← Book details Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 128

Sashe 35

Rumaisa Salman Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace "yawwa ni sunana DOCTOR SURAYYA AHMAD.matar DOCTOR HAKIM sannan yayar AHMAD UMAR da SALIMA

Lokaci guda muka kalli juna da mama.

Taci gaba da fadin " nazo nan ne domin in gargadeki da ki jawa 'yarki rumaisa kunne da ta fita daga harkar Ahmad domin ba ajinta bane shi.

Sannan ta cire glass din idonta ta kalleni up and down ta ce " ke kuma duk abubuwanda kikeyi muna sane daga lokacin da kike tare da doctor har zuwa yanzu da kk likewa Ahmad.don haka yauce zuwana na farko kuma na karshe ina mai kara gargadinki akan Dan uwana da mijina domin idan kk kuskura na sake jin wani abu to ki kuka da kanki.

Ta kalli mama tace " ke kuma kamata yayi ki nemawa ' yarki dangin ubanta ko da kuwa bata hanyar halak kika sameta ba wnn shawarace domin in ba haka ba 'yarki bazata taba samun mutunci da kima a idon mutane ba. Babu wani Dan arziki da zai iya auren ta a garin nan don haka ki maida hankali wurin nemawa ' yarki UBANTA ba wai Ku tsaya kwadayi da buri ba. Ina fatan kun fahimci inda maganata ta dosa?

Nikam kallon mama nake .

Sai naga ta danyi murmushi tace " shikenan abinda ya kawo ki?

A yatsine tace" eh shikenan amma fa idan yarki bata fita harkar Dan uwana ba zaku fuskanci wulakanci da rashin mutunci da tozarci .......

Mama ta girgiza kai tace " ba sai an kai ga haka ba.in Allah ya yarda ma ta rabu da shi .ki kwantar da hanakalinki.

Ta sauke ajiyar zuciya tace" kun kyautawa kanku.

Ta juya ta fita muka bita da ido har ta bace nikam hawayene ya taru a idona da sauri na wuce daki mamace ta karasa shanya min kaya.

Ahmad na kira bai dauka ba har tsinke sannan ya kira ni na dauka da sauri.cikin nishadi yace" my Queen! Sarauniyar mata!ina fatan kina lfy?

Nace" Ahmad ba lfy.

Da sauri yace" what!!!
Nace " yanzu doctor surayya ta bar gidan nan bayan ta gama shimfida mana rashin mutunci....

Nan na gaya mishi komai hankalinsa a tashe ya kashe wayar.

Tuni ya tafi asibityn da take aiki ya sauke mata kwandon bala,i hade da yi mata gargadi sosai akan kar ta kuma shiga rayuwarsa don bai shafeta ba.

Yazo har gida ya yita baiwa mama hkr mama tace ita dama ranta bai baciba kawai tunda abin ya zama haka dole ne kawai ya rabu dani domin bazata yarda in shiga familinsu ba tunda abin yazo da haka.

Juyin duniya yayi da mama amma Sam taki yarda hasalima taki yarda mu hadu jikinsa a mace ya bar gida nikam ina daki ba abinda na Sani sai kuka.

Yana komawa gida yaje ya sami his Excellency ya kai karar surayya .bai taba tunanin mahaifinsa zai juya masa baya ba amma sai gashi kiri kiri ya nuna masa yana sane da maganar kuma shima yana goyon bayansu su surayya.

Anan Ahmad ya fahimci hada baki surayya tayi da Salima da mahaifiyarsa suka rusa maganar aurenmu ta hanyan bata min suna a cikin familynsu.

A ranar Ahmad ya bar kasar gabadaya da don tsabar bacin rai.

A bangarena ba rabuwa da Ahmad ne kawai ya dameni ba 99% abinda yafi damuna maganar waye MAHAIFINA?Ina son sanin asalina ko na huta da gori.

Ranar ko abinci nakici mama tayi ta shiga tana min magana amma naki in kulata .

Haka muka kasance har dare.

Hankalinta ya kasa kwanciya.

Ta kuma shigowa ta sameni kamar yadda ta barni.

Zama tayi a bakin gado tace" haba Rumaisa har yanzu bazaki bar kukan nan ba ? Tunda safe kike aiki daya.

Ta danyi shiru sannan ta sa hannu ta dagoni tace " kinga kiyi shiru ba amfanin kukan nan addua zamuyi Allah ya kawo miki wani mijin......

Cikin kuka nace " ni ba shi ya dameni ba.

Tace " to me nene rumaisa?

Nace" ni so nake nasan waye MAHAIFINA da danginsa.

Ta zuba min ido tace " shikenan?
Na daga mata kai.

Ta danyi shiru sannan tace " to ki ta shi kici abinci kiyi wanka ki kintsa ki sameni a daki na.

Ta jawo tray din abinci da ta shigo dashi tace " to sauko kici.

Na goge fuskata na sauko na danci amma ba mai yawa ba. Sannan na shiga wanka na fito banga mama ba na shirya cikin kayan baccina na tafi dakinta amma bata nan zama nayi akan gado ina jiranta can ta shigo yayinda take cire hijabinta tace " naje gun yaya ne.

Ta bude wardrobe dinta ta dauko wani jaka Wanda yake a kulle sai da tasa keys ta bude sannan tazo dashi ta zauna gefena.tace " rumaisa komai dinki yana cikin jakar nan zan fada miki inda mahaifinki yake kuma zaki tafi goben nan insha Allahu amma sai Na baki labarin rayuwata da yanda aka sameki har zuwa yanzu ban Sani ba ta iya yiwuwa kiji dadin labarin ta iya yiwuwa kuma bakin cikinda kike ciki ya karu amma koma meyene kiyi hkr.

Ta share hawaye da ya taru a idonta.

Ta mika min wani hoto Na karba tace " wnn shine mahaifinki IBRAHIM.

Na zuba ma photon ido kyakkyawan saurayi daga gani bafilatani ne usul don fari Sol ba shakka a gurinsa Na dauki haken nan domin su mama basu da haske sosai.kuma daga gani wayayyene nitsasse.

Kawai Na tsinci kaina da sakin murmushi .

Mama ma murmushi tayi tace " rumaisa mahaifinki dan babban gida ne dan manyan mutane kuma suna da tarin arziki kuma mutane ne masu kirki da karamci da mutunta Dan Adam.

Fara,a sosai ya bayyana a fuskata hakama mama taci gaba da fadin " wani albishir ma da zan miki shine ni da mahaifinki aure mukayi muka haifeki ba zina ba.kuma mahaifinki yafi sonki a cikin dukkan yaransa.amma daga baya da kansa ya koreni a gidan........

Ta karasa maganar cikin kuka .

Ido na zuba mata !!!

Hauly ce🥰👍🏻
🌹 *_RUMAISA_* *_SALMAN_* 🌹

👨🏻‍🚒```MATAR ```SOJA`👨🏻‍🚒

*Story* *and* *written*
*By*
*Maman* *khausar* ✍🏻

*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION* 📚📚📚

*Dedicated* *_to_* *Ummi* *Abdallah* 🥰

*Bestowed* *to* *Zuwairiyya* *Abdulwahab* ( *real* *mum* *afrah* ) *❤*

~```BISMILLAHIRRAHMANI``` ```RAHEEM``` !~```

Page➡31

🌹 *_LABARIN_* *_AMINA_* 🌹

*************Amina Suleyman yakasai Wanda aka fi Sani da ( meenah)

Amina ta tasone cikin kulawar yayyunta kasim da Mohd domin iyayensu sun rasu tun tana primary.

Asalinsu kanawa ne domin dukkan danginsu anan suke.
Amma tun bayan rasuwar mahaifinsu babu Wanda ya kula dasu a dangi kowa yayi watsi da lamuransu.

Mohd shi ya dauki dawainiyarsu domin a lokacin yana malamin primary kuma yana taba kasuwanci.

Kasim kuwa yana bautar kasa a Kaduna.

Yayinda Amina take ss2 kuma boarding school

Mohd ya hadu da shatune a lokacin da suka tafi kamaru daurin auren wani abokinsu anan Allah ya hadashi da shatu wacce ta matukar fizgar hankalinsa domin dama kunsan kanawa da son farar mace lol! Bare kuwa shatu kam bayan haske ga kyau ga gashi ga kuma diri.

Nan fa ya like mata bai wani sha wahala ya sami amincewarta har maganarsu ta yi karfi gun iyaye.basu cika shekara ba akayi bikin aurensu shatu ta tare a gidan Mohd Na Kaduna domin acan aka masa transfer

A lokacin amina tana ss 3 kasim kuma ya kare bautar kasarsa.

Koda su Amina sukayi hutu kasim ne ya tafi kano domin ya daukota.

Aikuwa tana ganinshi ta kama tsalle da murna tana " kai yaya nayi kewarku wnn term ko visiting Baku zo min ba.

Yana murmushi yace " ke dai bari kanwata ni din na zama busy ne.

Tana dariya tace'kai yaya ina auntyna ne?

Yace " tana gaisheki au albishirinki ?

Tace"goro fari Sol yaya na.

Yace " yaya yayi aure last 2 weeks yanzu haka in mun koma zakici girkin Amarya....

Cikin tsantsan farin ciki tace wayyo yaya amma naji dadi domin ina son yaya yayi aure dama masha Allah ni har ma na kosa inga mun isa gida.bari inje in sallami friends dina.

Ta juya da sauri ya bita da kallo yana dariya .

Sun iso Kaduna da yamma Amina tun daga kofar gida take ta rafka sallama hade da fadin " ina aunty amaryar yayan nawa?

A lokacin da ta isa tsakar gida sukayi arba da shatu wacce take shara ko a jikinta kamar ba sallama ake ba.

Turus amina tayi tana binta da kalli kasim ne yace " madam baki ganmu ba?
Ta dago tana murmushi tace " na ganku mana .

Sannan ta kalli Amina cikin hausarta da bai gama nuna ba tace " shannunku da juwa ga taburma.

Ta wuce ta dauki taburma ta shimfida kasim kam cewa yayi ni dai na zauna a kujera ki bani abinci na inci in wuce shago nasan yaya na jirana ya samu ya dawo gida yaga amaryatsa

Murmushi tayi tace " to kasim
Ta wuce kitchen amina har lokacin tana tsaye kasim yace " to wai bazaki shigar da kayanki kije ki zauna ba kin wani tsaya kina binta da kallo?

Amina tace " yanzu fisabilillah ya Mohd ga ' yanmata a cike a gari wayayyu shine ya tsallaka kamaru har kauye yaje ya dauko wnn bigidajiyar yarinya da ko Hausa bata iyaba?
Gaskia ni wlh matar nan bata min ba wlh wnn ai abun kunya ne ma in nunata a matsayin matar yaya na.

Taja tsaki ta suri jakarta a lokacin shatu kuma ta fito daga kitchen Anan sukaci karo shatu ta zubawa Amina ido.

Yayinda Amina ta watsa mata harara tace " wai kallon me kk min ne ? Mtswww

Ta wuce daki.
Ran shatu ya baci sosai sai dai kasim ya bata hkr yace haka halin amina yake.

Kwata kwata amina bata sakarwa shatu fuska kuma ko girkinta bata ci bare ta tayata aikin gida hasalima in su biyu ne a gidan zakice kurame ne ba mai uhm bare uhm uhm.
Chapter 35 · 0% Book details