← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 128

Sashe 111

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na nunata da yatsa nace " wata daya da suka wuce aka kawota gidan nan a matsayin amaryarka ta yanki jiki ta fadi ta suma 'yan uwanka suka sakoni a gaba da zagi ciki harda mahaifiyata sukace mu mukayi tsafi don mu wargaza aurenka da Nafisa.

Hawayene masu zafi suka gangaro bisa kumatuna na ce"jiya jiyan nan aka kai maka ita a gidan ka na Abuja ka tafi.snn yau ka daukota kuyi sammako kuzo min gida kace ta dawo?

Ko kallo ban isheba dama jiya da haushina ya tafi Abuja.don haka ya kalleta yace "ke shiga ciki ina zuwa.

Ta wuce jikinta a sanyaye na bita da kallo har ta shige.

Sannan na dawo da kallona gareshi.nace" shikenan tunda haka ka zaba ni zan bar maka gidan ka yanzu ba sai anjima ba kaje ka zauna da matarda mahaifiyarka da 'yanuwanka suka zaba maka.

Wucewa yayi ba tare da yace min komi ba.

Kamar zan fashe don bakin ciki nayi ciki a zuciye Na dauki jakata da wayata da key din motata .

Juyawan da zan yi sai ganin mutum nayi tsaye ya zuban ido fuska daure.

Ban kulashi ba Na saka takalmina Na karaso bakin kofan ba tare da na kalleshi ba nace ban gu in wuce.

"Ina zakije? Ya fada can kasan makoshinsa.

Shiru na masa .

Juyawa yayi zai fita yace min Salim yazo da Farida suna palona .

Daga nan ya fice

Zuciyata ce ta buga nace Farida da sassafen nan me ta ballo kuma?

wayyo Allah da wanne zanji ni RUMAISA?

Na ajiye jakata na tafi side dinshi a Palo na samesu suna zaune shiru Farida na zaune a kasa kanta a kasa.

Na karaso na zauna jikina a mace na kalli Salim nace "ya Salim ina kwana?

Cike da kulawa ya amsa min lfy RUMAISA.ya jikinki ?

Nace"jiki da sauki Alhamdulillah

Shiru ya biyo baya daga bisani ya Salim ya gyara zamansa yace" to kun ganta nan duk yadda naso ta zama mutum abin ya faskara RUMAISA ke kam kinsan komi gameda halin ta dama Salman Kaine muke boyewa saboda gudun zuciyarka amma yau an wayi gari fareeda da kanta tace min in dawo da ita gaban iyayenta ina muzguna mata dan bani na haifeta ba.

Zaro ido nayi na kalli Farida nace "fareeda dama rashin hankalin naki har ya kai haka? wai shin ya salim suwa suke hure mata kunne ne haka?

Salim yaci gaba da fadin hmm har yanzu bata rabu da Farouq ba rumaisa maganar da nake miki jiya har karfe dayan dare na ganota a wurin club suna tare bayan duk tsaro da na sa akanta sai da tasan yadda tayi tayiwa momynsu wayo ta fice jiya gaba daya bamu yi bacci ba Dan bakin cikin fareeda na rasa me zan mata a rayuwa don ta rabu da Farouq ..........

Sai lokacin ya salman yayi magana ta hanyar katse ya Salim da fadin " waye Farouq din?

Ya tambaya yayinda ya dauki Kofin ruwa dake gabansa yana sha.

Salim ya danyi shiru sannan yace hmm Farouq dan gidan Alhaji Ahmad umar ministern Ab.....

Tuni ya salman ya kware ya kama tari.

Nikam na kara zaro ido a tsorace don ban taba sanin Farouq Dan Ahmad Umar ba ne sai yau .

Kamar da wasa ya salman tarin sai tsananta yakeyi ya Salim ya mike da sauri ya isa wurinshi

"Sannu don Allah karka daga hankalinka kan wnn maganar.

Hannu ya daga masa sannan yace ba komi.

A hankali fareeda tace sannu daddy.

Ya dago jajayen idanunsa ya kalleta sannan yace " zo nan.

Ta mike ba tare da fargaba ko dar ba don tasan yana matukar ji da ita baya muzguna mata duk zafin sa.

Ta karaso ta zauna kusa da kafarsa.

Ya fara magana"fareeda haka kika zama? Me yake damunki don Allah ki fada min koma me kk so zan miki amma bana son wnn banzar dabiar taki.

A shagwabe ta fara magana tace daddy ni bana son inje makaranta ni zan yi aure ne....

Nikam na bushe a zaune Dan tsabar mamaki.

Yace" waye ne kk so?

Tace Daddy Farouq........

Ya mike tsaye idon nan ya kara yin jazir yace fareeda ni bazan yarda Dan wajen Ahmad ya aureki ba koda kuwa babu maganar aure tsakaninki da munir bare kuma kin gama amincewa munir kk so har munyi akan in ya dawo daga kasar waje zayi bikinku.don haka bazanyi magana biyu ba don ni ba mutumin banza bane.Farida ko kinaso ko ba ki so munir shine mijinki...Sannan kinga wnn?

Ya nuna ya Salim yace"Dan uwanane banda kamarsa idan kin kyautata masa kamar ni kikayiwa idan kin masa biyaiya kamar ni kikayiwa haka nan idan kika masa rashin biyaiya kamar ni kk yiwa naji kince don ba shi ya haifeki ba to bari kiji duk duniya bakida Ubanda ya wuce Salim.ina so ki Sani akan Salim zan iya rabuwa dake.don haka se kije ki nemi wani uban bani ba tunda kince Salim ba mahaifinki bane.

Tunda ya fara maganar kuka takeyi .

Ta durkusa gabanshi tana daddy don Allah kayi hakuri ka yafe min na tuba.....

A fusace ya bugeta da kafa ya fice ciki.

Ta na kuka ta mike ta iso gabana ta durkusa tace mama don Allah kuyi hakuri wlh ......

Tsaki nayi nace don Allah tashi gabana Mara hankali me zakice min?

Tana kuka ta juya gun ya Salim tace daddy don Allah kayi hakuri ka yafe min wlh na gane kuskurena

Dagota yayi yace na yafe miki fareeda Allah ya shiryeki.

Sannan ya mike yace ni na tafi.

Nima na Mike nabi bayansa

A bakin kofa mukayi kicibis da Nafisa batace mn komai ta wuce ciki na bita da kallo sai naga ta wuce direct dakinsa.

Wani irin kishi naji to waye nuna mata turaka bayan dazu tazo?

Tabe baki nayi.

Bayan ya Salim ya tafi na dawo dakina na rasa me yake min dadi a rayuwata dole ne kawai inje in sami ya salman domin mu tattauna maganar fareeda.duk da ma na lura fushi yakeyi 'yan halin nasa sun murdo gaban goshi.

Na tashi na fita a babban Palo na tarar da khalilullah yana kallo.

Yana ganina yayi murmushi yace mama ina kwana?

Nace lfy Babana ina ka shiga tun da safe ban ganka ba?

Yace na tafi gidansu Innah ne a can nayi breakfast ma.

Na gyada kai nace yayi kyau babana.jeka duba min daddyn ka yana Palonsa ne?

Yace to
Sannan ya mike ya tafi ba,a jima ba ya shigo yace mama yana nan.

Nace "Nafisa fa?

Yace aunty Nafisa dazu ta wuce kitchen.a raina nace har ta karbi girki knn? Hmm amaren zamani.

Nace to ina fareeda?

Yace na ganta ta fita dana tambayeta tace zata kai karar daddy gun innah.mama me ya sami sister ne?

Na danyi shiru sannan nace maganace mai tsawo kar ka damu ina zuwa.

Na wuce palon ya salman a zaune na sameshi yana waya da abokan kasuwancinsa na sami guri na zauna har ya gama.

Ya zuban ido sannan yace lfy?

Na girgiza kai nace ba lfy ba nazo ne mu tattauna yadda zamu bullo ma lamarin fareeda kamin yafi karfinmu.

Yace hakane ina jinki.

Na gyara zama nace " ni yaya a ganina gara a bar ta tayi auran ta auri Farouq din tunda akansa ne take wannn......

Ya katseni da fadin lallai bakida hankali kina tunanin cewa ni SALMAN zan dauki 'yata ta cikina in bawa Dan Ahmad aurenta! Ni na yanke hukunci koda zatayi aure yanzu to munir ne zata aura bare ma kuma makaranta zata tafi.har sai munir ya dawo.

Nace "yaran nan fa na zamanin yanzu daban suke da na da tunda kaji ta bude baki bataji kunya ba tace ma aure takeso kuma ga wanda ta zaba to ka barta kawai karkace zaka tursasa mata domin watarana zata bijire.

Kallona yake rai bace sannan yace" zata bijire min in dai halinki ta dauka da banzar dabiarki........

Raina bace na Mike nace OK haka kace to bari kaji ni 'yata aure zatayi kuma Wanda takeso zata aura Farouq din tunda aure bai haramta tsakaninsu ba ni a matsayina na uwa na gama yanke nawa hukuncuin.

Har zan tafi yace tsaya!

Ya mike ya karaso gabana ya zuba min manyan idanunsa da sukayi jazir Dan bala'i yace " sai yanzu na fahimce ki rumaisa wato saboda Ahmad tsohon saurayinki ne shine kk son dansa ya auri 'yarki ko?
Kai tsaye nace eh hakane sai me?kasancewar Mahaifiyar Farouq din Salima tsohuwar budurwarkane don haka me a ciki?

Na juya zan tafi ya fincikoni da iya kacin karfinsa wani irin kykkyawan riko ya min.

Sai faman kwatar kaina nake kokarin yi na kasa.

Murmushin mugunta yayi yace "yanzun kin fahimci banbanci dake tsakanina dake?

Ya sassauta min rikon yace ni ne nakeda ikon aurad da fareeda ga duk Wanda naso bake ba don na fiki karfi a wajanta.ke kanki a karkashin ikona kk don haka bakida ikon zartar da komi a gidan nan.

Hawayene ya ya ciko idona fal har ya fara saukowa don takaicin ya salman.

Yana kallona yace kina da wani abu da zakice kuma?

Na girgiza mishi kai kawai.

Ya sakeni hade da fadin good girl haka nake so.

Fita nayi na tafi daki kuka na kama yi kamar raina zai fita

Karar wayata ce na jiyo a kan bedside drawer ban kula ba har ya tsinke.

A Jere aka kira sau uku ana hudun na lalubo wayar ban lura da kowaye ba nayi answering.

Muryana a sarke nace Salamu alaikum.

Muryar Inna na jiyo tana " to uwar makirai annamimiya ba sallamarki na ke bukata ba. ki fada min me yasa kk ce Salman ya dawo da Nafisa kano alhalin jiya jiya aka kai ta Abuja ?

Cikin muryar kuka nace inna banice nace ya dawo da ita ba nima kawai sai ganinsu nayi sun yo sammako.....
Chapter 111 · 0% Book details