← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 128

Sashe 12

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadiya ko kan ta ankare tuni ya fara sauke mata belt ko ta ina baya ko sararawa .
Ihu take yi tana wayyo inna yaya zai kasheni wayyo mama don Allah yaya kayi hkr zan koma

Inna kam shiru ta yi tana kallonsu sai da mmn Sakina ta tashi ta rike hannun ya salman tace " salman lfyrka kk dukan matar mutum da ciki? Ka Wa Allah ka barta zata koma ai .

Ya kalli sadiya rai bace yace zaki tashi ki tafi ko sai na kashe ki da duka?

Aikuwa da sauri ta mike takalminta a hannu ta yi waje. Ya bita a baya.

Nikam sai godewa Allah bake da bai rufeni da duka dazu ba.

Na idar da sallar isha inna tace nazo na dauki abincinsu kamar nace mata bazani ba don tsoro haka na daure don zainab bata nan .

Na isa gidan har zanshiga Palo na jiyo muryarsa yana fada kasancewar kofa a bude na danyi baya na ajiye abincin a bakin kofa har na juya sai naji yace" look Salima in har sai Ahmad zai auri rumaisane kamin a bani aurenki to sai dai a bari don wlh bazan taba yarda Ahmad ya hurewa rumaisa kunne ba.

Na zaro ido yayinda na dafe kirji .

Sai naji muryarta cikin tsigar lallashi ta na" my dear don Allah ka bar Ya Ahmad yaci gaba da soyayya da rumaisa hakan shine zaisa daddy na ya yarda muyi aure kaga fa tuntuni kk so a fara maganar aurenmu amma su dad sunki saboda ya Ahmad to yanzu Allah ya karbi rokonmu ya Ahmad ya daina kulani yanzu ya dawo rumaisa yake so baka ganin wannan wata damace muka samu.....

Ya katseta da fadin " sai yanzu na fahimceki Salima ke muguwace .nifa bari kiji ba don komai na jajrce da son aurenki sai don ina tausayin hadaki da Ahmad da za,ayi don kinfi kowa San in halinsa na shaye shaye da koyawa yaran mutane tantiranci.amma ke kina cewa wai na amince Ahmad ya batawa kanwata rayuwarta ? Don kawai in aureki to bari na sake jaddada miki Salima idan akan rumaisa ta yi soyaiya da Ahmad gwara na rabu dake.

Muryanta naji ta na kuka tace " shikenan dama ba sona kk ba yaudarace kawai na gode.

Nima tuni na fara sheshshekar kuka ban ma San ta fita ba .sai jin muryar ya salman nayi kusa dani yana " Rumaisa me ya sameki?

Na dago fuskata da ya jike da hawaye na kalleshi amma sai na kasa magana kawai durkusawa nayi gabansa naci gaba da kuka.

Jikinsa a mace yake kallona......

Hauly ce👍🏻😍......
[05/07, 15:10] Aufana 4rel Marubuciya: 🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

_Wannan_ _page_ _naki_ _ne_ *UMMI* *ABDALLAH* _na_ _gode_ _kwarai_ _da_ _irin_ _kulawarki_ _gareni_ _Allah_ _ya_ _saka_ _da_ _alheri_ 🥰🥰😀👏🏻

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```

Page1⃣1⃣

Ya daure yace" shikenan taso muje ciki.

Ba musu na tashi na dauki abincinsu ya wuce gaba na bishi baya.

Bayan mun zauna ya dan numfasa yace" bansan me yasa kk kuka ba amma dai nasan kinji maganata Salima. Rumaisa ko dai kina son Ahmad?

Girgiza kai nayi nace" yaya ni bansanshi yau ne haduwarmu ta farko kuma ni dama banjin zan soshi.

Yayi ajiyar zuciya sannan yace " to meyasa kk kuka?

Na share hawayen da ya ke zubowa nace" bana son ace nice silar rabuwarka da Salima bayan kun dade kuna soyayya.

Shiru yy tsawon lokaci na dauka ma ko maganar tawa ta bata masa rai ne har ya kasa magana.
Don haka nayi kasa da murya nace" kayi hkr idan maganar da nayi ta....

Ya girgiza kai yace" baki bata min rai ba.kawai abinda nake son ince miki shine ki dinga sanin irin mutanen da zaki na mu,amala dasu.domin duniya ta zama abin tsoro.

Na gyada kai nace" hakane yaya

Yace " bansani ba kila kina da ra,ayin yin aure idan kk sami Wanda kk so.bazan hanaki ba kar ki ga abinda ya faru dazu kiji tsoro.sai dai faa ki Sani bazan taba yarda ki auri mutumin da bai cancanta domin nayiwa goggo Amina alkawarin zan kula da dukkan lamuranki don haka bazan taba yarda kiyi mu,amala da gubatattun mutane ba.ki kula da kyau.

Na daga mishi kai hade da fadin insha Allah yaya bazan watsa ma kasa a ido ba.

Yace " shikenan kina iya tfy.

Na dan Sosa kai nace" uhmm yaya dama....

Nayi shiru na rasa ta inda zan fara maganar.

Shiru yayi yana saurarena jin nayi shiru yasa shi fadin" shikenan ki tafi sai kin tuno jeki.

Na daure nace" yaya dama shawarace nake son in baka in ranka bazai baci ba.

Yace" ina jinki.

Na Sosa kai nace" uhm dama dama....nace ....me ..zai zai hana idan iyayen Salima sunki ka aureta.....ka ...auri ...uhm uhmm....faiza kawai.

Ina gama fada naji zuciyata na bugawa ina jiran saukan tuni na dafe kumatuna da hannuna duka biyu.

Duk abinda nake yana kallona sannan yace" sai dai ki nemo min wata amma fa,iza kam tuni wani ya rigani.

Na girgiza kai nace" bata da kowa yaya take so.

Kai tsaye yace " bana son ta ki nemo min wata kawai yanzu ina nan ina jira sai naji daga gareki.tashi kije dare nayi.

Na mike jikina ba kwari bakina ya Jan yo min masifa ni ina nasan zan samowa ya salman budurwa.gaskia fa,iza da ya salman sun Sani a matsala babba.

Da wnn tunanin na bar dakin shikam bina yayi da ido har na fita na hadu da ya salim da rais a waje sun dawo a mota muka gaisa ya salim yacewa ra,is " baka gani ba saboda ita salman yaki yarda muje meeting din friends wai ya gaji wato so yake mu tafi ya samu yy hira da rumaisa.

Murmushi nayi nace" kai yaya ba fa haka bane abinci na kawo muku yanzu.

Ra,is yayi murmushi yace" ba wani nan mun ganoku tuni.

Dariya nayi nace" wlh ba komi abincinku na kawo.

Ya salim yace" shikenan idan tayi tsami ma ji.

Ni dai na musu sai da safe na wuce gida.ina Allah Allah kar In sami inna a daki. Aikuwa banci sa,a ba ina zuwa tace" ke kuma daga kai abinci kk je kika zauna ? Wai ina kk je ne? Don nasan tun dazu ba gidan kk ba tunda su salim yanzu dawowarsu salman kuwa nasan ba dariya ma yake miki ba bare ince gunsa kk zauna.ina kk je?

Na danyi shiru sannan nace inna yaya ne ya Sani aikin shirya masa kaya a drawer.

Ina fada na wuce ciki bina tayi da kallon tuhuma amma tayi saurin watsarwa taci gaba da harkokinta.

A kwanakin kowa sai da ya fahimci salman ya sami sabani da salima don kuka ta dinga yi tazo ta gayawa inna ta fadawa ya salim harma da sadiya don shirme😜

Inna kam bata ji dadi ba ta tambayi ya salman yace " shi dama ba wani son ta yake ba tausayi take bashi ganin tana da hankali amma ake son hadata aure da wani shashasha mara tarbiyya.

Inna tace" hmm salman knn Salima ta gayan komi saboda Dan,uwanta yace zai auri rumaisa.........

Yace" inna Ahmad fa ba mutumin arziki bane zai batawa rumaisa rayuwarta ba kuma auren
ta zaiyi ba.

Tace" to sai me? Waya fada maka rumaisa zatayi abin kirki? Bari kaji indai amina ce ta haifi rumaisa to rumaisa bazata taba zama ' yata gari ba.don ma kaji da kyau don haka ka fita harkanta taje tayi duk abinda take so ba ruwanka.Salima kuwa ita tafi dacewa da kai don haka ga dama ta samu karkayi wasa da shi.

Shiru yy yace " inna Ahmad fa ba auren.....

Ta katseshi da fadin" na shiga uku ina maka maganar Salima kana min maganar rumaisa .ai sa,a ma taci da Ahmad yace yana sonta Dan babban gida irin nan sannan uwa uba mahaifinsa gwamna?ai ba Wanda ya kaita sa,a in dai zai aure ta da bakun fentin da take......

Ya katseta da fadin " kawai inna ki bar maganar nan babu dadin ji.ni zan tafi in kina bukatar wani abu ki turo zainab.

Ya fita da sauri ransa a nace".

Faiza kuwa koda mukayi waya na fada mata duk yadda nayi da ya salman.

Shiru ta danyi sannan tace" hmmm rumaisa kinsan meya faru? Ina cikin damuwa sis.

Nace " me ya faru ne sis?

Tace hmmm wai kinsan me ashe tuntuni wai yaya
Ra'is wai sona yake tuntuni babu Wanda ya fadan a cukinsu wai suna jiran sai na fara University kiji wani al,amar kuma don Allah?

Cikeda mamaki nace" waya gaya miki?

Tace" shekaranjiya suka shigo Zaria dukansu ai shine fa suke fadamin.kinga yanda yaya ra,is din ya rikice daga ganina ko kunyan su yaya baiji ya dinga min sambatu?

Dariya nayi nace" wayyo sisi na aikuwa guy din ya hadu wlh ki amince daga ganinsa mayen love ne.ke kuma dama haka kk so ai na sanki da mugun jarabar tsiya aure kk so ido rufe.

Tace"ai aure abin so ne sai dai fa nafi son jarumi Wanda za,aita harka ba gajiya kinga shiyasa nake son yaya salman saboda ance sojojin sunfi iya harka in mace ta shiga hannunsu sai ta yabawa aya zakinta😜

Zaro ido nayi nace" to shine kuma kk dagewa so kk ki wahalane?

Tace" ke ni fa tuni na gane type dina.

Nace " ban gane ba.

Tace wlh na gane ni HARIJA ce

Da sauri nace" what!🤭wlh faiza baki da kunya .

Tace gara na fada miki gaskia don ni inaga ma bazan iya karasa makarantan nan ba aure ba kar inje in lalace gaskia

Dariya nayi nace kai faiza.
Tace " wlh serous nake miki wnn maganar har cikin raina.

Nace to shikenan yanzu dai shawaranda zan baki ki amince da auren ra,is din tunda kinga ya nuna da gaske yana sonki.batun jarumta kuma kuma ki bari in anyi auren kya bamu labarin don daga ganin idanunsa shima fa Dan hannune kamarki.

Tace" Allah dai yasa ai ban isa na bijire ba yanda su yaya suka dage shi kuma uban gayyan cewa yy auren a karshen wnn shekaran za,ayi yanzu muna watan hudu .
Chapter 12 · 0% Book details