← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 128

Sashe 88

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salmah ranar farinciki kamar tayi yaya da ranta tun a airport take ta mannewa ya salman tana ta zuba mishi shagwaba har muka isa gidansu innah .bayan mun gaishesu muka koma gidanmu .innah sai faman shan kunu take yau ma sai dai naci sa,a yau bata jefeni da bakaken maganganu ba.

Muna isa gida munir kamar zaiyi ya da ransa da murna ya salman ya daukeshi yana dariya yace"big boy dan wata daya da bama nan ne ka wani kara tsayi haka ? Masha Allah naji dadin ganin big boy dina cikin farin ciki ina aunty sa,a?

Yace"tana ciki daddy.daddy ka kawo min tsarabar allura?

dariya mukayi ya salman yace"big boy allura kuma doctor kk so ka zama knn?

ya dagawa ya salman kai
Ya salman ya gyada kai yace"wow daz good !Allah ya nuna mana rai da lfy .

Yace"amin.

Salmah tuni ta wuce sashinta ta barmu da a palo mun biye wa munir sai hira muke anan sa,a ta fito cike da fara,a tayi mana barka da dawowa hade da gaishemu

Ya salman yace"ina zainab kuma?

Sa,a tace"adda sadiya ta aiketa gidan addah raihana dazu.

Yace"sadiyan tana nan ne?

Tace"eh tana side din aunty salmah.

Yace " ok

Muna nan zaune kuwa sadiyan ta fito tayi mana barka da dawowa ya salman bai amsa ba kawai ce mata yayi "ana kk zo kika tare yaran naki kuma kin barsu da waye?

Shiru tayi ta da da sunkuyar da kai.
Girgiza kai yayi yace"Sadiya knn wai ke har yaushe zakiyi hankaline? Anya sadiya zakiyi abin arziki a rayuwarki?

Yayi shiru yana kallonta snn daga bisani yace"koda yake bazan ma bata bakina ba.

ya mike ya wuce sama abinsa
Dagowa tayi ta kalleni hade da fadin"to wai kallon me kk min ke kuma?

Nace"hmm kin tsargu knn ?

taja tsaki hade da fadin "daga dawowarku har yaya ya fara min fada sai kace wata karamar yarinya kuma don wulakanci a gaban sa,a.

Ta wuce fuu tana ciccika.

sa,a tayi dariya tace"aunty mu isa side dinki na gyara miki komai ki samu ki huta.

Tashi nayi muka tafi a bedroom muka zauna nace"sa,a me ya sami sadiya ta lalace haka?

sa,a tayi dariya tace"aunty labari mai dadi ne albishirinki?

Nace"to fa goro fari sol!

Ta sakeyin dariya tace"bayan tfyanku bai dade ba sadiya ta samu sabani da jafar ya mata dan banzan duka sai kinga yadda ya faffasa mata jiki satinta daya a asibity da kyar ta fara gane mutane.......

Hannu na dagawa sa,a hade da fadin"haba sa,adatu wnn shine labari mai dadin har da yi mun albishir ?to meye abin dadi a cikin labarin ?kemafa macece

Dariya ta shiga yi sosai nikam binta nake da kallon takaici tace"wlh aunty sadiya ta fara girbar abinda ta shukane alhakinki ya fara kamata don haka bana bakin ciki ko kadan da abinda ya sameta.don ma bakiji farkon labarin bane.

Shiru nayi ina kallon sa,a tace"hmm kinsan su innah duk tunaninsu sun kama jafar a hannune suna juya shi son ransu ai ? To ashe ba haka bane jafar yana can yana sheke ayarsa da matan waje sadiya bata da labari.ita a ganinta tuni ta mallakeshi shine kawai ranar ta koma gidanta ta tarar dashi da wata 'yar makwabciyarsu wacce take kula da yaran sadiya in ta fita yawon banzanta ashe sun dade tare kuma a gidan suke harkarsu sai ranar ne kawai dubunsu ya cika tazo ta iskesu haka.karkiso ki ga irin haukar da sadiya tayi ranar gabadaya sai da ta tara musu mutanen anguwa ta debi tafasashen ruwa ta watsa musu a jiki shine jafar din ya fusata ya mata danbanzan duka se kinga yadda suka tara jama,ar anguwa sadiya ta dauki wuka wai wlh sai ta kasheshi.maganar kamar da wasa har ya isa gida nan da nan innah ta sabi hijabinta taje gidan don tayiwa sadiya magana anan jafar ya kama zagin innah sai da ya mata tass tukun snn yace ya saki sadiya saki biyu ta tattara 'yarta su bar mishi gida kuma a bar masa yaransa .

Tunda suka dawo innah ta yanki jiki ta fadi jininta ya mugun hawa haka aka tattarasu da sadiya aka kaisu asibity abba yayi ta fama da dawainiya har Allah yasa sukayi sauki suka dawo.sadiya duk ta lalace bata ko iya cin abinci gashi mutanen anguwan se maganarta suke duk inda tayi ba damar ta fita.....

Dafe kai nayi hade da fadin" Innalillahi wa innah ilaihirrajiun yanxu sadiya shikenan ta rabu da ja,afar ? Wlh na tausaya mata dolene kawai ta rame .
Sa,a tace"shine fa kika ga wnn uwar iyayi da kissa da kisisina tace wai sadiya ta dawo gidan nan su zauna ko zata rage yawan damuwa.wlh aunty tunda sadiya ta dawo gidan nan ko motsi kwakkwara bamu isa muyi ba nida munir sai ta kama zaginmu aunty salmah kuwa shiru takeyi

shiru nayi yayinda na shiga tunanin zamanmu da sadiya a gidan nan don ba karamin matsala zata haifar ba.dama yaya hmm Allah dai ya kyauta .

Mun jima muna tattauna matsalar sadiya da sa,a.

Ni dai inda nake godewa Allah ya salman yana kula dani sosai ko kadan bai son abinda zai bata min rai don haka ma ya gargadi sadiya akaina domin in ta kuskura ta min wani abu zata bar masa gida .

Don haka duk iya shegensu kasa kasa sukeyi.anan suka dinga kulla makirci duk ranar girkina su faki idona su debi gishiri su cika min a miya ko su cika barkono kai watarana har da sugar kuma a kwanon ya salman suke sawa don kawai su hada mu amma abin mamaki sam bai yi fada ba kuma ya gane makircinsu ne don haka ya kwace makullan side dinshi gabadaya ya bar guda daya yace duk wacce takeda girki ta rike a hannunta sai ta gama ta bawa 'yar uwarta ni kuma ya gargadeni akan duk ranar girkina na kula na sa ido sosai akan duk wani motsinsu.

Ganin basu sami nasara ba yadda suke so ba sai suka koma suka canza plan duk ranar girkina indai sinjini a kitchen sai su kunna burner su zuba turaren wuta mai karfin gaske su cika gida da hayaki ko wani corner .

Sau biyu suna yin hakan sai na koma sama da sauri ince sa,a ta karasa min girkin in kuma bata nan in sauke in jira har sai ta dawo.don bazan iya juran hayakin ba zai tada min da asmma dama da gangan sukeyi .ni dai har lokacin ban tanka ba.

Shine wata rana sadiya taje ta samo musu garin magani da katon kasko suka zo suka cika gida da hayaki ina kitchen na fara jin warin magani ga hayaki nan dan ya turnuke koina gidan da sauri na yi maza na kashe gas cooker .

Na fita da sauri na nufi side dina ko ganin gabana banayi da kyar na samu na shiga dakin na kulle kofa inata jera atishawa ba kakkautawa da sauri na jawo inhaler na duk kamar a banza don tuni na fara jin kirjina na toshewa don haka ne ma nayi maza na kira ya salman yana jin yanayin maganata ya gane ba lfy don haka ya kashe wayar da sauri bar abinda yakeyi ya fizgi motarsa da gudu ya dawo.yana shiga ya tarar hayaki har lokacin ya cika gida baiyi magana ba ya wuce sama zuwa side dina ya sameni ina ta kokarin lalubar numfashi da kyar don haka yayi maza ya dagani ya fita dani zuwa motarsa yaja sai asibity emergency suka karbeni nan da nan aka min alluran cikin jijiya wanda tunda ya fara shiga jikina numfashina ya fara komawa normal a hankali a hankali kamin su cire alluran har numfashina ya dawo dai dai cikin ikon ubangiji.

Ya salman ya sauke ajiyar zuciya hade da fadin Alhamdulillah sannu baby ya kk ji yanzu?

A hankali nace"normal ba komai.

Yace"to sai mu gode Allah .Amma hayakin me kuka sa a gidan ya turnuke koina ?

Idona a limshe nace"nima ban sani ba ina kitchen kawai naga haya ki.......

Karar wayarsa ne ta katseni nayi shiru ya daga hade da fadin " hakim ina jinka.

Sai naga ya mike da sauri hade da fadin"what!!!gani nan zuwa yanzu.

Kirjinane ya shiga bugawa da sauri na yunkuro zan tashi ya salman ya kamani ya kwantar dani hade da girgiza min kai yace"kwanta ke kam .

A rikice nace"yaya menene ka fada min kar zuciyata ta buga.

Yace"babu komai ba wani abu bane salmah ce ba lfy.ina zuwa ke dai kiyi hkr zance doctor james a kula dake da kyau ina zuwa.

Ya fita da sauri.
Hmm hausawa sukace in zaka gina ramin mugunta ginashi gajere don watakila kai zaka fada.
Ashe hayakin nan da suka turnuke gida dashi ya jawo salmah ta shiga wani yanayi nan dan ta fadi ta kama shure shure idanu suka kakkafe sadiya ta rikice ta kama shiga da fita ta rasa yanda zatayi duk da ma ta fitar da kaskon hayakin ta kashe amma ko da ta dawo a sume ta tarar da salmah anan sadiya ta kama kuka hade da salati tana yau ta shiga uku ya zatayi.

A cikin hakan hakim ya samesu a lokacinda ya dawo da munir daga school shine ya fadawa ya salman a waya .

Anan hakim ya debo ruwa suka shiga shafawa salmah don ta farfado.aikuwa tana farfadowa ta fara maganganu da wani irin murya na daban .

Daga hakim har sadiya sunja baya da sauri a tsorace da ganin yadda salmah ta koma alamun aljannune ita .

A haka ya salman ya samesu hankalinsa ya tashi sosai ya kimkimeta itama suka zo asibity .

Anan doctor yace masa salmah ciwonta bana asibity bane na gidane su koma gida a ne mi maganin aljannu don haka ya salman ya kira ya sanar a gidansu nan da nan suka zo suka tattarata sukayi gida da ita ashe su dama sun san tana dasu sa,arsu daya ne basa tashi akai akai kuma iyayenta sun tsaya mata tsayin daka wurin nemo maganin shiyasa abun nata baiyi tsanani ba.
Chapter 88 · 0% Book details