Sashe 86
Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta fita sadiya ta kalli raihana tace"ke kuma munafuka anan zaki kwana ne?
Raihana ta daure fuska tace"munafurcin me na maki ? Anan zan kwana sai me kinada matsala ne?
Sadiya tace "don me zaki kwana anan yaranki kinje kin zubewa innah tanata faman dawainiya dasu alhalin tana fama da ciwon kafa ke kinzo zaki kwana anan.....
Raihana tace"au yarana ne zasu zamewa innah dawainiya ke naki yaran da kk zube mata ba dawainiya bane koh?
Tace"to aini yanzu zan tafi kuma can zan biya in daukesu mu koma gida.
Raihana tace"se ki hada da su gabadaya ku tafi gidan naki tunda duk yarankine kokuwa?
Tsaki sadiya tayi snn ta fita tana cewa "zakuji da munafurcinku ai.ni kunga tfyta.
Sakinah tace"ummah ta gaida assha .
Tana fita raihana tace " yanzu zataje ta shirya min karya da gaskia gun innah .
Rumah tace " ko muma baza mu tsira ba ai.
Nace" hmm kema dai raihana tunda kinsan halinta dama baki tanka ba wlh.
Haka mukaci gaba da tattauna irin halin sadiya kamin daga bisani na bacci ya yi awon gaba dani na barsu ruma na ta hira .
Kwanan su ruma biyu suka koma da sakina raihana ma haka a ranar da suka tafi aunty samira kuma tazo naji dadin zuwan aunty samira sosai musammn ma da ta sauka a gidana ranar kwana mukayi muna hira duk gajian da nayi na daure.
Anan ta kawo min tarkacen mu na mata hade da yi min bayani sosai tana ihsan yanzu kam zagewa fa zakiyi sosai fiye da da don yanzu kinga ku biyu ne musamman ma da naga kishiyar taki idanu a tsassayen nan snn kuma kinga dama kince mun bazawara ce don haka ki kula sosai kinji?
Nace"Insha Allah aunty.
Tace"yanzu yaushe salman din ze dawo?
Nace"inaga sai nan da sati mai zuwa.
Tace"yawwa to don Allah ki dage ki fara ki fara kintsa kanki indai kinbi yadda na fada miki to fa kema zaki zama amarya zakiga yadda zai dinga nan nan dake.
Murmushi nayi nace"to aunty.
Snn ta nuna min wasu kayayyakin bacci sunfi kala ashirin tace"zuwanmu dubai da daddynku ne na siyo miki su nasan zaki matukar jan hankalin surukina dasu don wlh se kinga nawa da nasaka nima........
Kunya ne ya dan kamani nace"na gane aunty
Dariya tace"to shikenan tunda baki son jin karashen labarin .
Haka muka kwana hira washe gari karfe sha daya ta wuce gidan mama bata wani zauna ba ta wuce airport ni kuma ina nan ina ta faman gyare gyaren jikina wanda a cikin kwana uku rak har na fara jin sauyi nima .
Amarya kuwa tsakaninmu gaisuwa kawai kowa na harkar gabanshi .sai in sadiya tazo su kule a daki suyi ta gulmarsu
Kwanana goma da dawowa ya salman ya dawo unexpected ko waya bai mana ba ina kwance a palon kasa naci kwalliyata mai kayatarwa su sa,a da munir basa nan amarya kuma na kitchen .kawai sai gashi ya shigo muna hada ido bansan lokacinda na yi wani tsalle na tafi na fada jikinshi .
Dagani yayi kamar wata baby ya shiga juyawa dani a palon muna dariya sannan ya saukeni kankujera ya zauna shima hade da rumgume sam a jikinsa kamar zai maidani cikinsa yace"baby gaskia nayi matukar farinciki da kk dawo lfy.
Ya fada yayinda ya sumbaci goshina nayi murmushi nace"yaya wlh nayi missing dinka sosai.
Sha fa gefen fuskata yayi yace"adduan me kk mana baby?
Nace" komai ma da muke bukata saida na roka mana yaya musamman adduan samun baby....
Da sauri yace"wow! Naji dadi Allah ya ansa my dear mu sami baby.
Ya fada yayinda ya tura hannunsa cikin rigata yana shafa cikna a hankali yana murmushi yace"Allah ya bamu masu albarka.
Duk abinnan da mukeyi salmah na ganinmu can dining side a yayinda take shirya dining din gabadaya ganin yadda ya salman ya rikice a kaina take mamaki sam bata taba ganin ya salman na fara,a ba duk tunaninta ta dauka baya dariya amma sai gashi ta gani dariya yake sosai .don haka ji tayi kirjinta na bugawa kamar tazo ta shakoni.
Ta dai danne hade da karasowa cikin tfyr daukar hankali tana murmushi tace "amin ya Allah karkuce na sa muku baki a maganar ku.
A tare muka juya da ya salman muka kalleta da sauri na bar jikin ya salman shi kuma kallonta yakeyi har lokacin fuska ba yabo ba fallasa yace"salmah
Murmushi tayi hade da kwantar da murya tace"na,am honey barka da dawowa .tunda kace min kana hanya na shiga kitchen na hada maka girki na musamman honey na yanxu muje tukun kayi wanka ko dai?
Gyada kai yayi snn yace hakaneh thank you so much.
Snn ya kalleni yace"hajia bari inzo koh?ki jirani pls
Murmushi karfin hali nayi nace "sai kun fito.
Tuni salmah ta shige gaba rike da jakarsa shi kuma yana biye da ita a baya.suna haura stairs sai tfy take tana jujjuya mazaunai.haka kawai na fara tunani in sun shiga daki rumgumeta zaiyi yayita nuna mata soyayya su manta dani a palo wayyo zuciya!
Nan da nan naji hawaye ya cicciko idona ban iya na daure ba dakina na koma na kulle na fada gado na shiga rera kukan da bansan a wani matsayi zan fassarashi ba!!!!!!
Hauly ce🥰👍🏻
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹
👨🏻🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻🚒
*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻
*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚
*DEDICATED* *TO* *UMMI* *ABDALLAH* 🥰
*BESTOWED* *TO* *ZUWAIRIYYA* *ABDULWAHAB* ( *real* *mum* *afrah* )🥰
~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~``
*PAGE* ➡78
**************Kusan 30minutes snn yaya ya kirani a waya wai in sauko muci abinci nace"to.
Na tashi na shiga toilet na wanke fuskata naxo gaban madubi na maida kwalliyata snn na fita na iske su a dining table nima naja kujera na zauna.
Salmah ta kalleni da murmushi a fuskarta tace"hajia me za,ayi serving naki?
Na danyi shiru ina tunanin me zanci don bana kwadayin komai wlh.
Ya salman yace" ki bata pepper soup kawai nasan ba wani cin abinci take so da daddare ba
Salmah tace an gama ranka ya dade.
Bayan ta gama itama ta gyara zama muka fara ci nikam sai faman jujjuya spoon nake a cikin bowl abincin sam baya shiga.
Ya salman ya kalleni cikeda kulawa yace" my dear ya bakicin komai ko ba kya jin dadine?
Nace"wlh yaya nayi loosing apatite dina ne bana jin dadin komai .
Yace"ko dai muran ne har yanzu? Kina ma shan magungunanki?
Nace"eh inasha.
Yace"to ki daure ki danci abincin nan ko kadan ne Allah ya baki lfy
Nace"ameen.
Sai lokacin salmah tace " sannu Allah ya sawwaka.
Na danyi murmushi nace"ameen na gode da kulawarku gareni.
Bayan mun gama cin abinci ana ya ajiye mu a palo ya fara yi mana magana akan zamantakewa yayi ta mana nasiha masu sanyaya jiki daga karshe yace " don Allah ku zauna lfy karku bari aji kanku ni kuma zan yi kokari yin adalci a tsakaninku .
ya kalleni yace"Rumaisa na sanki da hkr dama to ki kara akan wanda kk dashi babu komai ku zauna lfy shine farin cikina da kwanciyar hankalina .
Na gyada kai nace"Insha Allah yaya zamuyi duk abinda kk so.
Ya kalli salmah yace"kema ina fatan hakan daga gareki salmah ku zauna lfy.
Ta kwantar da murya hade da cewa"insha Allah honey lfy lau zamu zauna Allah ya baka ikon yin adalci a tsakaninmu.
Yace "ameeni na gode muku da hadin kai da kk bani Allah ya muku albarka.yanzu se maganar raba kwana.inaga kwana bibbiyu ai yayi ko dai?
Nan naji gabana na faduwa hmm anxo wajen gaskia idan akwai abinda ke daga min hankali bai wuce inga salmah ta shigan min turakar miji ba sai dai ya zanyi itama mijintane.
Maganarsa ce ta dawo dani daga duniyar tunani yace"rumaisa bakice komai ba.
Nace"ba komai yaya hakan yayi amma ina bukatar wani alfarma a gunka.
Yace" ina jinki my dear.
Na danyi shiru snn nace"ina bukatar na huta na wata daya kan mu fara raba kwana.
Nan da nan ya sauya fuskarsa yayinda ita kuma salmah ta dan washe baki da alama maganar ya faranta mata rai.
Bai amsa min ba kawai dai ce mun yayi muje na rakaki kije ki kwanta.
Na tashi muka tafi side dina muna shiga bedroom ya kalleni fuska daure yace"don me zakice a barki se kin huta har na one month kina haukane akan me zan barki har one month bakida lfy ne?
Fuska sake nace"haba yaya one month ne fa ba one year ba nide kayi hkr don Allah so nake na huta sosai ne.
Ya kamo hannuna duka biyu ya zaunar dani kan bed snn shima ya zauna yana kallona yace"baby kiyi hkr idan akwai wani abu daya bata miki raine.wlh baby bazan iya one month dake a gidan nan ban kusanceki ba.yanzu ma hkr kawai nakeyi don Allah karki min haka .
Zare hannuna nayi cikin nashi nace"yaya sai kace ba amaryace da kai ba don Allah ka barni na huta pls pls pls don Allah.
Na fada cikin kwantar da murya.aikuwa mikewa yayi cikin bacin rai ya gyada kai ya fita.
Nikam binsa nayi naje na rufo kofan side dina gabadaya na dawo na kwanta na kama kuka alhalin ni nayiwa kaina hukunci.
Da safe kuwa kamin mu fita muyi break fast ko wacce sai da ta kure gindin akwatinta batun kamshi ba,a magana koda muka hadu a dining wani irin kallo salmah ke min duk jikinta ya mutu don tasan na fita kyau nesa ba kusa ba .
Shikam oga ko a jikinsa tunda ya amsa gaisuwata bai kuma ce mun komai ba sai ma daddaure mun fuska da yakeyi.don haka can tsakaninshi da amaryarshi suke dan hira jefi jefi.
Ni kuma saida na tabbatar munir ya koshi snn nace "to oya ka tafi kaje ka yi ta tusa karatunka kamin time din islamiyya yayi.
Yace"to momy .
Yana tfy nima nayi maza na gama cin abincina na tashi hade da fadin "to a huta lfy !
Har nayi nitsa yace"ki shirya zamuje gida yanzu.
Na kalleshi kamar bashi yayi maganar ba saboda kwata kwata ba side dina yake kallo ba .
Murmushi nayi nace"to dama a shirye nake bari na dauko veil dina da jakata kamin nan kun gama.