kuma kamata yy kayi wankane kamin alwala.....
Ya katseshi da fadin " kai! Dama dan iska ka daukeni OK bari in idar sallah inzo.
Ya salim yace" ina nan jiranka domin akwai tarin tambayoyi da zan maka .
Tsaki yy ya wuce ciki.
Nikam isa na gida direct na wuce sashin daddy a Palo na sami fa,iza ,Sakina,sadiya,r
Raihana da Zainab suna kallon wani series da akeyi a joyprime(Ashoka samrat)
Wucewa daki nayi bance wa kowa komi ba naje toilet nayi alwala nazo nayi magrib anan na zauna har nayi isha daga nan na jawo pillow na kwanta abubuwanda ya faru tsakanina da ya salman ya dinga dawo min.
******"sai tambayarka nake meye tsakaninka da yarinyar nan kayi shiru kana kallona.
Ya salman yace" so kake kaji?
Salim yace kwarai ma kuwa.
Salman yace"SONTA nakeyi.
Cike da mamaki ya salim ke kallonsa.
Nan yaci gaba da baiwa ya salim labarin duk abinda ya faru har zuwa lokacin da ya samemu tare.
Ya salim ya sauke ajiyar zuciya yace " me na gaya maka abaya ? Ka tsaya kana jan aji wai kai baka son ta rainaka waye waye.....
" da ace tuntuni ka bi shawarata ka fito mata da sonda kk mata da tuni an wuce wurin kuma wlh da bazatayi wasu samari ba.salman tun randa muka fara ganin rumaisa a kauye na lura da kai na fahimci sonta kk.bare kuma da ta dawo nan naga irin special kulawa da kk bata sai na gaskata sonta kk kuma na fahimci cewa Salima tausayi take baka ganin za,a hadata aur......
Salman ya katsrshi da fadin ya isa mallam don Allah ni dai yanzu kaina yy zafi.salim rumaisa ta fara rikitani ina tsoron kar taje ta fara soyayya da wani pls salim ka ban shawara ya zan yi?
Ya salim yace " waya San maka .ba kace zaka zaba mata miji ba? To waye mijin?
Salman yace" nima bansani ba fada kawai nayi.
Ya salim ya ce " OK ba matsala ga shawara me zai hana ka gabatar dani a matsayin Wanda ka zaba mata?
Salman ya zuba masa ido hade da fadin " serious faa
Ya salim yace" wlh kuwa am very very serious.
Shiru salman yayi har na tsawon minti biyar sannan yace" OK shikenan.
Ya salim ya mike hade da fadin " yawwa na gode Dan,uwa ina jiran ranar da zaka yi introducing dina a gun GIMBIYAR MATA RUMAISAH.sai da safe.
Kai kawai ya daga masa
Salim na shiga daki shima ya tashi a sanyaye ya wuce daki ranar baiyi bacci har gari ya waye yana idar da sallar asuba ya tafi airport don yin booking jirgin Lagos yaci sa,a kuwa sha daya ya wuce Lagos ba tare da ya sallami kowa ba kuma wayarsa ya kashe don kar a nemeshi🤦🏻♂
Comment and share
Hauly ce👍🏻😍
Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹
👨🏻🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻🚒
*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚
~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```
➡ page 15
**********Shiru shiru ba Wanda ya ganshi har shadaya kuma gashi layinshi bai shiga.
Abba da Inna duk sun damu.ya salim kam jikinshi yana bashi Lagos ya koma don haka ya kira Mohd abokinsa ya tambayeshi.
Yace" eh yanzu ma suka rabu.
Ya salim ya kalli Abba yace" wai wani kiran gaggawa aka masa ya tafi ba shiri wayarsa kuma ta sami matsala ne shiyasa.
Abba yace to ai shikenan Allah ya taimaka.
Sai lokacin inna ta saki ranta.
Muna shirin tfy gidan mama ya Salim ya shigo muna hada ido naji kunya ya kamani na sunkuyar da kai .
Faiza ne tace " yaya kun sami yaya salman din?
Yace " eh yana Lagos
Wani irin ajiyar zuciya na sauke hade da hamdala a raina.
Ya salim ya ce" rumaisa ya jikin?
Nace" da sauki yaya
Yace kinsha maganinki?
Nace" eh nasha.
Yace" OK Allah ya kara lfy sai ki dinga kiyayewa kuma.yanzu ina zakuje?
Fa,iza tace" gidan goggo Amina
Yace" Ku bari sai da yamma na kaiku in yaso ki kwana .
Tace" kai yaya don Allah mu dai ka....
Sai lokacin sakina ta yi magana" shikenan yaya kawai da yamman sai muje.
Yace" yawwa kanwata rumaisa faa?
Murmushi nayi nace " Allah ya kaimu.
Yace "amin.
Yana fita faiza ta rufe mu da balai nida sakina sai dariya muke mata muna cikin haka raihana suka shigo da Sadiya .
Sadiya ta kalleni tace "Rumaisa don Allah ki min girki mana Inna tace kafarta na ciwo yau ni kuma kinga da kyar nake komi.
Faiza tace " mu fita zamuyi fa ba ga raihana ba tayi miki mana
Raihana tace" ke ni na gajine komi ni nakeyi a dakin Inna gaskia ni na gaji wlh tunda bani kadai nake cin abincin ba.
Sakina tace " amma dai kunsan rumaisa bata da isashen lfy ko kuma hayaki ma tada mata ciwo zaiyi kuma ya salman ya fada yace duk wani aikin kura ko hayaki ko ruwa ta nisanceshi kuma kar a sata.
Sadiya haushi kamar ta mari sakina tace" don na yau kadai shine me ? Don Allah rumaisa ki taimaka min.
Fai,za ta karba" ba fa inda zataje don bata warke ba ko sai na gayawa ya salim ne.
Anan fa suka kama sa,insa harda sakina da raihana.
Shiru kawai nayi ina kallonsu har suka gaji dan Kansu suka bari.
Na numfasa sannan nace"duk Allah ya huci zuciyoyinku abin bai kai ga haka ba .
Na kalli sadiya nace " yanzu da kinyi hkr kin zauna gidanki yaushe hakan zai faru dake ? Na fada miki ki daure ki koma komai mai wucewa ne a rayuwa ....
Ta tari numfashina da fadin " ke nifa bazan koma gidan dan iskan nan ba.in ma shi yake aikoki.
Sakina tace " ba kinji matsalarki ba wlh sadiya kima kanki fada duk nan kece fa babba .ki dinga hkr mana.
Tsaki taja ta tashi tana cewa" don na sake muku ne kk raina ni.
Fita tayi ranta a bace.
Na kalli raihana nace" wlh raihana ki dai na biyewa sadiya har yanzu mallam na min zancanki
Anan muka rufam mata nida sakina faiza kam fushi tayi dama tun dazu na lura ' yan halin sun murdo.
Raihana jikinta a mace tace,wlh nima na gaji da zama gidan nan banda wahala ba abinda nake sha duk aiki inna da sadiya sun sakarmin ni daya a gidana kuwa girki kawai da gyaran dakin sadiq nakeyi duk sauran aiyukan ina da mai aikina.
Nace "to kinga lallaba ki koma ki huta.
Ashe duk abinda muke fada a kunnen sadiya da ta labe bata tafi ba don haka tana gama ji taje ta mayarwa inna harda Karin gushiri.
Aikuwa inna ta tura zainab ta kirani ni da raihana duk mun dauka a kan maganar girkinne.
Amma muna zuwa palonta ta rufe raihana da fada har kamar zata daketa tana" Ashe bakida hankali bansani ba da rumaisa kk hada kai ki zagi 'yar uwarki?
Raihana tace" laa inna wai tace mun zageta ? Wlh ba Wanda ya zageta....
Sadiya ta Karba" naji Ku sarai rumaisa harda cewa take inawa raihana bakin ciki ne.
Inna ta buga salati nikam tsabar mamaki na kasa cewa komai