← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 128

Sashe 122

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk hankalinsu na kan computer can sai gashi ta fara nuna komai daga sanda ya fita zai tafi masallaci sallar asuba.ita kuma ta shiga dakin ta zauna bakin gado kusa da twins ta buga tagumi alamun tana jiransa can kuma kamar an minsineta sai ta tashi ta kama yan dube dube harda bude masa drawer.bincike ta shiga yi sosai har Allah ya bata ikon gano side din drwar da na ajiye kudin ganin jaka yasata ta dauki gashi da nauyi tana budewa ta zaro ido cikeda tsoro da alajabi nan ta shiga waige waige ganin ba wanda ya ganta yasa ta rufe jakar ta dauka tasa cikin hijabinta ta fita da sauri.........

Ganin haka yasa nafisa ta fara mimmikewa nan ta zube musu a wurin ta shiga yin wasu abubuwa irin nasu na masu aljanu.

Addai madiha nabila gabadaya jikinsu ta mutu ji sukayi kamar kasa ta tsage su shige

Yayinda sadiya taketa harararsu tace"ba gashinan ba gaskia ta bayyana yanxu kuma me zakuce?

Raihana da sa,adatu kam tuni suka kama nafisa suna tambayarta lfy ?

Inna kuwa gabadaya duk A.C palon gumi takeyi sosai inna ta shiga salati tana dafe da kanta wanda yake matukar sarawa.

Ya salman ya tashi kallonsu yayi gabadaya snn yace"idan kun gama shawarwarinku a dawo min kudina domin sisi idan yayi ciwon kai a ciki......

Girgiza kai yayi hade da kwafa ya fice abinsa.

Tab koni ban taba sanin ya salman yasa cameras a part dinsa ba .

_Muje_ _zuwa_ _fans_

Hauly ce🥰🙏🏻
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰

*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``

*PAGE* ➡101

***********Gabadaya jikinsu ya mutu sosai kunya ya kama adda A'i don bata taba tunanin asirinsu zai tonu nan kusa ba.

Sadiya ta kalli nafisa tace"ki gama duk wani haukanki kuzo ki fitar ma ya salman kudinshi.macuta kawai.

Ta kalli Inna tace"Inna yanxun ba kin gani ba? Tuni na rigada na gane komai ina ta kokarin fahimtar da ke amma kika ki to yanxu gashi nan kingani kuma kinji don haka yanxu sai kisan matakin da zaki dauka.......

Raihana ta katseta da fadin "haba sadiya don Allah ki bari za,a fahimci juna a hankali.yanxun bakiga halunda nafisan ke ciki bane?kuma yanda kk daga murya kowa zai iyaji kuma abin kunyane a wurinmu don dukkanmu anan yan'uwane ba bare ko daya .....

Habawa ai raihana kamar sake tunxuro da sadiya tayi don sake daga murya tayi tace"wayan nan macutan sune yanuwan nawa?Allah ya kiyaye bari kuji na fada muku gabadaya yanxu ba wani sauran mutunci da ya rage tsakaninmu da ku domin mun gane ku din ba masoyanmu na gaskia bane don haka daga yanxu kowa ya kama gabansa.ku tattara yar uwarku ku fice mana daga gida kuma ku tabbatar kun maido ma yayana kudinshi ehe.

Haka sadiya ta zage ta dinga zuba rashin mutunci.duk tsit sukayi suna jinta .

Yayinda raihana da sa,adatu suke ta yiwa nafisa addua suna tofeta har ta nitsu bacci ya dauketa .

Inna kam ba magana tunda salman ya fita take jin kanta kamar zai tsage don haka daga karshe tashi tayi ta koma daki.

Da kyar raihana ta lallaba sadiya ta bar maganar.yau adda A'i taga ta kanta.madiha duk rashin kunyarta haka ta hkr suka zubawa sadiya ido.

****Lokacinda ya dawo gida ransa a bace matuka da abinda su nafisa sukayi masa.don haka direct dakinsa ya wuce bai nemeni ba zama yayi bakin gado yana juya wnn alamari a ransa.

Ni kuma ina can na gama shirin tarbansa tsaf don nasan lokacin dawowarsa yayi haka ma su hanifa na shiryasu cikin kayansu mai kyaun gaske se kamshi muke tashi.ganin sun koma bacci yasa na kira aunty samira muka shiga hira anan tace min"abubuwanku sun gama haduwa fa ihsan zan turo miki kuma komai a rubuce.naki daban na farida daban.don ita akwai wasu takardu ma dana hada mata ki bata kuma ta karanta zai mata amfani sosai a zamantakewar aure don nasan ba komai zaki mata bayani ba.

Nayi murmushi nace gaskia kam aunty .wani abun da nauyi fada wlh duk da ma farida ba kunya ne da ita ba har wasu tambayoyi take min masu nauyin gaske .

Aunty samira tayi dariya tace hmm ke kuma kina kunyar 'yar fariko?

Nace"aa wlh kawai dai wani abun se inga be kamata ta sani ba.

Aunty samira tace"ke dai ihsan kinji dadinki wlh.to banda abinki me ya rage yarinya ta kusa aure ba gara tasan komai ba.kuma ai ko baki fada mata ba wasu zasu gaya mata don haka gara ki zage ki cire kunya ke da farida yanxu kawayene.

dan dariya nayi nace"tou shikenan aunty zan daure.

Itama dariyan tayi snn tace"Allah dai ya kaimu lokacin bikin rai da lfy.bari na barki naga magrib tayi.

Daga nan mukayi sallama tashi nayi na fita palo zuciyata cike da dsmuwan rashin dawowar ya salman har yanzu

Fitowata knn se gashi nan ya fito daga part dinshi sanye da jallabiya ash colour.

Da sauri na karasa gunsa cike da mamaki nace"yaya dama ka dawone ban sani ba?

Kamar bazai amsa ba har ya wuce snn yace"na dawo .bari naje masallaci kar na rasa jam,i.

Nace"to a dawo lfy.

Amin ya fada tuni ya wuce na bishi da kalllo.gaskia na lura yau ransa a bace yake sosai kawai dai baison nuna min ne.

Bai sake shigowa gidan ba har sai bayan isha yanxun ma sashinshi ya wuce.

Khalil ne ya shigo ya sameni yace min"mama daddy yace kije ya dawo.

Nace"ok to.ina munir ne ?

Yace "yana palo da sister farida.
Nace"to kar ku jiramu kuje kuyi dinner dinku.muma muna zuwa kuma in ka fita kace larai tazo yanxu.

Yace min to
Ya fita ba dadewa larai ta shigo nace"larai kunci abinci?

Tace,eh hajia munci.
Nace"to ga nan su hanifa ki kula dasu da kyau ina zuwa yanxu.

Tace"to hajia .
Na tafi gaban mirror na dan gyara fuskata snn na fita.

A bedroom dinsa na sameshi zaune gaban computer dinsa sallamata ta saka shi dagowa yana amsawa.

Snn ya maida hankalinsa kan computer din.
Bakin gado na zauna ina kallonsa.

Kusan twenty minutes dakin shiru snn ya kashe system din ya tashi ya karaso bakin gadon yayinda ya cire eyeglass din idonsa ya ajiye kan drawer muryarsa a sanyaye yace"Rumaisa.

Nima jikina a mace nace"na,am.

Ya danja numfashi snn yace"duniya ta zama abin tsoro.domin cike take fal da makiya .wai ace ni su adda A'i zasu hada kai su cuceni .....

Bai karasa maganar ba saboda wani irin bacin rai da ya rufeshi.
Zuba mishi ido kawai nayi don har yanzu ban fahimci inda ya dosa da maganarsa ba.

A hankali ya riko hannayena duka biyu snn ya shiga gaya min komai tundaga farko har karshe abin mamaki duk wani plan din adda A'i tun kamin ya auri nafisa ya sani bayan ya aureta duk abinda suke kullawa ya sani .haka nan yasan duk wani alakar nafisa da suraj.

Nidai tsoro da mamaki suka cika min zuciya na kasa cewa komai .

A hankali yace"rumaisa yanda inna take sonsu kamar me musamman adda A'i inna ta sota fiye dani domin tasha musguna min akanta .inna ta ba adda ai dukkan wata kulawa da gata ta jata a jiki fiye dani amma kinga wai yau aka wayi gari ta hada kai da yanuwanta zasu cuceni.....

Sai lokacin nace"kayi hkr yaya duk da nasan basu kyauta maka ba amma bana son ka dauki wnn maganar kasa a ranka bare ya dameka.kawai ka barsu da Allah shiyasan yadda zaiyi dasu.kuma ni bana son ka juya musu baya saboda wnn matsalar da kk samu yanxu.nafisa ma ka yafe mata kuma kaja mata kunne ta dawo kuci gaba da zamanku.na tabbata yanxu tunda suka gane kasan komai zasu nitsu.

Girgiza kai yayi yana murmushi snn yace"shikenan.

Nima murmushin nayi nace"yawwa yaya na gode.yanxu ka tashi muje muci abinci.

Yace"ba abinci nake bukata ba baby.
Nace"to me kk bukata?

Ya zuba min ido cikin wani irin salon kallo da ya sanya ni jin tsigar jikina na tashi da sauri na tafi na fada kirjinsa maida hannu yayi ya rumgumeni sosai yayi wani irin ajiyar zuciya yace"baby wlh ina missing dinki sosai .nasan bazan dawo dai dai ba har sai na kasance dake my dear pls a taimaka min.

Lumshe ido nayi nace"doctor yace sai na huta tsawon watanni shidda kamin nsn....

Cije lebensa yayi da karfi ya dada kamkameni yace"wlh bazan iya ba baby dole ne mu koma gun doctorn nan ya sake yin wani bayani.
Ba shiri na saki murmushi snn na dago na kalleshi nace"to shikenan yanxun tashi muje kasan yaran nan idan basu ganmu a dining ba suma basa taba cin abinci.

Ya dan dafe kai snn yace "to muje.don bazan iya barinsu da yunwa ba duk da ma banajin son cin komai.

Tare muka tashi ina fadin hakan dai zaka daure komai zai wuce insha Allah.

Yace "hakane my dear.

****Nafisa kuwa har dare ta tashi da matsanancin ciwon kai saida adda Ai ta bata paracetamol tasha da kyar ta dansha kunu.ta kwanta a lokacin sadiya da raihana sun koma gidajensu tuni.

Adda A'i kuwa kasa bacci suka yi suna ta shawaran yadda zasu bullo ma wnn lamarin don su gyara kuskurensu.

Sa,adatu tace"hmm yanxu baga irinta nan ba kunxo kunyi abinda ya dameku.

Madiha ta harareta hade da fadin "ke dan Allah yi mana shiru da zancan banza.

Snn ta kalli adda ai tace"wlh adda da nasan wnn abin kunya da nafisa tayi ne aka kiramu da banzo ba.

Nabila ta ce "koni ma wlh

Adda A'i ta karba tace"hmm ai ku bari kawai ni nan wlh da na sani da tuni na zare kaina na barta yar banza ta karata dasu.

Hawayene ya zubowa nafisa a hankali tace"Adda duk kece sanadiyar sanya ni cikin wnn ....

Adda A'i ta katseta ta hanyar zaro ido tac"nice nace kiyi sata!!!
Chapter 122 · 0% Book details